Wani kamfanin kera bindigogi na Florida da ke Amurka yana fuskantar suka sakamakon kera wata bindiga domin cin zarafin Musulmi.
Jaridar OnIslam ta intanet ta ruwaito a ranar Lahadin da ta gabata cewa, kamfanin ya sanya wata aya ta Baibul bisa niyyarsa ta hana “Musulmi ’yan ta’adda” daga amfani da ita.
Kakakin kamfanin Ben “Mookie” Thomas, wanda tsohon sojin ruwan Amurka ne ya shaida wa jaridar Orlando Sentinel da ake bugawa a Amurka cewa “Babu Musulmin kirki” da zai iya taba bindigar. Da so samu ne da na samu bindigar da in Musulmi dan ta’adda ya dauke ta za ta yi tartsatsti ta bindige shi ya mutu.”
Hoton bindigar mai suna AR-15 Crusader Spike’s Tactical ya sanya a Apopka ya nuna tambarin gicciye a cikin wata garkuwa irin wadda mayakan da ake kira Knights Templar suka yi amfani da ita a lokacin yakin Gicciye a daya gefen. Yayin da a daya gefen aka rubuta wata ayar Baibul daga Zabura sura ta 14:1 mai cewa: “Albarka ta tabbata ga Ubangiji dutsena, wanda ya horar da hannuwana ga yaki, yatsuna ga fafatawa.”
Wannan bindiga ta fusata jama’a kan yadda ta takali Musulmi.
Babban Daraktan Majalisar Hulda a Tsakanin Amurka da Musulunci da ke Florida (CAIR-FL), Hasan Shibly ya mayar da martani kan bindigar inda ya ce: “Shin an kera ta ne don Kirista ’yan ta’adda?”
Shibly ya ce daga cikin kisan gilla 205 da aka yi a Amurka, daya ne kawai ya hada da Musulmi, inda ya ce CAIR-FL tana adawa da duk wuce iyaka a addini to amma masu kera bindigogi “ba su da ’yancin su kirkiro abubuwan da za su sanya mu fada da su.”
Majalisar CAIR-FL ta kuma fitar da wata sanarwa kan bindigar da ake sayar da ita kan Dala 1,395 tare da waranti daga kamfanin. “Abin bakin ciki makerar ta fito da wata sabuwar bindiga da ba za ta iya yin komai wajen dakatar da hakikanin barazanar da ke cikin Amurka ba. Yaduwar matsalolin harbe-harben bindiga, wannan wani abin kunya ne na kasuwancin da ake neman riba ta hanyar yada kiyayya da rarrabuwa da tashin hankali,” inji sanarwar.
Amurka ta kera bindiga don cin zarafin Musulm
Wani kamfanin kera bindigogi na Florida da ke Amurka yana fuskantar suka sakamakon kera wata bindiga domin cin zarafin Musulmi.Jaridar OnIslam ta intanet ta ruwaito…