Shekaruna 55. Na ba wa ’ya’yana jinina ne, shi ne nake tambaya ko akwai matsala? Domin ni dai ban ji komai ba.
Daga Musan Radda
Amsa: A’a in dai ba yaran naka suna da yawa ba sannan kuma ba ka da wani ciwo ai ba komai. Sai ka haura shekara 65 ne za a ce ka huta da bada jini. Sai dai na ji ka ce ’ya’ya, suna da yawa ke nan? Domin ba a so a debi abin da ya haura rabin lita wato milimita 500 a zama guda. Za ka kuma iya badawa bayan kowane wata uku.
Idan ina karatu sai in rika jin barci. Mene ne mafita?
Daga Usman 440
Amsa: Mafita ita ce ka rika karatu lokacin da a al’ada ba lokutan barci ba ne. Kamar da safe da hantsi ko da yamma, amma ba da rana tsaka koda dare. Yawancin dalibai suna kuskuren cewa wai sai da dare ne za su yi karatu, musamman idan jarrabawa ta zo.
Ni tafin hannuna ne ke da karfi sosai, shi ne nake tambaya ko akwai wani mai da zan yi amfani da shi domin ya yi laushi?
Daga Kamaluddeen Gusau
Amsa: Yawanci kyawun fata ba a man shafawa ba ne, a yanayi ne da ci-maka da yanayin aiki. Misali ko ka shafa man shafawa mai kyau idan aikin daukar bulo kake da hannayenka da wuya su yi laushi, sai dai idan kana sa safar hannu
Ni kuma gabobin hannayena ne ke yin baki kuma ba sigari nake sha ba. Na dai san na yi aiki da bakar rama na wanke amma ta ki fita.
Daga Baban Maryam, Pandogari
Amsa: Yauwa to ka ga wannan watakila daga aikinka ne. Watakila idan kana sa safar hannu idan za ka yi aikin abin zai ragu ka ma daina gani.
Na je an auna mini ko ina da hawan jini sai aka ga 160/90, to amma sai nake shakka ko daga abin aunawar ne.
Daga Abdulkareem G. Maiduguri
Amsa: A’a ai saboda kawar da kokwanto mu ma idan aka auna hawan jini sau daya kacal muna cewa a sake aunawa a wani lokaci na daban kashi na biyu. Idan awo na biyun ma ya yi sama kamar wannan to ba makawa akwai hawan jini.
Idan ban ci abinci ba wani lokaci ina jin juwa.
Daga Khalifa Kabir, Pandogari
Amsa: Ni ma a wasu lokuta idan na dade ban ci abinci ba nakan ji jiwa, alamu ne na cewa sugan jinin mutum ya yi kasa
Wai shin ko akwai maganin iskokai a asibiti? Idan akwai a fada mini maganin.
Daga Ashiru Katsina
Amsa: Eh, idan aka kai mai ciwon asibiti wurin likitan kwakwalwa zai iya dubawa ya gani ko akwai iskokai ko babu, sai ya ba da magani ko ya fadi abin da ya dace. Yawanci likitocin kwakwalwa su ne suke tantance wannan.
Me ke sa mutum ya rika jin idanunsa na zafi har a ga jini a cikin kwayar idon?
Daga M.M
Amsa: Wannan tabbas yana nuni da matsala ce. Sai ka nemi likitan ido ya duba.
Me ke kawo ciwon kafa a manyan mutane, ka ga a wasu lokuta ba ma sa iya tafiya?
Daga Murtala I. Birnin Gwari
Amsa: Cututtuka ne da dama, tun daga shi kansa tsufan zuwa karancin sinadaran bitaman da kashi kan bukata wato bitaman na D da calcium, zuwa ciwon sanyin kashi zuwa hawan jini wanda kan iya sa mutuwar barin jiki. Cututtuka dai birjik ga su nan duk za su iya jawo wannan.
Ina son zama likita. Ta wace hanya za ka taimaka mini in cika burina?
Daga Yahya Usman Muhammad
Amsa: An taba ba da cikakkiyar amsar wannan tambaya a jaridar ranar 9 na watan Yuli shekarar 2017, inda aka amsa irinta ga wani mai karatu Isa Ali. Don haka ka nemi wannan jaridar ta waccan rana ko da a shafin Aminiya na Intanet ne
Jin yawan ciwon kai da zafin jiki alamun mene ne?
Daga Ahmad Isa Jibrin
Amsa: Kai kana Najeriya ba ka san wadannan alamun mene ne ba? Anya! To idan mutum yana jin zafin jiki da ciwon kai babban abin da aka fi tunani shi ne zazzabin cizon sauro, sai zazzabin typhoid sai kuma ciwon mura. Sai mutum ya je likita ya tantance masa.
Wai a ina ake samun allurar rigakafin ciwon typhoid ne? Na nema a Gombe ban samu ba.
Daga Haruna Usman Gombe
Amsa: Idan ka ji na yi wa wani kwatance to na san garin da ma asibitocin garin ne. Gombe ban san ta sosai ba ballantana in ce maka ga inda za ka samu. Manyan asibitocinku kana nufin babu wannan allura? Tabbas akwai allurar rigakafin ciwon typhoid mai suna typhired a Najeriya.
Lurwanu Musa Malumfashi kuma yana so a ba shi dama ne ya ja hankalin mutane musamman ganin karatowar lokacin zafi. Yana fadakar da jama’a a kan kwana cikin gidan sauro da kuma tsabtace muhalli kamar tsabtace kwatoci, domin kiyaye cizon sauro. A bangaren kiyaye cututtuka masu alaka da yanayin zafi kuma ya kamata mu kula da tsabtar abinci da abin sha, sai tsabtar jiki da ta tufafi, sai kwanciya wurin da iska ke zagayawa wato bentilation.