✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi: Ranar Wayar Da Kai akan Ciwon Daji na Mama

A ranar Lahadin nan ne za mu shiga ranaku da aka ware kacokan domin tunatarwa da mata akan hanyoyin kariya daga ciwon daji na mama.…

A ranar Lahadin nan ne za mu shiga ranaku da aka ware kacokan domin tunatarwa da mata akan hanyoyin kariya daga ciwon daji na mama. To wannan fili ma ba a bar shi a ba ya ba a bana. A yau za mu sake duba hanyoyin da mace za ta bi ta kiyaye kanta daga wannan annoba:

i. Babbar hanyar kare kai daga kamuwa daga kansar mama ita ce ta yawan shayarwa. Wato masana sun yi amanna cewa shayar da yaro a kalla tsawon shekara biyu yana iya kare mace daga kansar mama. Haka nan kuma yawan yaran da matar ta shayar, yawan kariyar kenan.

ii. Sai kuma rage kiba. Masana sun tabbatar da cewa mace mai kiba tana cikin hadarin kamuwa da ciwon sankarar mama musamman idan wata a danginta ta taba yin ciwon. Don haka sai an rage maiko a abinci a rika kuma yawan motsa jiki

iii. Sai kiyaye shan kwayoyin nan na ba da tazarar iyali wato pills. Wato kada mace kawai ta je kyamis ta saya ta sha, sai an tantance ta a asibiti ko za ta iya sha ko a’a. Domin su ma wadannan kwayoyi an tabbatar suna iya jawo wannan ciwo na sankarar mama. Idan da hali kenan a bi wasu hanyoyi ba ta wadannan kwayoyi ba ma zai fi. Wannan ce ma ta sa duk wata kwaya ko man shafawa mai sinadarin estrogen da mata kan saya ke da hadari.

ib. Duk matar da ta kai a kalla shekaru 40 yana da kyau ta koyi yadda ake duba mama. Wannan wata hanya ce da mace za ta iya ita kadai a dakinta ko ita da mai gidanta domin duba mamanta a madubi ko akwai wani canji a jiki. Yadda ake yi kuwa shi ne: mace ta tube a gaban katon madubi ta dora hannayenta kan kugunta, ta duba ta ga ko akwai wani yanayin canjin fata ko kurji ko kullutu ko kari a jikin mamanta. Bayan nan sai ta juya ta gefe ta sake yin haka (wato ta duba gefen dama da hagu). Daga nan sai ta sake kallon mudubin, ta sa hannunta na hagu a bangaren dama ta fara latsa gefe zuwa ciki, kasa zuwa sama, da karkashin hammata, ta ji ko za ta ji wani kullutu ko kari. Sai ta sake dawowa kan maman ta matso shi ko za ta ga wani ruwa ya fito (idan ba shayarwa take ba kenan). Idan ta gama sai ta je bangaren hagu ta yi kamar yadda ta yi a dama. Sai kuma ta daga maman duk biyun ta duba yanayin fatar karkashin a lokaci guda ko akwai wani miki. Idan babu komai shike nan ta gama sai bayan a kalla wata shida kafin ta sake. Amma idan ta ji wani kullutu ko ta matso wani kalar ruwa ko ta ga wani canjin yanayi a fatar, to dole sai ta je asibiti an kara bincike.