✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka za ta fara yi wa jirage marasa matuka rajista

Jirage masu sarrafa kansu da kuma wadanda suka mallake su dole ne su yi rajista a kasar Amurka daga ranar Litinin mai zuwa.Duk wani jirgi…

Jirage masu sarrafa kansu da kuma wadanda suka mallake su dole ne su yi rajista a kasar Amurka daga ranar Litinin mai zuwa.
Duk wani jirgi mai sarrafa kansa da aka saya daga wannan rana dole ne a yi masa rajista kafin tashinsa na farko, a cewar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta kasar, kamar yadda BBC ya bayyana.
An ba masu jiragen nan da watan Fabarairun badi da su yi rajista, inda aka yafe musu Dala biyar domin su yi azama a cikin kwanaki 30.
Kakakin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka, Les Dorr ya ce hukumar za ta yi kokarin ilimantar da wadanda ba su yi rajistar ba maimakon hukunta su.
Ya kara da cewa wadanda kuma suka ki su yi rajistar, “Muna da hanyoyin da za mu tilasta musu yin hakan.” Hukuncin da za a yi musu zai kai tarar Dala dubu 27 da 500 (fiye da Naira miliyan shida), amma ana iya tsaurara tarar ta kai Dala dubu 250 da kuma daurin shekara uku a gidan yari.
Wadanda suka mallaki jiragen marasa matuki da suka wuce shekara 13 dole ne su yi rajista da kansu, wadanda ba su kai wannan shekaru ba kuwa iyayensu ne za su yi rajistar a madadinsu.
Kowane jirgi marar matukin za a ba shi lamba ta daban wanda a za a lika a jikin jirgin, a cewar hukumar.