Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan fili da fatan Allah Ya amafanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Insha Allah za mu amsa tambayoyin da masu karatu suka aiko:
Tambaya: Maganin cikar kirji
Shekaruna goma sha bakwai amma har yanzu kirjina kamar ba na budurwa ba, shi ne nake neman shawara shin zan sha wani magani ne ko kuwa? Anti Nabila ki taimaka min abin na damuna.
Amsa: In dai sun fara tsirowa ko yaya ne to babu matsala sai dai kawai ki saki zuciyarki ki kwantar da hankali, ki fahimci cewa komai da lokacinsa, kowane fure lokacin bayyanar daban da na waninsa, kamar yadda wadansu ’yan mata suna fara balaga kirjinsu zai cika da sauri wadansu kuma a hankali nasu yake tafiya, wadansu sai sun dauki ciki sannan kinjinsu ya kai kololuwar cikarsa, kuma irin wannan mai tafiya a hankalin ya fi karko don mai cikowa nan da nan haka kuma zai yi saurin saki da zubewa nan da nan. Don haka ki kwantar da hankali ba wani abin damuwa a ciki. Sai dai in kwata-kwata ba su tsiro ba ko yaya ne, to wannan kila akwai matsala musamman in yarinya ta fara jinin haila, ta iya yiwuwa akwai wata cuta wadda binciken likita ne kadai zai bayyana. Garin hulba yana taimakawa ga ciko da kirjin ’ya mace, ki rika dama shi tare da garin alkama kullum ki sha kofi daya, haka ’ya’yan ‘fennel’ su ma suna taimakawa wajen cikar kirji, amma ki sani ba wai garanti ne lallai da kin sha kirjinki zai ciko ba. Wani sa’in yanayin halittar da Allah Ya yi wa mutum ita ke tabbata. Sannan ki rika cin abinci masu kiba musamman in ke siririya ce, karancin kitse a cikin jiki na haifar da rashin cikar kirji da wuri. Ki yawaita yin sadaka da ikhlasi da niyyar Allah Ya biya miki bukatarki. Babban magani dai shi ne ki amince da kanki a yadda kike kuma ki yi godiya ga Allah ga hakan.
Tambaya: Salam, za ka ga mace ta zama ’yan mata har ta kai shekara 16 amma sai ka ga kirjinta kamar na yara, me ke kawo haka?
Amsa: In kwata-kwata ba wani canji ga kirjin budurwa bayan ta balaga, to lallai akwai wata cuta da ke haifar da haka, gwajin likita ne kadai zai bayyana haka.
Tambaya: Nakan raina girman gaba har hakan yana saka ni cikin damuwa musamman in aka yi rashin sa’a a ranar na kalli mazakutar wani namijin a ranar ba barci kamar na fama ciwo. Don Allah a taimaka mini da magani kowane irine.
Amsa: A gaskiya wannan fili na yawan samun tambayoyi makamantan wannan daga maza masu tsananta ganin karantar mazakutarsu da ’yan mata masu tsananta damuwa da karantar cikar kirjinsu da matan aure masu tsananin su kirjinsu ya koma yadda yake kafin su haihu ko ma ya fi da gyaruwa. Maganar gaskiya wannan tsananta damuwa duk a tunani kawai, amma bai da nasaba da abin da yake zahiri ga masu fama da wadannan matsaloli. Mazakuta ba ita ce bajintar mazantaka ba, bajintar mazantaka a zuci take ba a gaban namiji ba. Akwai mazan da ba su taba aure ba amma sun yi abubuwan bajinta da har gobe duniya na tinkaho da su. Binciken kimiyya ya tabbatar sama da kashi 90 na masu ganin karantar gabansu a zahirin gaskiya ba su da karantar gaba su din ne kawai suke ganin haka. Haka nan kananan wajen shayarwa ba ya nufin mace ba ta isa mace ba, haka nan don sun zube saboda shayarwa ko wani dalili ba ya nufin mace ta raunata ko darajar ta ta rage, sha’awa da ‘macentaka a zuciya da ma’aikatar hankali suke ba a wani bangare na jikin dan Adam ba. Yawanci masu fama da wannan damuwa suna kwatanta kansu da wasu mutanen da ba a zahiri ba, misali garin kallon fina-finan batsa, wadanda jikinsu bai yi daidai da jikin gama garin mutane na zahiri ba. Ko ’yan mata su rika kwatanta kansu da ’yan fim din Indiya da sauransu wadanda yawancisu ma kananan wajen shayarwa gare su don ya fi daidai da lafiya illa da gyara da suke sha kafin su bayyana a gaban kyamara. Rainawa da tsananta damuwa a kan wani bangare na jiki da neman canjinsa tangardar ma’aikatar hankali ce da a likitance ake kira da Body Dysmorphic Disorder, don haka in dai damuwar ta tsananta har tana hana barci ya kamata a ziyarci likita don neman waraka. Allah Ya taimaka Ya sa a dace.
Sai mako na gaba insha Allah. Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin