Mace mai ciwon koda za ta iya samun juna biyu kuma ta haihu kuwa? An yi mata hoton ciki ne an ga kodarta ta kumbura
Amsa: Ya danganta da irin ciwon kodar da kuma tsananinsa, don ka san akwai cututtukan koda iri-iri. A lokuta da dama koda za ta iya samun ciwo amma ta farfado ba tare da an ga alamu ba, amma ya nuna a hoto, akwai ma kumburi na ciwon koda wanda ba ya da wata illa, kamar ciwon kumburin koda na wadanda aka haifa da shi, wato ciwon polycystic kidney disease. Akwai wadansu ma da misali tsakuwa ce za ta sa wa kodar kumburi amma da ta fita wurin ya sabe ya warke shi ke nan. Sa’annan wani batu mai dan kwantar da hankali game da koda shi ne aikin da koda biyu suke yi, guda daya ma za ta iya yi ba tare da wata matsala ba. Don haka ke nan idan hoto ya nuna koda daya na da matsala, ba lallai ba ne a ce dayar ma na da matsala. Shi ya sa ma ake ganin wadanda aka ciri daya daga cikin kodarsu aka dasa wa wani sukan yi rayuwarsu kamar kowa.
Yawanci ciwon koda ana kasa shi kashi uku dangane da tsananinsa; akwai mai tsanani sosai, akwai matsakaici akwai marar tsanani. Masana ciwon koda sun tabbatar cewa idan ciwon marar tsanani ne to ba matsala mace za ta iya daukar ciki ta kuma haihu lafiya, idan matsakaici ne kuma za ta iya daukar ciki amma za ta iya samun matsala tsawon lokacin cikin, idan kuma matsananci ne da wuya ma ta iya daukar cikin, saboda babu kwayayen da za ta iya saki isassu. Koda a ce za ta iya dauka ma, ba a so matar ta samu cikin kwata-kwata domin zai iya tagayyara rayuwarta da ta abin da ke cikin. Amma idan ta riga ta samu cikin sa’annan daga baya aka gano akwai ciwon koda, kuma mai tsananin ne, to watakila idan aka fara magani kamar na wankin koda za ta iya haifewa lafiya. An ce watakila saboda za a iya samun cewa magungunan ciwon ma ba za su yi wa abin da ke ciki dadi ba. A irin wannan yanayi magungunan za su iya sa bari. Ba dai a so mai ciki ta kasance ana mata wankin koda sai ya zama dole.
To ka ji. Abin da ya fi yanzu shi ne likitan da ya yi hoton ya tura ku wurin likitan koda wanda zai duba ta ya duba hoton, ya gano sababin kumburin a gani ko marar tsanani ne.