Wai me ya sa ne da na yi wanka kaikayi mai tsanani yake rufe ni? Me ke jawo hakan ne, kuma mene ne abin yi?
Amsa; To a likitance yadda muke bullowa abubuwa irin wadannan da ba su da amsa kai tsaye, shi ne, idan matsala irin taka ta faru sai a tsaya a duba a ce to, daidai lokacin da matsalar ta fara, me da mene ne suka auku a lokacin, canjin yanayi ne ko canjin wurin zama, ko na abinci, ko me. Sa’annan a duba shi wankan da me da me ake yinsa? Ka ga dai na daya akwai ruwa, akwai sabulu, akwai soso a mafi yawan lokuta, akwai kuma roba ko bokiti da sauransu. Sai ka tsaya ka duba, ka ce to ko shin ruwan nan ne ke ba ni matsala? Sai ka tambayi duk mutanen gidanku masu wanka da ruwan, akwai mai samun kaikayi idan ya yi wanka da ruwan gidan nan? Idan akwai to kusan ka samu shaida, idan babu, sai ka canza idan da na sanyi kake, ka koma mai dan dimi, idan da na zafi sosai ma kake ka rika kara sirkawa.
Idan ka yi haka bai tafi ba sai ka binciki sabulu, ka duba ka ga ko sabulun ne. Yadda ake yi shi ne sai ka canza zuwa wani nau’in sabulu ka gani ko wani sabo zai sa ka daina jin kaikayi. Idan hakan ma bai biya bukata ba, sai ka dubi soso. To shin soson nan nawa tauri ne da shi ko laushi, kuma me fatata ta fi bukata? Wato shi ma dai ka canza ka gani daidai bukatar fatarka. Idan duk hakan ba su wadatar ba sai ka koma ka canza abin wankan, wato bokiti ko roba ko daga nan ne matsalar, domin idan suka dade suna tara datti da maiko da kwayoyin cuta, wanda za ka gani a bangon abin wankan. Sai kuma ka duba, ko mai ne ba ka shafawa idan ka yi wankan, alhali fatarka na bukata.
Idan an dace shi ke nan, idan kuma ba a dace ba, sai ka ce to ko matsalar a karan-kanka ne, wato ko kana da matsalar borin jini idan ka yi wanka lokaci kaza, da ruwa kaza. To idan haka ne ke nan sai ka ga likitan fata ya ji bayaninka ya tantance ko akwai borin jinin ko babu, ko ma wata matsalar ce ta daban, musamman ma idan kana ganin kananan kuraje lokacin kaikayin. Kafin ka ga likitan, kwayoyin hadiya kanana na kaikayin jiki za su iya taimaka maka wajen rage kaikayin, kuma za ka iya samun su a kyamis ko da ba a rubuta maka ba, domin wasunsu ma na magance mura ne.
Likita shin akwai wata illa ko rashinta yin wanka da ruwan burtsatse ga mace ko namiji? Don wasu suna cewa wai yana sa kyasfi.
Daga Ibrahim Kabara.
Amsa: Tun da ruwan burtsatse ya fi na famfo yawan sinadarai masu karfi irinsu gishirin calcium, iodine, magnesium, potassium da sauransu, wanda shi ya sa yake da zartsi a baki, hukumomin lafiya da ma Hukumar Lafiya ta Duniya ba su ba da wani kashedi ga mutane akan kada a sha ko a yi amfani da irin wannan ruwa ba. A wasu yara dai, ko ma manyan mutane, tabbas bincike ya nuna akwai alakar fitowar kyasfi da yawan wanka da wannan ruwa. A irin wadannan, idan an ga haka sai a canza musu da ruwa marar zartsi, wanda zai sa kyasfin ya tafi.
Ni kuma idan na sha abu mai zaki sai na rika jin kaikayi a jikina, ko me ya sa?
Daga Aminu M.
Amsa: E, kai tunda ka ce sai ka ci abu mai zaki, to watakila a cikin sugan ne, domin akwai nau’in sugan da ke sa borin jiki da kaikayin fata. Nau’o’in suga suna da yawa; ban da wanda muka sani na yau da kullum, wato glucose, akwai wasu wadanda ake samu a kayan marmari, irinsu fructose, galactose, da sucrose da maltose ko na madara lactose da sauransu, da ma wasu a irin abinci ko lemon gwangwani da akan kara a kamfani, irinsu saccharine wato sukarin da kera su ake yi, da sauran ire-irensu.
A cikin wadannan da aka zayyana, wasu za su iya samun borin jini idan suka sha daya daga cikinsu amma ba duka ba. Don haka dole ke nan ka lura ka gani a kowane kayan zaki ne kake samun kaikayin ko kuma a wasu daidaiku. Wato ka lura ka gani shin sai ka sha mangwaro ne kake samun kaikayin ko sai ka sha rake, ko ko a’a sai idan ka ci dabino ko ka sha lemon kwalba, ko ko a’a har ma idan na sha koko ko shayi. Idan ka gano haka ka ga shi ke nan, tun da kowannensu kusan sugansa daban ne. Idan kuma ka kasa ganowa, ke nan sai dai ka hakura da abu masu suga, ko ka je ka ga likita ido-da-ido wanda zai kara bincikar batun.
Ni kuma fatata ce ke ta cinyewa. Na je asibiti an ba ni magani amma ba ta daina ba. Mece ce shawararka?
Daga Musa Ali.
Amsa: Shawarata ita ce, ka nemi asibitin fata, wato inda kwararrun masana lafiyar fata suke ka je su duba fatar a kuma yi bincike-bincike na jini da na fatar duka. In an dace za a gano matsalar da maganinta.
Mene ne ya sa fitsari ke da zarni?
Daga Magaji Abu.
Amsa: Duk da cewa za ka ga fitsari a ido kamar ruwa, abubuwan da kowannensu ya kunsa daban. Mun fadi sinadaran gishiri da ke cikin ruwa irinsu calcium da sauransu, amma fitsari shi ruwa ne mai dauke da guba iri-iri hade da wasu sinadaran irin na cikin ruwa. To wannan kwayoyin guba, wadda babba a cikinsu ita ce ta ammonia, ita ce ke sa fitsari zarni, kuma yana da illa ga fata.
Ina da matsalar olsa amma duk maganin da zan sha ba zan ji sauki ba sai dai allurar pentazocine. Ko yawan amfani da wannan zai iya jawon mini matsala?
Daga Umma I.
Amsa: E, kwarai kuwa yawan amfani da allurar da kika ambata ba zai haifa miki da mai ido ba, tunda takan jawo wa kwakwalwa matsala, ta dawwama a kan idan fa ba ita allurar aka yi miki ba, har abada ba ki da sukuni sai an yi miki, wato dai ki zama ’yar kwaya ke nan, Allah Ya kiyaye. Mun sha fadar yadda za a shawo matsalar olsa a nan, wadda muka ce akwai magunguna masu karfi da za a iya rubuta miki a asibiti, wadanda sai kin sha na tsawon makonni ko ma watanni kafin ta warke. Su kuma masu rubutawar watakila ba za su rubuta ba har sai an dauko hoton olsar da kyamara a ciki sun tabbatar olsar ce.
Amsoshin tambayoyi da suka shafi kaikayin jiki
Wai me ya sa ne da na yi wanka kaikayi mai tsanani yake rufe ni? Me ke jawo hakan ne, kuma mene ne abin yi?Amsa;…
