Wai mene ne amfanin ruwan soda wanda wasu kamfunan saida lemo ke sayarwa?
Amsa: Ai abin da ake nufi da soda shi ne gishiri a Hausance. Wato ruwan soda ke nan ruwan gishiri ne, domin soda sinadari ne na sodium, wanda gishiri ne. Sai dai sukan sa dan sukari, shi ya sa za ka ji dan zaki. Mu a likitance kuma bai kamata a sha ruwan gishiri da suga ba idan mutum lafiyarsa kalau, sai dai idan gudawa yake, ko idan ya kasa cin wani abu, wato ba abin da ke masa dadi a baki dalilin wata rashin lafiya. Shi ma a hakan sai an tambayi likita, domin akwai cutukan ma da ba a son a sha ruwan gishiri kamar hawan jini da ciwon koda.
Su lemukan kwalba masu gas kusan dukansu suna da irin wannan soda, sai dai yawansu bai kai a ce musu ruwan soda ba. Shi ya sa ruwan soda yake daban da sauran, shi ne kuma yakan sa wasu lokuta mukan yarda wasu su sha lemon kwalba amma ba lemon ruwan soda ba. Da fatan ka fahimci bambancin da ke tsakanininsu.
Ko idan mutum ya ji yunwa zai iya shan alawa don ya dan kwantar da yunwar? Ko kuwa a’a?
Daga Nasiru Kainuwa Hadejia
Amsa: kwarai kuwa idan mutum yana jin yunwa sosai irin mai rikitarwar nan, mutum ya ji jikinsa na kyarma don yunwa, jiri da ciwon kai na kwasarsa, tabbas ana so ya nemi wani abu mai zaki wanda za a samu jiki ya tsotse shi cikin mintuna kafin ya samu abinci sosai. Irin wadannan abubuwa mai suga sun hada da alawa, cakulet, lemo mai suga, kwayar suga kanta (sugar cube), dabino, mazarkwaila da sauransu. Wato ke nan abubuwa masu zaki suna da rana, irin wannan rana da aka ji matsanaciyar yunwa mai rikitarwa. Haka nan ko mutum mai ciwon suga idan ya fara jin alamun yunwa ko karancin suga a jikinsa an yarda ya sha ko ya ci daya daga cikin wadannan abubuwa domin sugansa ya dan farfado. Yawanci su masu ciwon sugan ai sun san alamun da ake magana, alamun yunwa da karancin suga na kyarma da zufa da jin jiri da ciwon kai da gani dishi-dishi.
Ina so in san amfanin fatar shanu a jikin mutum.
Daga Aliyu Isa
Amsa: Idan na fahimce ka kana nufin abincin nan da ake kira ganda ke nan. Masana cimaka wato nutritionists sun ce fatar sa, wato ganda wani nau’i ne na kitse kawai ba nama ba. Don haka duk mai cin ganda ya san cewa ba nama yake ci ba, wani nau’i na kitse yake ci, wanda kuma muka sha fadar cewa sai an yi taka-tsantsan wajen cinsa domin shi ma zai iya kara wa mai cinsa kitse a jiki.
Ni mutum ne ma’abocin cin kayan fulawa irinsu burodi gurasa da funkasau da ire-irensu. Shin ko yawan cin wadannan zai iya zama matsala ga lafiyata?
Daga Reezan Wushishi
Amsa: A’a ai kowa yana bukatar kayan abinci masu kara kuzari irinsu kayan fulawa. Inda gizo ke saka shi ne mukan yi musu cin fitar hankali, wato sai mun take ciki. To in dai za ka rika cinsu saisa-saisa daidai gwargwado ba sai ka take ciki ba ai babu komai.
Shin me yake sa idan ina cin abinci ko wane iri ne zufa ke karyo mini ta ka, har tana gangarowa? Ko hakan matsala ce?
Daga Ibrahim, Deidei
Amsa: In dai abinci mai zafi ne to ba matsala ba ce, in kuma abinci mai sanyi ne, tunda ka ce abinci ko wane iri ne, to shi ne za a ce akwai matsala. Don haka idan na farkon ne, wato matsalar sai ka ci abinci mai zafi ko mai dumi take faruwa to ba komai, amma idan mai sanyi ma na sa ka zufa sai an binciki lafiyarka.
Ni kuma ina zufa ne kawai a tafin hannuwa da na kafafuwa ko a wannan yanayi da ba na zafi ba. Mece ce mafita?
Daga Abba Saraki, Birnin-Kebbi
Amsa: E, akwai wasu nau’in mutane wadanda a tafin hannu da kafa kawai suka fi yin zufa. Mafita ita ce ka nemi likitan fata wanda zai rubuta maka magani ko ya ba ka shawarwari.
Na taba yin tarin lumonia a yarinta, to amma a yanzu ni kullum ina cikin mura da tari. Ko akwai alaka? Ina kuma son shawara.
Daga Rufa’i Mai Ja’o’ji da Kabiru ‘Yan Dadi
Amsa: E, za ta iya yiwuwa wata lumoniyar ce. Domin ita cutar lumoniya tana warkewa, sa’annan wata sa’a ta dawo a lokuta mabambanta. Abin da dai ya fi shi ne a ga likitan da zai duba ku ya sa abin sauraron kirji ya ji kirjin, ya ba da gwaje-gwaje kamar na hoton kirji, sa’annan ya tantace ko lumoniyar ce ko wani tarin ne na daban.
Ko dai matsalar ciwon cikin appendid na faruwa fiye da sau daya a jikin mutum ne? Domin ni an mini tiyata an cire appendid din amma sai na ji wani irin ciwon a gefen haguna. Ko zai iya tashi a daya gefen?
Daga Ummu Malik
Amsa: A’a appendid daya ne a cikin mutum kuma a bangaren dama yake. Idan kika sake jin irin ciwon ciki mai kama da waccan matsalar to wata matsalar ce daban ba ta appendid ba. Akwai halittu da dama a wannan bangare na hagu da kan iya kawo miki irin wannan matsala tun daga babban hanji, zuwa mafitsara da shekar kwai ta obaries tunda ke mace ce, da sauran wasu sassan jiki duk dai a nan gefen. Don haka kenan sai an duba an tantance a ina wannan sabuwar matsalar take kenan.