✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta bai wa Nijar jiragen yaki

A jiya Alhamis ne aka ruwaito cewa kasar Amurka ta taimaka wa gwamnatin Jamhuriyar Nijar da jiragen yaki guda biyu da motocin 30 da kuma…

A jiya Alhamis ne aka ruwaito cewa kasar Amurka ta taimaka wa gwamnatin Jamhuriyar Nijar da jiragen yaki guda biyu da motocin 30 da kuma wasu kayayyaki domin yaki da ta’addanci.

Jiragen na dauke da na’urorin zamani na tattara bayanai, kuma za su taimaka wa Nijar wajen gano barazanar ‘yan ta’adda da kuma kare iyakokin kasar, kamar yadda BBC ta bayyana.
Jamhuriyar Nijar dai na fama da matsalar masu tayar da kayar baya na Boko Haram, inda ko a shekaraniya Laraba suka kashe sojojin kasar guda biyu.
Har ila yau, a ranar Asabar da ta gabata ne Shugaban dakarun Amurka na Afirka Janar Dabid Rodriguez ya bai wa jamhuriyar Kamaru motocin yaki domin tallafa mata wajen yaki da kungiyar Boko Haram. Hakazalika, a farkon makon jiya ne gwamnatin Amurka ta sanar da tura dakaru 300 zuwa Kamaru domin murkushe Boko Haram.
Boko Haram ta dade tana amfani da yankin arewacin Kamaru wajen kaddamar da hare-hare. Sai dai a bara dakarun kasar tun fatattake su daga yankin.