Ni na kasance tun ina yaro na yi wani ciwo. A yanzu kuma akwai tabonsa a jikina tun daga wuya har kafa. Shi ne na ke son shawarar yadda zan yi su rabu da ni.
Amsa: To ai duk kusan yaran zamanin da masu wasa a waje kamar buga ‘yar tile ba takalmi, da yawan yawo a gari a kafa ko a keke, duk haka muke da tabuna iri-iri na jin ciwo da tuntube. Wasu kuma ciwo suka yi irinsu kyanda da agana da ta bar musu tabo duk jiki. Don haka da wuya a wannan zamani ka samu wanda ya ba shekaru 30 baya a ce ba ya da tabuna a jikinsa. Sai dai kawai na wani ya fi na wani. Wasu kuma saboda dadin rayuwa nasu ma sun fara bajewa.
Duk da haka dai ba za a ce ka kyale su ba in dai kana da halin ganin irin wancan likita na kwalliyar fata wato plastic surgeon. Za ka iya nemansa a babban asibiti mafi kusa da kai, ya ga tabunan ya ba ka shawara.
Ko akwai maganin da mutum zai amfani da shi kasumba ta daina fito masa?
Daga Wise Boy
Amsa: A’a ban zo wannan karatun ba tukuna. Amma dai kai ma idan ka tuntubi likitan fata ko na kwalliyar fata watakila su fada maka dabarar da akan yi, don rage yawan suma a jiki.
Ni kuma hadari na yi wata uku kenan, na ji rauni a kafa, aka mini wankin ciwo a asibiti. Sai dai har yanzu kamar wurin bai warke ba, domin ruwa na fitowa a wurin. Shi ne nake tambaya ko akwai matsala ne?
Daga Adam Jibril
Amsa: E, tunda wuri bai warke sarai ba da alama akwai matsala. Shawara ka samu babban asibiti mafi kusa da kai a bangaren tiyata ka ga wani likita a cikin masu tiyata ya duba wurin a yi hotuna a gani.
Mene ne ke kawo yawan ciwon idanu da kaikayi ko kuma su rika yin ruwa?
Daga Aliyu A., Malam Madori
Amsa: Manya daga ciki akwai canjin yanayi, ko raunin idanun, wato idanun sun fara tsufa. Amma dai likitan idanu shine ke da hurumin tantance wane ne a cikinsu. Don haka yana da kyau a duba.
Matata duk lokacin sanyi mukan ga halayenta na canzawa. Mun yi maganin gida amma abin ya faskara. Shi ne muke tambayar irin asibiti da likitan da za mu gani
Daga M.L., Bauchi
Amsa: Babban asibiti kamar nan General ko asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa balewa za ku je ku bude fayil bangaren kwakwalwa na psychiatry, a dubata a fada muku ko lafiyarta kalau ko kuma akasin haka.
Idan bugun jinin mutum yana yawan sauka me ya kamata ya rika yi?
Daga Bello Tata, Kano
Amsa: Babban abinda mai samun saukar bugun jini wato hypotension, ya kamata ya yi shine ya je a bincika masa mene ne takamaimai ke kawo jinin nasa ke kasa. Ta haka ne za a gano masa magani.
Ko cin doya da dankali da rogo ga mai ciwon suga zai iya masa illa?
Daga Umar Muhammad Maiduguri
Amsa: A’a ai su wadannan nau’ukan abinci masu starchi muna musu lakabi da abinci masu daukar lokaci kafin su narke, wato suna da low glycaemic inded, ba sa daga sukarin jini sosai. Sauran sune wake, alkama, maiwa da kayan ganye da na ‘ya’yan itatuwa. Wadannan na’ukan abinci mai ciwon suga zai iya cinsu duk lokacin da ya ga dama, in dai ba likitanka ba ne ya dakatar da su. Akwai kuma nau’ukan abinci wadanda ba a so mai ciwon suga ya rika yawan ci irinsu taliya, shinkafa, macaroni da tuwon masara. Don haka irinsu sai an yi a hankali da su. Kuma yana da kyau mai ciwon suga ya rika hirar irin abincin da ya kamata ya rika ci a wurin likitansa.
Idan aka hada kayan marmari daban-daban kamar lemo da abarba da ayaba a matsayin fruit salad aka ci, sai aka ji bayan gida, shin hakan matsala ce?
Daga danladi, Kaduna
Amsa: Ai ka san akwai bambancin bayan gida da gudawa. Bayan an sha wadannan ‘ya’yan itatuwa, idan ciki ya kama ciwo ko yana murdawa kuma bayan gidan da aka yi aka ga gudawa ce sosai, to tabbas akwai matsala kenan, wato watakila ba a wanke kayan marmarin sosai ba, ko wadda ta hada bata tsabtace hannayenta yadda ya kamata ba kafin ta yi aikin hada wannan salad.
Wai da gaske koren ganyen shayi hade da zuma na kara lafiyar kwakwalwa?
Daga Aliyu B.A
Amsa: Dukansu biyun suna taimakawa lafiyar jiki gaba daya ba wai kwakwalwa kawai ba domin dukansu suna tsane gubar da ke taruwa a jini da muke kira free radicals. Don haka idan ana amfani da su za a iya samun wannan fa’ida.
Wai yawan shan shayi da kayan kamshi da na yaji suna iya sa matsala?
Daga Baban Abbas, Kano
Amsa: A’a idan bangon cikinka mai kwari ne ba ka samun tashi gas a ciki irin na olsa, za ka iya shan abinka. Masu irin wannan matsalar tarin acid a ciki ne suke samun matsala idan suna yawan shan kayan kamshi da na yaji.
Duk abinda na ci ko na sha ni kuma sai cikina ya kulle. Ko akwai matsala?
Daga Ashiru A. Tafa
Amsa: E, akwai matsala mana Mallam dahiru, tunda ai da ba haka kake ba a da ko. Don haka kana bukatar a duba cikin a ga mene ne takamaimai ke damunsa kenan.
Wai da gaske ne yawan sa kwalli a ido yana bata lafiyar idon?
Daga Iliyasu Akuyam
Amsa: Ka san kwallin iri-iri ne. Idan za ka samu na ainihi angariya ba zai bata maka ido ba, amma a yanzu garin kwalli da dama za ka ga ana sa musu dalma a ciki wato lead. To wannan dalma tana iya bata lafiyar ido