✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban kan lafiya

Ina son karin bayani ne a kan ciwon hanta mai saurin yaduwa na hepatitis Amsa: Ciwon hanta mai saurin yaduwa wasu kwayoyin cuta na birus…

Ina son karin bayani ne a kan ciwon hanta mai saurin yaduwa na hepatitis

Amsa: Ciwon hanta mai saurin yaduwa wasu kwayoyin cuta na birus ne ke jawo shi, saboda shiga cikin hanta ta hanyar jini da suke yi. Akwai nau’insu har kusan kala shida; akwai A, akwai B, akwai C, da D da E da kuma F. Amma an fi ganin nau’uka uku na farko wato A, B, da C. A cikin wadannan ukun ma an fi ganin nau’in ko ajin B, wanda kuma shi ne ya fi yi wa hanta illa. Ya kamata a san banda wadannan rukunin kwayoyin cutuka akwai sauran kwayoyi da ba na birus ba, da sauran abubuwa ma da suke kashe hanta, kamar barasa da burkutu da shan miyagun kwayoyi da shan wasu guba kamar gubar dalma da sauransu.

Nau’in da za mu yi magana a kai su ne wadanda kwayoyin cutar rukunin B da C ke kawowa. Hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa hanyoyin da ake daukar wadannan kwayoyin cuta masu nakasa hanta kusan hanyoyi iri daya ne da ake daukar cutar kanjamau, wato ta hanyoyin saduwa da karin jini da amfani da kayan kaifi da allurai na ‘yan kwaya. A yanzu haka an fi samun mace-mace ma daga cututtukan hepatitis fiye da mace-macen cutar kanjamau saboda ba a samun magungunan ciwon hantar kamar yadda aka samar da na kanjamau, haka nan kuma saboda fadakarwa da ake ta yi a kan ciwon na kanjamau din ana mantawa da na hanta mai yaduwa. 

Domin a yanzu mutane fiye da miliyan 1.5 ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hantar, amma masu kanjamau wajen miliyan 1 ne ke mutuwa a duk shekara. Haka kuma kusan kowa ya san cutar kanjamau, amma da yawan mutane ba su san ciwon kumburin hanta mai yaduwa ba. Shi ya sa da yawa mutane idan za su yi aure sai dai a yi gwajin kanjamau kawai ba a hadawa da na ciwon hanta. Yawanci a wurin gwajin ba da jini kawai akan gano mutum yana dauke da cutar tunda sai ta yi shekara da shekaru mutum bai ma san yana dauke da kwayar cutar ba, domin da fari ba alamu take nunawa ba.

Hanyoyin da ake daukar kwayoyin su ne yayin saduwa daga mai dauke da kwayar zuwa wanda bai dauke da ita, sai kuma ta hanyar karin jinin da ba a yi wa gwajin tantance kwayar cutar ba, sai kuma ta hanyar amfani da kayan kaifin da ba su da tsabta, kamar askar wanzamin da ba a gasa ba, ko almakashin mai yankan farce da ba ya sa wuta, sai amfani da rezar da mai ciwon ya yi amfani da ita, ko amfani da allurar da aka yi wa wani, maimakon a yi amfani da sabuwa. Wata hanyar kuma ta daukar ciwon a jarirai ita ce ta wurin uwa mai dauke da kwayar cutar, yayin haihuwa ko yayin shayarwa.

Da yake kwayoyin cutar shiga cikin hanta suke su yi barcinsu, da yawa masu dauke da kwayoyin ba sa jin wasu alamu tsawon shekaru sai ranar da suka farka suka fara cin hantar sa’annan alamu za su bayyana. Wannan na faruwa ne kawai a kashi daya cikin hudu na wadanda ke dauke da kwayar, sauran kashi ukun ba za su taba nuna wata alama ba duk tsawon rayuwarsu, shi ya sa aka fi cewa masu dauke da kwayar su kwantar da hankalinsu domin zai wahala su nuna alamun. Amma a wannan tsakanin ne masu ciwon ke yada ta musamman ga abokan zama na aure da kuma ’ya’yansu.

Alamun ciwon, idan har sun bayyana, sune yawan zazzabi, yawan ciwon ciki bangaren dama, yawan tashin zuciya da rashin son abinci, yawan samun shawara, wato kadawar ido zuwa ruwan dorawa da rama da sauran alamu da mutum zai ji dai cewa ba lafiya ba. A daidai wannan lokaci ne dole a dauki matakin rage kwayoyin cutar domin kada su nakasar da hantar gaba-daya, wanda babban abin da suke kawowa shi ne motsewar hanta ko ma ciwon daji na hanta. Magunguna da alluran da ake amfani da su a ci karfin kwayoyin cutar kafin su kai ga illa suna da matukar tsada sosai, shi ya sa mukan ce riga-kafi ya fi magani.

Hanyoyin Kariya:

1-Kamewa har sai an yi aure, masu auren ma su rike matansu kawai. 

2-Tabbatar da an yi gwajin cutar ga wadanda suke shirin aure, su je tare kuma a nuna musu sakamakon tare kafin a daura auren.

3-Tabbatarwa cewa jinin da za a kara wa mutum an gwada shi a asibiti an tabbatar ba ya kauke da kwayoyin cuta. 

4-A wurin awon mata masu juna biyu ana auna wannan ciwon. Idan an samu mace mai kwayar cutar ana daukar duk matakan da suka kamata wajen kare abin da take dauke da shi don kada ya samu, don haka a ba wa ma’aikatan lafiya hadin kai. 

5-A yanzu akwai alluran riga-kafin kamuwa daga wadannan kwayoyin cuta na ciwon hanta wadanda aka sa a jadawalin alluran riga-kafi don yi wa yara da zarar an haife su, sa’annan a watanni na biyu da na uku, akasin kwayar kanjamau wadda har yanzu ba a gano allurar riga-kafinta ba. 

6-Ba yara kawai ba, har manya wadanda ke cikin hadarin kamuwa za a iya yi wa allurar riga-kafin. Wadannan sun hada da ma’aikatan lafiya, musamman masu aiki a dakin gwajin jini da tiyata, mata masu zaman kansu, da mutanen da ke aiki cikin damara. A ma’aurata wadanda aka samu daya ke da kwayar cutar amma daya ba shi da shi, shi wanda ba ya dauke da kwayar cutar sai ya samu a yi masa riga-kafi. Ana samun wadannan allurai a asibitoci da cibiyoyin riga-kafi. 

7-A tabbata an tafasa kayan kaifi kamar na wanzamai ko na mai yankan farce ko a kona su da wutar lighter ko a wanke su da sinadarin bleach kafin a yi wa mutum amfani da su. Sai dai idan sabuwa ce daga ledarta aka bare a gaban mutum. Haka ma sirinji da reza, a rika tabbatarwa sababbi fil aka bare kafin amfani da su. 

Ko me ciwon hanta zai iya cin wake? Me ya kamata ya ci, kuma mai ya kamata a ce ba zai ci ba?

Daga Jamila dalhatu


Amsa: Ciwon hantar ai iri-iri ne; akwai irin wanda muka yi bayani a sama, akwai ma ciwon zuciya da kan shafi hanta, akwai ma na barasa. Don haka akwai wadanda za a ce abinci mai gina jiki kamar su wake da nama ne za su daina ko rage ci, akwai kuma wadanda mai kara kuzari za a ce su rage. Don haka likitan da ya gano ciwon hantar, shi ne zai shimfida masa ka’idojin irin abincin da zai ci.


Muna fama da ciwon ciki da tashin zuciya da taruwar miyau a baki da ya kai shekaru 15. Mun je asibitoci da dama an mana hoton scanning amma har yanzu ba wani abu da aka gani. Shine muke neman shawara.

Daga Kabiru Makauraci da Bashir Miko

Amsa: To ai ban da hoton scanning akwai sauran bincike Malamai. In da za ku je asibitin gaske, wato babban asibiti kamar na koyarwa ko FMC bangaren da ke kula da ciki, wato GIT ku bude fayil ku ga likita, sa’annan a samu aljihunku ya jure wa duk abin da za su bukata na gwaje-gwaje, da za a gano muku ko mece ce matsalar.