✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyin daban-daban: Ranar Allurar Barci ta Duniya

A da idan aka ji an ce za a yi wa mutum tiyata, ba abin da ke zuwa ran wanda aka fadawa sai allurar barci…

A da idan aka ji an ce za a yi wa mutum tiyata, ba abin da ke zuwa ran wanda aka fadawa sai allurar barci wadda ake tsoronta sosai. Kai har yanzu ma akwai wadanda da sun ji sunanta sai sun dan firgita. Wadansu ma allurar kanshin mutuwa suke kiranta da shi. Wadanda za a yi wa ita kuwa wasunsu jininsu ne kan hau saboda tsoro.

A shekaranjiya Laraba ce ma’aikatan lafiya masu sa marasa lafiya barci a dakin tiyata za su yi bikin ranarsu, inda suke so su wayar wa al’umma kai kan irin nasu aiki, saboda a daina jin tsoron wannan allurar.

Allurar barci na nufin samar da wani yanayi ta hanyar amfani da magunguna ko allurai ko iskar shaka ta yadda jikin dan Adam ( ko dabba ) ba zai ji radadin ciwo ko zafi ba a lokacin gudanar da aikin tiyata, ko yayin aiwatar da wasu gwaje-gwaje wadanda kan jawo jin ciwo, ko ma domin hana jin radadi lokacin nakuda da haihuwa.

Magunguna ko alluran da ake amfani da su suna iya kasancewa masu sa barci ne hade da hana radadi, wato na general anaesthesia ko masu hana jin radadin ciwo kawai ba tare da an yi barci ba wato regional anaesthesia kamar ta kashe zafin nakuda ko tiyatar fidda jariri (C.S).

A duk lokacin da nau’in rashin lafiyar mutum yake bukatar wata babbar tiyata, to likitan fida zai tura shi wajen mai allurar barci kafin a yi aikin. Shi kuma ma’aikacin zai duba marar lafiyar ta hanyar yi masa tambayoyi da aune-aune da gwaje-gwaje domin tantance ko yanayin jikin marar lafiyar zai iya jure magunguna ko allurar da za a yi masa.

Ma’akatan suna yin la’akari da cewa marasa lafiya sun kasu kashi daban-daban. Akwai maza, mata, yara da tsofaffi, sa’annan wadansu marasa lafiyar suna dauke da wasu cututtuka daban da matsalar da za a yi tiyata a kanta, kamar hawan jini, ciwon suga, ciwon asma, ko amosanin jini da sauransu. Haka nan yana iya yiyuwa wanda za a yi wa aikin tiyata jininsa ba ya jituwa da was nau’o’in magunguna ko wani launin abinci. Kuma akwai yiyuwar marar lafiyar na shan taba sigari ko barasa da sauransu. Duk wadannan bayanan dole mai allurar barci ya tattara su saboda zaben magunguna da alluran da suka fi dacewa da marar lafiyar.

Bayan tattara duk wadannan bayanan sai ma’aikacin ya yanke hukunci ko ana iya yi wa marar lafiyar nan tiyata ko kuma sai an kara dan lokaci domin a inganta lafiyarsa kafin yin aikin tiyatar. Aikin mai allurar barci ne ya kula da majinyaci a duk tsawon lokacin yin aikin tiyatar, ta hanyar amfani da wasu na’urori don tabbatar da numfashinsa, aiki zuciyarsa, hana masa jin ciwo, kara masa ruwa ko ma jini idan ta kama, saisaita bugun jinin wato blood pressure da sauransu. Ma’ana dai alhakin mai allurar barci ne ya kula da majinyaci ya kuma tabbatar an yi aikin lafiya an gama lafiya, sa’annan ya farfado da shi har ya wartsake ba tare da ya samu wata matsala ba.

To kun ji. Don haka ke nan yana da kyau al’umma su kara fadaka da fahimtar kashe-kashen ma’aikatan lafiyarsu ta hanyar sanin ma’abuta fannonin kula da lafiyarsu. Duk marar lafiyar da nau’in ciwonsa na bukatar aikin tiyata to akwai wajibcin ba shi ingantacciyar kula daga kwararre a fannin allurar barci da rage radadi. Kuma hakkinsa ne ya san wane ne ma’aikacin da zai yi masa, yana kuma da hakkin zabar irin nau’in da za a yi masa bayan an gamsar da shi da cikakkun bayanai. Mata masu juna biyu ma na iya samun zabin yin nakuda tare da haihuwa ba tare da jin zafin nakuda ba.

Muna kira ga gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi su kara taimakawa wajen inganta wannan fanni ta hanyar samar da wadatattun kayan aiki da magunguna tare da kara samar da gurabe da makarantun karatun wannan fanni.

Muna kuma kira ga matasan likitoci da ma’aikatan jinya su rika shigowa wannan fanni domin har yanzu akwai karancin kwararru kuma a kullum bukatar kwararru a fagen karuwa take saboda karuwar al’umma da fadadar aikin kiwon lafiya.

Murtala Ahmed shi ne Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Jinya Masu Allurar Barci (NANA), Reshen Jihar Kano.

 

 

Mene ne yake sa wa idan ina rashin lafiya ina shan magani sai cikina ya rika kullewa, kuma sai na yi kwanaki uku ko hudu ban zaga ba. Ko me ke kawo haka?

Daga Muhammad Zahraddeen

 

Amsa: Watakila rashin cin abinci ne sosai a yayin da kake rashin lafiyar yake kawo maka haka, domin rashin cin isasshen abinci zai iya kawo alamun da ka zayyana, kullewar ciki saboda yunwa da kuma rashin zagawa, saboda ba a ci komai ba.

 

Ni ma duk inda asuba ta kawo jiki sai cikina ya kama ciwo, idan ya samu ’yan awoyi sai ya bari haka kawai. Me ke kawo haka?

Daga Ibbira Mani

 

Amsa: Kai ma watakila a daidai lokacin cikinka yana bukatar abinci, watakila kuma kana da gyambon ciki, domin zafin cikin gyambon ciki ya fi tashi tsakar dare ko karshen dare lokacin da aka dade ba a sa wani abu a ciki ba.

 

Ni kuma idan na karya da safe da hantsi ya karato sai na ji jikina ya mutu ina jin barci idan ban je na yi shi ba ba na jin dadi. Ko me ke kawo haka?

Daga S.P., Koko

 

Amsa: Watakila abin da kake karyawa da shi ne yake kashe maka jiki. Duk kayan karyawa na tsimi da ya dan yi kwanaki a tsime, irin su kunu ko koko ko fura, wato kayan sha wadanda sai da aka tsima gero kafin a hada su za su iya sa haka. Sababbin tsimi ba su cika sa haka ba. Har ka sa na tuna, a da muna makarantar sakandare ta kwana har tsoron shan kokon safe na makarantar ake saboda tsoron barci a aji.

 

Na kasance idan ina barci sai na jitsiye nake jin dadin barcin. Ko hakan da matsala?

Daga A.U. Darhela

 

Amsa: A’a Basakkwace, ba matsala in dai gicciyewa kake nufi A.M.A Daurawa Kiru da Muhammad ku ma tambayar da kuka yi iri daya ba matsala a kan abubuwan da kuka tambaya, zai wuce.

 

Me ke kawo mutum ya ji abu na masa yawo a jiki?

Daga Hafsat Jamil

 

Amsa: Malama Hafsat ina ga na amsa wannan tambaya amma kin sake aikowa, idan ba ki gani ba ki gani yau. Na ce akwai matsala idan mutum yana ji wani abu na masa yawo a jiki, sai kin je an binciki mene ne.