✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi

Wane irin abinci mace mai juna biyu ya kamata ta rika ci domin samun saukin nakuda da haihuwa? Daga Surajo Mada, Zamfara   Amsa: A…

Wane irin abinci mace mai juna biyu ya kamata ta rika ci domin samun saukin nakuda da haihuwa?

Daga Surajo Mada, Zamfara

 

Amsa: A likitance ba wani abinci na musamman da mace mai juna biyu da ta karato lokacinta za ta ci ya mata maganin ciwon nakuda, amma akwai dabarun motsa jiki kala-kala da bincike ya tabbatar za su iya saukaka nakuda da haihuwa. Kun san mun ce a watannin farko na ciki ba a son mace ta rika yawan aiki to amma a watannin karshe na ciki kamar daga watan bakwai ana so ta kara zirga-zirga da motsa jiki iri-iri amma ba masu wahala sosai ba, irinsu tafiyar kafa, tuka keken tsaye da ire-irensu. Wadannan ne binciken kimiya ya tabbatar cikin sauki mai yinsa za ta haife. 

 

Da gaske ne magungunan da sukan dawo wa da mace al’adarta akwai kuma wanda zai iya hana ta daukan ciki?

Daga Musa L.

 

Amsa: A’a Mallam Musa, ai dama rikicin al’ada ke hana daukar ciki. Maganin da zai daidaita al’ada ta dawo yadda ya kamata ai sai dai ya sa a dauki juna biyu ba ya hana ba. Duk maganin da ya kasa dawo da al’ada yadda ta ke to kuwa ba zai iya sa a dauki ciki ba.

 

A likitance akwai abinda ake yi wa yara masu fitina sosai ne domin rageta? Domin muna da wani dan shekaru 9 amma fitinarsa ta yi yawa sosai. A ba mu shawara.

Daga Abban Abdussalam, Kano

 

Amsa: E, a likitance idan yaro ya fiye fitina sosai likitan kwakwalwa muke hada shi da shi, domin ya duba shi ya karanci halayensa ya ga daidai ne ko kuwa akwai matsala. Idan akwai matsala shi ya kan ba da shawarar abinda ya dace a yi. Don haka kenan sai kun nemi babban asibiti kun je bangaren likitocin kwakwalwa kun yi rajistar ganin daya daga cikin likitocinsu da yaron

 

Wai me ke kawo kan jariri ya fada daga wurin goshinsa?

Daga Nura B.G., Kano

 

Amsa: Idan na fahimceka kana nufin madigar jaririn nan ta gaba. To bari in kara jaddada maka cewa duk wanda ya ga madigar jaririnsa ta loba to kada ya yi sake ya zauna a gida, alama ce ta cewa jaririn ba shi da lafiya. Likitocin yara na iya gane alamun ciwo daga madigar jariri. Akwai cutuka da dama tun daga gudawa da rashin isasshen ruwa a jiki, da sankarau da tamowa da ire-irensu da kan sa jariri madigarsa ta loba. Wato kenan madigar jaririn da yake lafiya kalau yake bai kamata ta loba ko ta fada ba. Da fatan ka fahimta.