✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi kan lafiya daban-daban

Matata ce ke da tarin fuka. An ba ta magunguna na wata shida ta fara sha. To amma har yanzu takan dan yi zazzabi. Shi…

Matata ce ke da tarin fuka. An ba ta magunguna na wata shida ta fara sha. To amma har yanzu takan dan yi zazzabi. Shi ne muke tambaya wannan yana da nasaba da ciwon tarin ne ko kuwa? Tana samun saukin tarin sosai, sai dai zazzabin.

 

Amsa: E, a wasu lokuta idan maganin kashe kwayar TB ya fara aiki yana fasa kananan kwayoyin halitta na cells wadanda suka hadidiye kwayoyin cutar. To wannan fasa kwayoyin halittu na cells zai iya samar da sinadarai a jiki masu sa zazzabi. Wannan ce kan sa wasu akan hada musu da maganin zazzabi na ‘yan kwanaki. To idan ma ba a hada wa mutum ba, idan yana jin zazzabi zai iya sayen ‘yan kwayoyin kashe zazzabi kamar fanadal ya sha duk lokacin da ya ji alamun zazzabin ba tare da ya ajiye wadancan magunguna ba. Idan kuma zazzabin ya lafa a daina sha, a ci-gaba da kwayoyin maganin na watannin da suka rage. Sa’annan a tabbatar ana samun abinci mai gina jiki da mai kara bitaman irinsu kayan ganye da ‘ya’yan itatuwa a kullum. Wannan daina tari da ta yi alama ce ta cewa maganin na aiki.

 

Ko za a min bayani akan abin da ke kawo kofofin gashi a fuskar mutum? Kuma ta yaya za a magance hakan?

Daga Umar Sani, Kaduna

Amsa: A’a Mallam Umar ai kofofon gashi a ko wane bangare suka fito a jikin dan Adam ba matsalar lafiya ba ce. Da ma ai a jikin ‘yan Adam akwai kofofin gashi. Da kamar a jikinmu ba kofofin gashi to fitowarsu shine ciwo ko tangarda. Abinda kawai ke faruwa shine mutum na kara girma wasu kofofin gashin na kara budewa a wasu bangarori na jiki, kamar fuska, wadda sai kana yawan aski ne ma za ka ga kofofin gashin baro-baro in ka kalli mudubi.

Me ya sa suma ba ta fitowa a wasu sassan jikin mata sai dai sassan jikin maza?

Daga Garba Sabiyola, Gashuwa

Amsa: Saboda sinadaran da ke jikin mace ba su cika maida hankali wajen tofo da gashi a sassan jiki ba kamar yadda sinadarin testosterone yake maida hankali wajen tofo wa maza gashi a kusan ko’ina a jiki. 

 

Ni ban cika yin barcin rana ba, kuma idan na kwanta da dare sai na kai asuba ban yi barci ba. Sai dai fa bayan asubar ne ya ke zuwa na ‘yan wasu awoyi. To ko akwai matsala kenan?

Alhaji G.B.S., Kano

Amsa: E, akwai matsala, tunda ba ka samun awoyi da suka kamata a ce ana samu a barci, kamar awoyi shida zuwa takwas a rana. Sai dai kai ne da kanka za ka zauna ka wa kanka hisabin dalilin da ke kawo maka wannan matsala. Domin watakila ka san akwai abubuwa masu hana barci, in dai kana bin wannan shafi. Sai ka tsaya tsai ka lura mene ne a rayukarka a rana tun daga safe har dare kake yi da zai iya hana barci? Shaye-shayen shayi da kofi masu karfi ne ko lemuka ko kuma cin goro, ko yawan tunani, ko damuwa ko rashin motsa jiki, ko rashin cin lafiyayyen abinci da dare ne ke kawo maka wadannan. Idan ka gano dalili Kenan zaka iya gujewa abin. Idan kuma ka kasa gano dalili watakila sai ka je likita ya auna lafiyarka kamar su hawan jini da sauransu.

 

Wai shin me ke kawo jan lebe ne a wasu mutane? Shin ciwo ne ko bambancin halitta?

Daga Idris Abba, Kaduna

Amsa: Akwai wasu matsalolin lafiya da za su iya zama bambancin halitta za kuma su iya zama alamu na wani ciwo. To jan lebe yana daya daga cikin wannan. Don haka babu tabbas a ce alamun ciwon ne ko kuma bambancin halitta ne, sai likita ya ji bayanin rayuwar mutum ya kuma duba mutum musamman ma idan da can shi mutumin ba shi da jan leben sai daga baya abun ya zo.

Wai shin cin dabino yana da illa ne ga mai ciwon suga ko kuwa babu?

Daga Umar Muhammad, Maiduguri

Amsa: A’a don dai cin dabino kwaya daya zuwa uku a rana ga mai ciwon suga ba zai rikita masa sugan jininsa ba in dai yana kan magunguna. A tasa shi dabinon a gaba ne a rika ci kamar abinci shi ne zai iya hargitsa lissafi.

 

Wai shan lemon coka cola a kullum yana da wata illa ne?

Daga Muhammad danBorno, Da Umar A., Kano

Amsa: E in dai kuna kona sukari da gishirin da ke cikin lemon ai ba matsala. Wato in dai aikin karfi kuke, ko kuma a ko yaushe kuna motsa jiki ai ba matsala. Dama wadanda ke sha alhalin aikinsu zama ya gada sune ake cewa su rage irin wannan shaye-shayen lemukan zaki na kwalba, ba masu kazar-kazar sosai ba.

 

Ko mene ne amfanin cin yalo da data ga jikin dan Adam?

Daga S. Umar, Malumfashi da Nasiru Kainuwa, Hadejia

Amsa: E, ai da yake yalo da data na daga cikin ‘ya’yan itatuwa, suna da amfani sosai a jikin mutum, wadanda su ma ke da sinadaran bitaman na rukunin B da sinadaran ma’adinan potassium. Za a iya cin su a kullum idan an samu ba wata matsala in dai an wankesu sosai kafin a ci din. Sune ma nau’ukan abincin da ya kamata a ce ana ci a kullum ba lemukan zaki ba.

 

Wai da gaske ne karas yana kara lafiyar idanu idan ana yawan cin sa?

Daga Munnir A., Kano

Amsa: E, da gaske ne Mallam Munir. Ai a nan ma an sha fada cewa akwai sinadarin beta-carotene da na bitaman rukunin A masu kara kaifin gani da lafiyar kwayar ido.