✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi: Shan tafasasshen shayi na da illa in ba a fifita ba?

Ina ganin wadansu mutane idan suka sayi shayi ba a fifita musu shi koda tafasasshe ne haka za su sha. Shin shan irin wannan shayi…

Ina ganin wadansu mutane idan suka sayi shayi ba a fifita musu shi koda tafasasshe ne haka za su sha. Shin shan irin wannan shayi ba ya da illa ga jiki?

Daga Nasiru Kainuwa, Hadeja

 

Amsa: Eh, haka ne wani lokaci wadansu sukan sha shayi mai dan karen zafi, kai ba wadansu ba ma, har ni da kai a wasu lokuta, muna shan irin wannan shayi tafasasshe za mu ji harshenmu da dasashinmu da makoshinmu sun amsa ko ma su daye daga ’yar kuna wanda sai an dauki kwana biyu zuwa uku kafin ta warke. Ban da wannan ba wata illa a likitance.

 

Da gaske ne idan aka dafa sukari kafin a sha ba wata matsala?

Daga Hassan Usman, Abuja

 

Amsa: Ko ka dafa sukari ko ba ka dafa ba, dama can dafaffe ne, an dafa shi a kamfani. Domin sai an dafa ruwan rake yake zama sukari. Don haka ko ka kawo shi gida ka sha haka ko ka kara dafawa duk daya. Wadansu dai sukan ce idan aka kara dafa shi kamar a shayi wai yakan kara zaki. Haka ne saboda dafawar na kara tsane ruwan jikinsa zakinsa ya fito, amma dai duk nauyinsu daya ne, wato nauyin ma’aunin calory.

 

Wani ne aka auna jininsa aka ga saman 88 kasa 50, wani kuma aka auna saman maki 160 kasa 90. Shi ne nake neman karin bayani a kansu.

Daga Aminu Ahmed Kazaure

 

Amsa: Eh, ai mun taba bayani a kan wannan. Daya jinin ya yi kasa, dayan kuma ya yi sama. Tsaka-tsaki shi ne aka fi so wato maki 120 ko 110 sama kasa kuma 80 ko 70. Amma kafin a ce tabbas mutum jininsa ya hau, sai an gwada shi akalla sau biyu a ziyara daban-daban kuma an ga makin na’urar ba ya sauka. Ita wannan na’ura tana auna karfin bugun jini da zuciya kan yi a magudanan jini na sassan jiki a kan ma’auni mai karfin maki daga 100/60 zuwa 140/90. In bugun jinin ya yi karfi da yawa, akan ce jini ya hau, wato makin ya kai kamar 160/90 kamar yadda ka ce, ko 170/110 ko ma 200/140 ko ma fiye. Zuciyar kuma za ta iya aiki a karfin makin da bai kai 100/60, wanda hakan a iya kiransa saukar jini ko ‘hypotension’ kuma ita ma alama ce ta cewa zuciya ba ta aiki da karfin da ya kamata. Hakan kan faru in ciwon zuciya ya yi nisa ko kuma ya kai makura, ko kuma in jinin jikin mutum ya yi kasa kamar a hadarin abin hawa.

 

Mene ne yakan sa numfashin mutum kamar ya dauke?

Daga Abubakar Dan Borno

 

Amsa: Abubuwa da dama, tun daga ciwon zuciya zuwa na hanyoyin numfashi kamar su asma duk za su iya sa wannan. Mai samun wannan yana bukatar ganin likita cikin gaggawa

 

Ina da ciwon asma na je asibitoci da dama na karbi magunguna har na gaji ba canji shi ne nake tambayar magani na kwarai

Daga Musa Sani

 

Amsa: Da fari dai ya kamata ka san cewa idan kana da ciwon asma mu a likitance ba maganin waraka, sai dai mai sa ciwon ya lafa. Magunguna masu sa ciwon ya lafa hawa-hawa ne. Idan matakin farko bai yi aiki ba, sai a koma mataki na biyu, idan shi ma ba ya aiki, sai a koma na uku. Haka har sai an samu wanda zai sa ciwon ya lafa. Don haka hakuri za ka yi ka ci gaba da bibiya. Idan kuma asibitin ne ba sa canja maka maganin, sai ka nemi na gaba, inda za ka iya ganin likitan cututtukan numfashi wato pulmunologist.

 

Kuraje ne suka dame ni a gadon baya da kafada da fuska, shi ne nake neman magani

Daga Abdul, Deidei

 

Amsa: Kurajen pimples ne, wato barni-da-mugu masu wahalar sha’ani. Su ne idan suka yi tsanani ban da fuska har baya da kafada suke zuwa. To idan haka ne ke nan sai ka nemi likitan fata.

 

Da gaske shakar garin ganyen zogale ta hanci yana maganin amosanin kai?

Daga Umar Kano

 

Amsa: A’a wannan ba a likitancin da na karanta ba ne, sai dai ko wani likitancin na daban. Ka san likitancin iri-iri ne.

 

Me ke sa jijiyoyin kan mutum su rika tashi idan yana ciwon kai mai kuda?

Daga Dantanin Yalwa

 

Amsa: A wasu lokuta za ka ga irin wadannan jijiyoyi a kai ko a goshin mutum ko da babu matsala, a wasu lokuta kuma sai an dan samu wani abu ya kumburo su, kamar motsa jiki, ko damuwa wato stress, ko ma ciwon kai. Ko ma dai mene ne ya tada su, da an yi maganinsa za su kwanta.

 

Me zan rika yi in rage kiba, ina motsa jiki amma ba na raguwa.

Daga Abu Muhammad T.Y

 

Amsa: To ko sai ka je an auna nauyinka a asibiti a gani ko za ka bukaci tiyatar rage tumbi? Mu a likitance idan motsa jiki da rage ci suka ki aiki, kuma nauyi ya yi yawan da zai iya jawo wata matsala, to tiyatar rage ciki ake don cikinka ya koma kamar na dan yaro ka rika cin abinci kadan.

 

Akwai magunguna da mutum zai rika sha lokaci-lokaci ko da lafiyarsa kalau?

Daga Sani Dan-Katsina

 

Amsa: Eh, kuma a’a. Wato babu magani da mutum mai lafiya zai rika sha haka kawai. Amma akwai wasu magunguna da allurai na rigakafi da akan iya ba masu lafiya duk shekara domin kiyaye cututtuka, misali magungunan kiyaye cutar zazzabin maleriya ga wanda yake yawan samun ciwon, (kamar a lokacin damina) ko allurar kiyaye sankarau misali (lokacin bazara da zafi).