Kasashen Amurka da Birtaniya sun tsame Babban Birnin Najeriya, Abuja, daga cikin biranen da ake fargabar yiwuwar kai harin ta’addanci a cikinsu.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Ofishin Kula da Harkokin Kasashen Waje na kungiyar Kasashen Rainon Ingila (FCDO) ya fitar.
- ‘Akwai ’yan gudun hijirar Najeriya 500,000 a kasashen waje’
- Za mu kawo karshen fita kasashen waje neman lafiya – Buhari
Ofishin ya sanar da hakan ne a shafinsa na Intanet a daren Litinin.
Sanarwar na cewa, “Ofishin FCDO ya janye shawarar da ya ba ’yan kasashen waje a kan su guji ziyaratar Abuja in ba ya zama dole ba, sai dai har yanzu akwai burbushin hatsarin da ta yi gargadin na nan…”
Sai dai sanarwar ta ce gargadin da Ofishin ya yi na zuwa wasu garuruwa a Najeriya na nan daram.
Jihohin da ofishin ya gargadi ’yan kasashen wajen da ziyarta su ne; Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Kaduna da Katsina da Zamfara, da wasu jihohi na bakin teku.
Jihohin su ne; Akwa ibom, da Kuross Ribas.
Jihohin da ke da sassaucin gargadi na FCDO sun hada da Bauchi da Kano da Jigawa da Neja da Sakkwato da Kogi da kuma kilomita 20 daga bakin iyakar jihohin Neja da Kebbi.
Sai kuma jihohin Abia da Delta da Bayelsa da Ribas da Filato da kuma Taraba
Ofishin ya kuma shawarci ’yan kasashen wajen da a kodayaushe su rika bincikar sashen da ke sa ido kan shige da fice, kafin su yi duk wata tafiya don ba su shawarwari da ingantattu.