Me ke kawo ciwon zuciya ne? Kuma ko ana warkewa?
Daga Shu’aibu Abdurrashid, Makurdi da Abdulkareem Maiduguri
Amsa: Ciwon zuciya suna ne a dunkule na wasu cututtuka da sukan shafi zuciya. Wato dai ba ciwo daya ne kan shafi zuciya ba. Akwai nau’o’in cututtuka iri-iri da sukan shafi zuciya.
Ciwon zuciya shi ne kan gaba wajen kawo ajalin mutane da dama a kasashe masu arziki, domin an yi kiyasin cewa a kowane rabin minti mutum guda na mutuwa a sanadiyar ciwon zuciya a kasashen Yamma, duk da ci gaban da suka samu wajen wayewa da fahimtar cututtukan zuciya da aikin tiyata na zuciya.
Mu ma nan muna da nau’o’in cututtukan zuciya irin namu na kasashe matalauta, wadanda ba a jin duriyarsu a kasashen da suka ci gaba, misali ciwon zuciya wanda karancin jini kan haifar.
To sai ya kasance a yanzu sakamakon irin dabi’un rayuwa da wasunmu suka ara daga kasashen da suka ci gaba, wato rayuwar jin dadi, mu yanzu kusan muna da kowane nau’i na ciwon zuciya. A wannan kasar an yi bayanin cewa ciwon zuciya shi ne ciwon da ya fi hallaka manyan mutane a wannan zamani.
Ga wasu muhimmai daga cikin abubuwan da kan kawo ciwon zuciya:
1. Akwai ciwon zuciya wanda ake haifar jarirai da Irin wannan nau’i kan rabu kashi biyu; mai tsanani da marar tsanani. A mai tsananin sosai, wadansu jariran ma ba sa kwana, da an haife su suke komawa. A nau’in da ba tsanani kuma, jariri kan girma da shi ya kai minzalin babban mutum ba tare da ma an gane ba.
Alamun da za a iya gani a ce jariri na da wannan ciwo ya danganta da tsanani ko rashin tsananin ciwon da kuma ko wane iri ne. Wani lokaci ba wata alama da ake gani, kuma hakan na nufin yaro zai iya rayuwarsa lafiya sumul. Wani lokaci kuma, akan ga wasu alamu ko ma a rasa yaron cikin kankanen lokaci ko watanni.
Alamun sun hada da yawan haki a jarirai, ko a ga ba sa iya shan mama sosai, sai dai su sha kadan su huta, sannan su kara sha, ko a ga lebbansu suna duhu ko baki-baki maimakon ruwan hoda.
Za kuma a iya ganin kirjin su yana bal-bal saboda saurin da zuciyar ke yi wajen bugawa. Idan yaro ya fara magana, yakan iya cewa yana jin ciwon kirji, kuma za a ga bai cika shiga wasanni irin na yara ba, don ko ya shiga, yana saurin gajiya.
A iya kuma ganinsa yana yawan tsuguno don hutawa in ya shiga wasan yara, ko kuma ya yi wani dan gudu kadan. Za a iya ganinsa yana yawan tari, ko samun kumburin ciki, ko kumburin kafafu, sa’annan ba ya girma kamar sauran yara.
Wadansu iyayen a kauye a wannan lokaci ne suke samo wanzami ya yi wa yaro mai wannan alamu balli-balli a kirji, musamman idan an ga kirji na harbawa da sauri-sauri. Mu kuma mukan ba da shawarar kada a yi haka, a samu a kai mai wannan matsala asibiti a duba shi.
- Nau’in ciwon zuciya na biyu da za a yi bayani a kai shi ne wanda hawan jini kan Wato hawan jini na kawo ciwon zuciya. Amma hakan na faruwa ne idan hawan jinin ya dade a jikin mutum ba a sauko da shi ba ta hanyar shan magunguna wadanda za a iya samu a asibiti.
Mai wannan ciwo zai iya jin numfashi na sama-sama, musamman in ya kwanta, wanda hakan kan sa mutum kwanciya da matashi biyu ko uku. Numfashi sama-sama zai iya sa mutum ya kasa barci, domin da ya kwanta sai ya ji kamar an shake shi. Sai kuma a fara tari, da kumburin kafafuwa. Wani lokaci akwai ciwon kirji.
- Bayan hawan jini kuma, ciwo na gaba muhimmi mai kawo ciwon zuciya shi ne ciwon Idan aka ce mutum na da kiba, ana nufin mai ya yi masa yawa a jiki ke nan.
A kasashe irin namu, wadansu mutane har alfahari suke da mummunar kiba, saboda ba su san ciwo ba ne. Amma a kasashen da suka ci gaba, kullum za a ga masu kiba da ma marasa kibar, suna guje-guje don motsa jiki a filaye. saboda sun riga sun san illolin tara kiba.
Kiba tana lahani ga zuciya idan daskararren mai ya toshe magudanan jini da suke zagaye da zuciyar, don su ne suke ba ta nata kason na jini. Idan hakan ta faru bangaren da abin ya shafa a jikin zuciyar zai iya mutuwa, ya kuma jawo matsala ga zuciyar baki daya. Yawancin masu kiba kuma suna da hawan jini, wanda hakan kan hadu ya kara wa zuciya ciwo.
Babbar alamar da ake ji idan irin wannan ciwon ya kama mutum shi ne ciwon tsakiyar kirji, daidai saitin da zuciya take. Ciwon ya fi tashi idan aka dan yi wani dan kazar- kazar, ko aka ji mummunan labari.
Yakan lafa idan aka dan zauna aka huta. Za a iya ganin mutum yana zufa ko gumi idan ciwon ya yi tsanani, wanda hakan alama ce ta cewa dole a kai mutum asibiti cikin gaggawa kada zuciya ta buga.
- Sai kwayoyin cuta. Kwayoyin cuta daba-daban kan samu damar shiga cikin zuciya su samu wurin zama idan jini ya kwaso su daga wasu sassan jiki musamman wadanda suke daga baki da makogwaro, su sa wa zuciya Akwai irin wannan ciwon zuciya da kwayoyin cuta kan kawo har iri biyu, wato ‘Rheumatic Balbular Heart Disease’ mai kama murafan zuciya da ‘Infectibe Endocarditis’ mai kama tsokar naman zuciyar.
Kwayar cutar bakteriya ita ta fi samun sukuni a jikin zuciya, duk da cewa kwayoyi irin su virus da fungus sukan iya sa wa zuciya ciwo.
- Akwai kuma nau’in ciwon zuciya wanda ciwo a huhu kan Idan aka samu matsala a huhu matsalar takan iya shafar zuciya. Cututtukan huhu da za su iya sa ciwon zuciya sun hada da ciwon tarin fuka, da ciwon daji na huhu, wanda ya fi kama mashaya taba sigari.
- Akwai ma ciwon zuciya wanda muka ce karancin jini kan iya kawowa, musamman a mata masu ciki ko masu shayarwa wadanda suke da karancin
Yawancin cututtukan zuciya ba sa warkewa sai an kawar da abin da ya haddasa su, ko a yi dashen wani bangaren da ciwo ya taba, ko a yi ta shan magani har tsawon rayuwa.