✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban 04

Shekaruna 60, ina da sha’awar shan madara (ta gwangwani ko garinta), musamman cikin Ramadan ko ranakun da zan yi azumin nafila.  Nakan sha gwangwani daya…

Shekaruna 60, ina da sha’awar shan madara (ta gwangwani ko garinta), musamman cikin Ramadan ko ranakun da zan yi azumin nafila.  Nakan sha gwangwani daya kullum, amma da aka ce min (wai) akwai matsala, sai na koma shan rabi.  Shin akwai matsalar? Duk da yake a shekarun baya, an ce min ina da olsa, kuma a wani binciken gwaji da aka yi, sai aka rubuta ‘stomach erosion.’ Yaya abin yake? Nakan sha kwayar ‘gelusil’ ko ruwan minti.
Daga Mallam Ahmad, Abuja
Amsa: To da kai da masu irin wannan matsala da suka aiko da tambayoyi, da ma wadanda suke da irin wannan matsala amma ba su yi tambaya ba, musamman saboda ganin cikin watan azumin ake, ya kamata mu san cewa akwai masu matsaloli iri daban-daban na gyambon, ciki wadanda idan suka yi azumi galabaita suke sosai, akwai kuma wadanda ba sa galabaita. To kowa dai shi ya san irin yadda yake ji idan yana azumin. Abin da dai aka sani a likitance shi ne, akwai da dama masu irin wannan matsaloli da ba sa iya azumi kuma ba ma sa iya ramawa, sai dai kawai su tambayi malamai makusanta ko sa iya ciyarwa.
Dalilin da ya sa wasu matsalar ta su ta fi ta wasu shi ne cewa akwai wasu mutane ’yan kalilan da bangon cikinsu ba ya da kwari sosai, don haka sinadarin acid na ciki ko abinci mai tsami ko mai gas ko mai yaji, ko wasu kwayoyi magunguna samfurin aspirin kan iya kwarzane shi bangon cikin nasu su samu wani dan miki. Dangane da tsananin matsalar idan aka haska da kyamara a yayin gwajin endoscopy akan bambance mai saukin cikinsu wanda shi ne erosion ko gastritis da mai tsanani, wanda shi ne ulcer. Wadanda bangon cikinsu ke da kwari, ba su cika samun irin wannan matsala ba. An yi amannar kuma akwai wata kwayar cuta wai ita H.pylori da kan mamaye bangon cikin, wadda ita ma takan taimaka wajen rage kwarin bangon cikin. Don haka a wurin gwaji idan aka auna aka ga wannan kwayar cuta, har da magungunan kasha ta ake ba mutum.
Ko ba lokacin azumi ba yawanci masu irin wannan matsala sukan bukaci wani dan abu tsakanin abincin dare zuwa na safe, musamman tun da wannan lokacin ne ya fi tsayi a tsakanin cimakarmu, wanda a wannan lokaci acid din ke kartar cikin. To yawanci sai a ce su sha madara ko gelusil ko ruwan minti saboda ya dan sirka acid din su ji dan dama-dama. Shi ya sa masu matsalar suke son madara da gelusil din sosai don idan aka sha ana dan jin dama-dama a cikin.
To kai dai idan ka ci gaba da sha din ba komai. Abin da ya sa aka ce ka rage yawan shan madara watakila saboda tana da maiko, kuma ga shi an manyanta, don haka ko dai ka sha rabi din ko kuma ka nemi maras maiko sosai da ake kira low-fat milk, ka rika adanawa a firinji.
Na ga bayaninka a kan ranar sikila ta duniya. Ina so ka ba ni shawara. Akwai matar da zan aura amma ita ‘AS’ ce domin ta taba aure ta haifi ’ya’ya biyu duk masu ciwon sikila. To ni kuma ga shi genotype dina ‘AA’ ne. Kana ganin za mu iya haifar ’ya’ya masu sikila?
Daga Shehu Garba
Amsa: A’a, idan ka aure ta ba za a samu sikila ba da yardar Allah, tun da kai ‘AA’ ne, sai dai a samu masu rabin ciwon irinta wato ‘AS.’ To su ‘AS’ din fa amma nan gaba suna iya aurar wani ‘AS’ din a samu sikila wato ‘SS’ a jikoki. Sai dai idan kun tabbata ’ya’yan ma wadanda suka kasance ‘AS’ za ku ilmantar da su a kan wannan matsala don kada su auri ‘AS.’ Da fatan ka fahimta, domin abin yana da ’yar sarkakiya. Watakil sai gaba da gaba za a iya yi wa mutum bayani gamsasshe.
Wato abin da ya sa ita wadancan ’ya’yanta biyu suka zama sikila shi ne, watakil ‘AS’ ne mijinta na fari ko ma ‘SS.’
Sa’annan kuma ya kamata ka san ana iya samun dan laulayi irin na masu sikila a masu rabin ciwon, wato su ‘AS’ din ke nan amma sai dai ba ya kaiwa tsananin na sikila.
Game da illolin shan kwayoyi: Ina tambaya ne a kan magungunan sa kiba irinsu dedamethasone da Kristen. Shin akwai illa ne ko babu? Kuma wanne ya fi illa? Idan akwai illa to wane abinci mutum zai ci ya yi kiba?
Daga Yahya, Kano
Amsa: Ina jin Malam Yahaya bako ne a shafin namu, domin an amsa irin wannan tambaya fiye da sau biyu a wannan shafi: Cewa kwayoyin kara kiba illolinsu su ne lalata wata ’yar halitta a saman koda mai suna adrenal gland, domin ita ke samar mana da su sinadaran cikin kwayoyin a kullum. To idan suka ga kuma ana bayar da su ta hanyar allura su kuma sai su daina sarrafa nasu, wanda kan iya sa su su ma daina aiki gaba daya. A hankali a hankali kuma hakan sai ya jawo babbar matsalar da sai an yi da gaske kafin a ceto ran mutum.
Haka nan kuma ba a ce maka ga abinci mai sa kiba ba, sai dai a ce maka ga ire-iren abincin da idan mutum yana ci jikinsa zai ginu ba za a ce masa ba lafiyayye ba. Su ma an sha fadar su kuma su ne abincin da suka fi tsada a kasuwa, irinsu nama, hanta, kwai, kaji, madara da sauransu. Akwai masu sauki irin su wake, gyada, waken soya, wadanda akan iya sarrafa su a yi maka abinci daban-dabam kamar alele, kunun gyada da awara da sauransu.
Shin akwai matsayin da basir ke kaiwa ne yadda dole sai an yi masa tiyata? Yaya mutum zai gane cewa basir ya kai matsayin?
Daga Malam, Abuja
Amsa: kwarai kuwa, duk wani basir mai tsuro wanda ya ki jin magani ko ruwan gishiri da ake masa to lallai sai an dangana ga likitan fida ya duba ya gani ko dole sai an yi ’yar tiyata. Don haka idan basir ya yi tsuro yadda idan ka zo tsarki kana jin sa kamar wani kumburi babba, to alama ce ta cewa a dangana ga likitan fida.