✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta jinjina wa Angola ‘kan yaki da cin hanci’

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, wanda ya kai ziyara Angola, ya ce daya daga cikin abubuwan da suka ba shi mamaki a yayin da…

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, wanda ya kai ziyara Angola, ya ce daya daga cikin abubuwan da suka ba shi mamaki a yayin da yake ziyara a kasashen duniya shi ne yadda cin hanci da shawara ya yi katutu, amma ya yabi Shugaba Joao Lourenço na Angola bisa kokarinsa na magance almundahana, yana mai cewa illar da ta yi wa Angola a bayyane take.

Dangin tsohon Shugaban Angola, musamman ’yarsa Isabel dos Santos, tana fuskantar bincike kan zargin almundahana.

A ziyarar da yake kai a Afirka, Mista Pompeo ya ce yana so ya bunkasa harkar masu zuba jari a Amurka sannan ya dakushe tasirin da China take yi a nahiyar inda ya kawar da fargabar da ake yi cewa Amurka na shirin rage yawan dakarunta a nahiyar.

Daga Angola, zai Habasha a ziyarar kasashen Afirka uku da yake yi.

Tun farko ya kai ziyara kasar Senegal, kafin ya isa Angola.