✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyin daban-daban:  Me ake nufi da bambancin halitta?

Na kasance ba na son abinci da abin sha mai zafi. Ko wanka ma sai da ruwa mai sanyi. Ko hakan matsala ce ko bambancin…

Na kasance ba na son abinci da abin sha mai zafi. Ko wanka ma sai da ruwa mai sanyi. Ko hakan matsala ce ko bambancin halitta?

Daga Aminu Muhammad

 

Amsa: Bambancin halitta ne, abin da muke cewa idiosyncracy, bambanci ne a tsakanin ’yan Adam wanda ake gani ba ciwo ba ne. Wato wadansu mutane irinka su haka aka yi su daban. Abin da ake nufi da bambancin halitta ke nan, a ce wadansu suna da halitta ko wasu halaye da wadansu mutane sukan gani wani iri, amma kuma ba rashin lafiya ba ne, ba kuma ciwon kwakwalwa ba.

Kamar yadda muka ce akwai bambancin halitta ta jiki, akwai kuma ta halaye, bari mu ba da misalin kowane; misalan bambancin halitta na halaye ban da irin wannan naka na rashin son abinci mai zafi sai dai mai dan sanyi-sanyi, sauran misalan su ne, wadansu suna da son kure adaka, wato akwai mutane wadanda su a kullum sai sun kure adaka suke iya shiga mutane, ba sa sa kaya daidai da yanayin gari. Masu iya habaici da karin-magana da wake ma duk za a iya sa su a cikin wannan tafiya. Mutane masu shiru-shiru ko wadanda suka iya shige-shige, su ma za a iya cewa sun bambanta da sauran mutane

Bambancin halitta na jiki kuma misalansu su ne; wadansu an yi su farare, wadansu jajaye, wadansu bakake. Kuma dukansu daidai suke. Wanda ba daidai ba ta wannan bangare shi ne za ka gan shi zabiya (wanda akwai a kowace al’umma). Akwai kuma mutane dogaye, akwai gajeru, akwai matsakaita. Dukkansu daidai ne, wadanda za a ce suna da rashin lafiya ko matsala a wannan aji su ne wada ko zankali. Haka wadansu mutane an musu ajin jinin A, wadansu O, wadansu B, wadansu AB. Akwai wadanda ake kira mutane masu lankwasa, wadanda za su iya lankwasa jikinsu duk yadda suke so, kuma gabobinsu ba matsala ne da su ba. Da sauran ire- iren wadannan misalai.

Masu ba da magani na kimiyya wato (Pharmacists) ma sun lura magunguna na aiki a jiki mutane ta hanyoyi daban-daban, akwai kuma wadansu da sukan ga wasu abubuwan mamaki a tattare da aikin magani a jikinsu. Wato sun gano ba kowane magani ne zai yi aiki irin yadda ya yi a jikin wane ba. Kawai dai abin da masana tunanin halayyar dan Adam  (Psychologists) suke nusarwa ga wadanda suke da bambancin halaye da na sauran al’umma shi ne, tsakanin irin wadannan halaye na daban da matsalar tabin hankali tazarar kadan ce. Don haka suka ce wadannan mutane masu hali daban da na saura akwai yiwuwarsu ta fadawa cikin jerin mutane masu ciwon kwakwalwa, don haka suka ba da shawara ga mutane wadanda suke da halaye na daban da sauran al’umma su rika daurewa suna koyi ko rage zurfin bambancin nasu domin a zauna lafiya.

 

Ni kuma ina da yawan zufa. Ko mene ne maganin haka?

Daga Abdurrazak A. Bauchi

 Amsa: Kai ma watakila ba matsala ba ce, don akwai mutane masu yawan zufa, kuma ba wani ciwo ba ne da su, haka nan aka halicce su, za a gan su yawanci suna da kiba. Amma idan kowa yana jin sanyi kuma lokacin sanyin ne, kai amma zafi kake ji, to fa sai an duba lafiyarka, zai iya zama ciwo.

 

Ni kuma ina yawan jin kamar ana tsirata a fuska. Ko mene ne magani?

Daga Maman Khadija, Abuja

 Amsa: Kina jin tsiri a fuskarki ko kamar ana tsira? Domin akwai bambanci. Idan kika ce kina ji kamar ana tsira to ba tsirarki ake ba ke nan, amma idan kin tabbatar wurin na tsira, to akwai matsala. Za ki iya duba wurin da ke tsira a madubi ki gani ko akwai kumburi, ko canjin launin wurin ko tsaga ko dai wani abu. Idan akwai daya daga cikin wadannan sai kin je asibiti, idan babu maganin kaikayi na shafawa kawai za ki samu ki saya a kyamis.

 

Me ke kawo kyasbi a fuska ko a jiki?

Daga Usman Aminu Malumfashi

 Amsa: Mun yi maganar kyasbi a baya, muka ce akwai nau’i biyu; akwai wanda kwayoyin cutar fungus ke kawowa, akwai kuma wanda canjin yanayi da bushewar fata ke kawowa. Saboda mutane ba sa iya bambance nasu na mene ne, shi ya sa yake wuyar magancewa. Ya kamata mai kyasbi ya samu likitan fata wanda zai gani, ya bambance masa ya ba shi shawarwari da magunguna

 

Duk lokacin da aka tashe ni daga barci sai kaina ya yi ciwo, amma idan da kaina na tashi ba ya ciwo. Me ke sa haka?

Daga Rabi’u B. Bagiwa

 Amsa: Idan barci bai ishi mutum ba ya tashi ko aka tashe shi, zai iya samun ciwon kai. Wadansu da sun koma sun dan kara shi ke nan ciwon kan zai ware. Idan kuma ba a samu an koma ba, watakila ba zai bar ciwon ba a wannan yini sai an sha maganin ciwon kai. Don haka sai ka rika fada wa masu tashin naka su rika barinka kana tashi da kanka, ko kuma ka rika kwanciya da wuri domin ka samu barci isasshe.

 

Na taka kusa tun watan azumi, an yi mini allurar rigakafin sarke hakora, na sha kuma magani, amma har yanzu wurin yana mini ciwo kadan-kadan. Ina so ka ba ni shawara.

Daga Ahmed Ghali

 Amsa: Shawara ka je likita ya sake ganin wurin. Idan ya warke sarai zai sanar da kai, idan ma akwai wani abu da yake faruwa da ya duba wurin zai gani.

 

Tun ina karami aka yi mini allura ta taba mini kafa har ina dingishi. Ko akwai wani magani da zan rika amfani da shi?

Daga Labaran M

 Amsa: A’a zuwa za ka yi likitan kashi ya ga kafar ya duba ta ya ga wane irin taimako za a yi maka ka daina wannan dingishi.

 

Me ke kawo ciwon kai da kunar zuci da zafin jiki?

Daga Jibrin J. Legas

 Amsa: Wadannan alamu za su iya nuni da cututtuka masu dimbin yawa, babu daya da yake nuni ko tabbas da wani ciwo idan ba duba ka aka yi ido-da-ido aka yi maka tambayoyi, aka yi maka aune-aune da gwaje-gwaje ba.