✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi kan lafiya daban-daban

Shin yawan fitowar maruru matsala ce? Ni ina da matsalar maruru kusan shekaru biyar. Idan na sha magani ya tafi amma sai ya dawo. Me…

Shin yawan fitowar maruru matsala ce? Ni ina da matsalar maruru kusan shekaru biyar. Idan na sha magani ya tafi amma sai ya dawo. Me ya kamata na rika sha domin kiyaye aukuwar hakan?

Daga Baban Abbas, Kaduna

Amsa: E yawan fitowar maruru matsala ce. kwayoyin cuta na bacteria ke kawosu. Suna jin magani. Sai dai idan ruwan daya ya taba wani wurin da babu, to zai iya fitowa. Shi ya sa ko ka yi masa magani idan ba kiyaye aukuwarsa kake ba zai dade bai rabu da kai ba. Don haka kiyaye aukuwarsa shi ne muhimmi. Hanyoyin da za ka bi kuwa wajen kiyaye aukuwar ta sa masu sauki ne, kuma sun hada da:

1-Kiyaye tsabtar jiki da ta kayan sawa da ta kayan wanka ta hanyar yin wanka akalla sau daya a rana da yawan wanke suturar sa wa a kalla bayan sa wa biyu.

2-Yawan aske gashin hammata da na matse-matsin cinyoyi zai rage fitowar maruru.

3-Dole kuma askin sai da abu mai tsabta ko wanda aka tafasa ko aka sa wa ruwan spirit idan an taba amfani da shi a baya.

4-Wasu za su ga ana shafa musu ruwan kashe kwayoyin cuta na spirit bayan an yi gyaran fuska, to duk domin a kiyaye aukuwar irin wannan matsalar ne.

5-Idan hakan bai yi maganin maruru ba, za a iya soma wanka da sabulu mai kashe kwayoyin cuta na fata wato antiseptic.

6-Idan har wa yau ba su daina damun mutum ba to dole a je a yi gwajin suga, a tabbatar ba ciwon suga ne ke damun mutum ba.

7-A bar maruru ya fashe da kansa (kada a fasa shi ta karfi), sai a wanke wurin da ruwa da sabulu na musamman, wato antiseptic, a tsane wurin da sauri domin in ruwan marurun ya taba fata mai lafiya ba a wanke da wuri ba, zai iya sake dawowa.

8-Cin abinci da ’ya’yan itatuwa na marmari kan gina kwayoyin halitta na garkuwar jiki wadanda su ne idan kwayar cutar ta shigo cikin fata kan yi maganinta.

8-Idan maruru ya dade yana zogi kuma bai fashe da kansa ba, kamar wanda ke fitowa bayan an yi allura, dole a je asibiti a tsaga, a fitar da ruwan diwar da wuri, a karbi kuma magunguna.

9-A je a ga likitan fata idan an yi duk wadannan amma ba a dace ba.

Me ke sa kirjin mutum ya rika tsira kamar zai bude?

Daga Muhammad Tsagero

Amsa: Akwai abubuwa da dan dama da za su iya kawo maka wannan, kuma babba daga cikinsu, musamman idan ka manyanta, shi ne ciwon zuciya wato kamar bugun zuciya kenan, wanda zai iya irin wannan tsira a tsakiyar kirji na dan wani lokaci kafin ya saki, daga bisani ya sake dawowa, a wasu kuma ba ya saki sai zuciyar ma ta buga. Banda wannan akwai gyambon ciki shi ma zai iya zuwa da wannan alama, sai kuma tarin numoniya wato ciwon hakarkari, akwai ma buguwa wadda ita ma za ta iya kawo haka. Abin da dai ya fi shi ne mai jin irin wannan kada ya zauna, ya tashi ya je a duba a ga ko wane ne daga cikin wadannan, kada karamar magana ta zamo babba.

Ni ina da ciwon asma amma sai ta dade ba ta tashi ba. Ko zan iya zuwa karbar maganin shaka a asibiti?

Daga M. Bado, Kawo

Amsa: To shi likitan da ya ce maka kana da ciwon asma bai fada maka abubuwan da zaka rika sha ko shaka ba ne? Ko kuwa kawai kai ka duba kanka ka yanke cewa ciwon asma ne da kai?

Ni ina jika lemon tsami da ganyen shayi da lemon kara kuzari wato energy drink duka ina sha lokaci guda. Ko hakan zai iya mini illa?

Daga S. Haruna Shittu

Amsa: E, ga alama wannan jiko naka ba ya cikin tsarin kiwon lafiya, kuma zai iya maka illa in dai baka daina ba. Abinda zai bata hadin shi ne wancan lemo na energy drink wanda ka ce kana sa wa. Su wadannan lemuka akwai sinadarai iri-iri a cikinsu da masu ilimin cimaka na kimiyya ba su yarda da su ba.

Ni saurayi ne dan shekaru 32 amma na kan sha madarar gwangwani a kalla sau uku a sati domin na yi kiba. Ko hakan na da matsala? 

Daga Isma’il Yusuf, Jigawa da Hasan M. Sokoto

Amsa: Ga alama ku baki ne a wannan fili. Ai ba kiba za ku ce ba, lafiya za ka ce, domin mu a likitance kiba ciwo ne. Idan mutum kuma na son ya yi lafiya ba madara kadai ya kamata ya rika sha ba, Akwai cimakar da muka sha bayyanawa a nan ta balanced diet wato daidaitacciyar cimaka wadda ta hada da cin duk wani ajin abinci da ka sani a kalla sau daya a rana. Azuzuwan abincin kuma idan ka duba jaridun ‘yan watannin baya za ka gan su. Wadannan sune za su ba ku duk irin karfi da kuzari da lafiya da kuke bukata.

Wai shin me ke kawo wa mutum mura da rufewar hanci da kaikayin kunne?

Daga Abdulkadir Isa, Lagos

Amsa: Mafi yawancin abubuwan da kan kawo wannan kwayoyin cuta ne. A kwayoyin cutar ma akwai iri biyu na bacteria da na birus. Na birus da kansu suke tafiya bayan ‘yan kwanaki, na bacteria kuma sai an sha musu magani. Watakila kai ba za ka iya bambance wadanne irin kwayoyi ba ne don haka sai ka tuntubi likita zai duba ya gani ko na birus din ne ko a’a.