✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi

Ina so a mini bayani a kan cutukan da ke sa yara jijjiga (conbulsion) ko tafiyar ruwa, da yadda za a kiyaye aukuwarsu ko riga-kafi.…

Ina so a mini bayani a kan cutukan da ke sa yara jijjiga (conbulsion) ko tafiyar ruwa, da yadda za a kiyaye aukuwarsu ko riga-kafi.

Daga Umar Sarkin Yaki, Kano

 

Amsa: Akwai cutuka da dama masu sa yara ‘yan kasa da shekaru biyar jijjiga, wadanda idan ba a lura sosai ba ma sai a dauka ko ciwon farfadiya ne da yaro. Don haka ya kamata a san bambanci. Shi ciwon farfadiya a kwakwalwa ya ke, shi kuma ciwon da zai sa jijjiga mai kama da farfadiya ba dole sai a kwakwalwa matsalar kan faru ba. Yawanci shi zafin zazzabi ne ke sa kwakwalwar ta dan rikice a samu jijjiga. A wasu lokuta ma kafin mahaifiya ta san yaro ba lafiya zazzabi ya rufe shi ya fara jijjiga. Wadannan cutuka da kan sa irin wannan jijjiga sun hada da

1. Zazzabin cizon sauro.

2. Zazzabin sankarau.

3. Zazzabin ciwon hakarkari wato tarin numoniya.

4. Zazzabin ciwon kunne.

5. Zazzabin ciwon mafitsara. 

 

Don haka da an ga yaro ya fara irin wannan jijjiga kuma jikinsa na zafi sosai, kada a tsorata, sai a kwantar da shi a rike shi har ya gama, tunda da wuya irin wannan jijjiga ta yi wa kwakwalwa illa, sai a yi sauri a samu zani ko tawul a dan jika shi da ruwa a matse a zo a shafawa yaro a jiki har jikin ya yi sanyi. Idan ma akwai maganin zazzabi kamar paracetamol za a iya ba yaro, duka dai don zazzabin ya sauka kada ya sake wata jijjiga. Daga nan sai fa asibiti inda za a duba a ga ko dayan wadancan cutuka da aka zayyana a sama ne, sa’annan a ba da magani.

 

Hanyoyin kariya daga samun irin wadannan matsaloli ga yara ba su wuce cewa a rika tabbatarwa an musu cikakkun alluran riga-kafi ba, da kuma tabbatar da tsabtar abinci da abin sha da muhalli a gida da kwana cikin gidan sauro. Wadannan idan aka yi to ko ma mene ne zai zo da sauki da yardar Allah.

 

Shin alluran da ake wa jariri bayan kwana 40 ba ta dauke da sinadarin maganin rana ne da yawan kuka?

Daga Musa Kurna

 

Amsa: Babu wata allurar jarirai mai maganin rana mu a likitance. Alluran da a ke wa jariri bayan kwana 40 sun kai uku, daya daga cikinsu ma (pentabalent) cutuka biyar take karewa; tsinkau-tsinkau, tarin jaki, sarke hakora, ciwon hanta da murar influenza sauran sune na shan inna da ta kariya daga ciwon numonia da ta gudawa. To ka ji. A ciki dai ban san wacce ce ke kare rana ko yawan kuka ba.