✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi: Me ke kawo jinin al’ada ga mai juna biyu? Cikina ya kai wata bakwai sai ga jini. Ko akwai damuwa?

Amsa: kwarai kuwa akwai damuwa, babu al’ada ga mai juna biyu. Duk wani zubar jini ga matar da aka tabbatar tana dauke da juna biyu…

Amsa: kwarai kuwa akwai damuwa, babu al’ada ga mai juna biyu. Duk wani zubar jini ga matar da aka tabbatar tana dauke da juna biyu matsala ce da bai kamata a yi jinkirin zuwa asibiti ba, don kada a rasa abin da ke ciki, ko kuma a yi da-kwance-uwa-kwance. Duk mai juna biyu da ta ga jini, to alamu ne na cewa cikin na samun matsala, wato tana cikin hadarin barar da shi. Idan aka samu juna biyu, al’ada daukewa take kwata-kwata har sai an haife da sati shida, wasu kuma sai ma sun yaye take dawowa.
Idan dai har tsakanin al’ada matar aure ta samu batan wata ko da sau daya ne, to a wannan lokacin a iya cewa akwai juna biyu, kuma ba sauran al’ada ke nan sai an haife. Yana da kyau a auna fitsari da tsinken gwaji, idan akwai ciki a je a fara awo. Idan ba ciki a jira al’adar wani watan, idan bai zo ba a je a ga likita.

Muna da yarinya ’yar kamar shekaru bakwai, amma ba ta magana, kuma komai ta samu sai ta kai baki, har kazanta. Muna magani na gida da na asibiti, amma ba sauki duk mun gaji. Ko akwai shawara?
Daga Musa K.

Amsa: Matsalar a irin wannan larura daga kwakwalwa ne, wadda take da wuyar sha’ani, da kuma wuyar warkewa, idan wani ciwo ya taba ta. Akan samu haka ne tun jariri na ciki ko kuma da zarar an haife shi. Idan yana ciki, yawanci ko shan wata guba a magunguna barkatai ko a buguwa na hadari ko shigar kwayar cuta irin su birus kan sa kwakwalwar ta tabu. Yayin haihuwa kuma ana iya samu a jariran da aka haifa bayan doguwar nakuda, saboda kwakwalwarsu takan sha wuya. Idan kuma bayan haihuwa ne irin ’yan zazzabin da ake rainawa na jarirai masu sa suma da sassandarewa su suka fi jawo hakan.
Ba ita kadai matsalar ta shafa ba, takan shafi miliyoyin yara a duk fadin duniya, sai dai na wani ya fi na wani. Wasu ba sa iya magana sai gwaranci, amma suna ji, wasu ba sa ji ba sa magana kuma ba sa tunani.

A hakikanin gaskiya irin wannan matsala, idan ta riga ta faru, ba ta da wata hanyar waraka sai dai lallami, da saka yaro ko yarinyar a hanyar da ta dace, kamar makarantar nakasassu irin tasu. A kasashen da suka ci gaba akwai wadannan makarantu da dama, amma akan samu akasin haka a kasarmu.