Da gaske ne ciwon tarin TB yakan iya daukar tsawon shekaru biyar bai bayyana ba?
Daga Saminu Usman, Daudawa
Amsa: kwarai, kwayoyin tarin fuka ko na TB wadanda ake kira Mycobacterium sukan iya zama a cikin huhun mutum tun daga lokacin da suka shiga jiki a yarinta ko a kuruciya har mutuwarsa ba su nuna alamu ko sun kawo masa ciwon tari ba. Wato za ta iya yiwuwa kwayoyin su shiga huhu amma sai kwayoyin garkuwar jiki su yi maza su hadiye su, su sanya kwayoyin cutar su kasa komai, amma ba sa iya kashe su (duba hoton wannan shafi na makon jiya domin karin bayani). Kuma a hakan mutum ba zai iya yada su ba tunda kamar a kulle suke ke nan. To amma yayin da wadannan kwayoyin garkuwar jiki suka samu rauni sai su amayar da kwayoyin cutar su kuma su yi ta varnar da za su yi har sai an kawo dauki ta hanyar magunguna. Ka ga ke nan idan cikin shekaru biyar hakan ta faru ba mamaki. Zai iya faruwa ma ke nan bayan shekaru goma ko ma bayan shekara guda da shigar kwayoyin cikin huhu.
Ya kamata a san cewa a irin kasashenmu inda ayyuka da harkokin kiwon lafiya ke da rauni, akasarin mutane suna da wannan kwayar cutar a tare da su amma ba ta yi musu illa ko nuna alama saboda karfin garkuwar jiki. Sai garkuwar jiki ta karye ake alamun ciwon. Su kuma kasashe masu karfin harkokin kiwon lafiya tuni suka yi ikirarin kawar da wannan kwayar cuta daga kasashensu, domin ko an ganta ma a jikin wani to bako ne ya kai musu. Wannan ce takan sa kasashen sukan bukaci mutane masu son zuwa kasashensu karatu ko zama na wasu shekaru ’yan asalin nahiyar Afirka da Indiya su yi hoton kirji da gwajin majina, domin a gano ko akwai ita kwayar cutar a sarari wadda mutum zai iya yadawa ko babu. Idan aka gano wannan kwayoyi a jikin mutum kusan ba za su bar shi ya shiga ba sai ya sha magani ya warke.
To su mutanen wadannan kasashe su ne za a iya cewa da yawansu babu kwayoyin cutar a kirjinsu, amma da sun zo irin kasashenmu su ma za su iya kamuwa amma garkuwar jikinsu mai kwari ce sai su hadiye su.
Ni kuma ina son sanin bambancin tarin fuka da tarin numoniya
Daga Kabir A. Kebbi
Amsa: Akwai bambancin tarin fuka da tarin numoniya da ma sauran tari wanda ba na numoniya ba, irinsu tarin shika da sauransu. Tarin fuka kwayar cuta iri guda ce ke kawo ta ta bacteria wadda muka fadi sunanta a sama, shi kuma tarin numoniya kwayoyi daban-daban ne ke kawowa, tun daga bacteria zuwa virus zuwa fungus. Su kwayoyin da ke kawo numoniya sukan fi karfin garkuwar jiki a lokuta da dama saboda yawansu, ta yadda yanzun nan da sun shiga huhu za su fara sa alamomin ciwon kirji, tari da zazzavi, har sai an sha magani. Shi ma TB yana sa ciwon kirji, tari da zazzavin dare.
Yawanci maganin sati guda zuwa kwana goma ya isa ya kashe kwayoyin numoniya, amma kwayoyin tarin fuka ko, maganin da zai kashe su ba daya ba ne ba biyu ba, domin sai an hada uku zuwa hudu suke jin bugu kuma sai sun dauki watanni da dama kafin wadannan su ci nasara a kan su kwayoyin cutar.
Me ke sa mutum ya rika jin vangaren hagu na hakarkari ko awuzonsa na ciwo ko halbawa? Ko alama ce ta wani ciwo? Mece ce shawara?
Daga Sani K.
Amsa: A vangaren kirji a hagu, akwai abubuwa da dama da ka iya jawo ciwo tun daga huhu zuwa kahon zuci domin kahon zuci ma ya karkato wajen. Don haka idan aka ji wurin na ciwo, to a iya cewa kashin wurin ne ko tsokar wurin amma idan harbawa da dukan uku-uku, wani lokaci kuma a samu kullewa alama ce ta cewa akwai wata matsala a zuciya din wadda wannan na nufin dole sai mutum ya je an bincika a tantance ko wace irin matsala ce.
Me ke kawo ciwon olsa? Kuma wace irin hanya zan bi domin magance
cutar? Domin tana matukar bani matsala, sa’annan kuma wai shin ana
warkewa?
Daga Hamidan Badamasi [email protected]
Amsa: Shi ma ciwon olsa babbar alamarsa shi ne ciwon tsakiyar ciki zuwa tsakiyar kirji. Kowane mutum yana da wani ruwan acid da cikinsa ke samarwa amma a wasu mutane wannan acid din kan yi wa bangon cikinsa illa saboda ba kwari sosai ko saboda kasancewar wasu kwayoyin cuta na bacteriya da ake kira H.pylori, wadanda da su da acid din sukan hadu su kawo rami ko kwarzane a bangon ciki da ake kira olsa ko gyambon ciki. Barin ciki ba abinci kan zafafa wannan kuna na acid a kan ciwon tunda idan akwai abinci a cikin acid din abinci zai tava ba bangon ciki ba. A wasu lokuta kuma ba gyambo haka kawai yawan acid din ke kawo kunar zuci.
Ko ma dai mene ne ana iya warkewa tsab daga wannan matsala idan mutum ya je aka duba shi aka tabbatar ita olsar ce, aka ba shi magunguna na tsawon makonni. A wasu sai an sa kyamara an haska an gani ko gymabon ne ko wani abu daban.
Me ke kawo mutum yake jin wani abu kamar kiyashi yana yawo ajikinsa?
Kuma wane irin magani wanda yake da irin wannan lalurar zai nema?
Daga Mansoor Sa’id PRP [email protected]
Amsa: Wannan tambaya ma mun sha amsa ta a wannan shafi. Kuma abin da mukan ce shi ne yawanci matsala ce ta jijiyoyin laka ke samun matsala suke aika sakonni ga kwakwalwa na jin tafiyar kiyashi. Yawanci cututtukan suga da na koda sukan sa taruwar suga ko wata guba a jikin jijiyoyin. Akwai na rashin wasu sinadarai na bitaman a jiki, akwai na masu yawan shan barasa, ko yawan shan sigari duk sukan iya kawo hakan. Don haka mai wannan matsala sai an masa dan bincike da gwaje-gwajen jini sosai ake gane dalili, kafin a fara magani.