Mace mai ciwon sanyi idan ta samu juna biyu wane irin magani ya kamata ta yi amfani da shi ko allurai?
Daga Sadik S.B da Sakibu, Kano
Amsa: A’a ai ciwon sanyi ma da wuya ya bar mace ta samu juna biyu. In dai aka ga wani abu mai kama da ciwon sanyi a mace mai juna biyu ba ciwon sanyi ba ne, a je likita ta tantance ko mene ne ta ba da magani
Yarinya ce idan ta yi fitsari sai ya rika zarni har yana hawa kai. Hakan matsala ce?
Daga Bilki Rabson
Amsa: A’a to so kike ya yi kanshi? Ai da ma haka ake son fitsari ya yi zarni. Ke in takaice miki ma a likitance fitsari mai kanshi shi ne ciwo, domin muna da cututtukan yara bila adadin wadanda daga kanshin fitsarinsu kawai za mu iya gano irin ciwon.
Idan mai dakina tana shayar da yarinyata sai ka ga madarar na fitowa yarinyar ta hanci. Me ke kawo haka?
Daga Dantanin Yalwa
Amsa: Alamar ba ta iya shayarwar ba ke nan, wato ba ta iya sa jariri a kan nono ba yadda ya kamata. Fitowar nono ta hanci yana nufin makoshin yarinyar ba a bude yake ba sosai, an makare shi. Akwai bukatar ku tafi asibitin sha-ka-tafi na kusa da ku domin ungozoma su koya mata yadda ake sa jariri a kan nono.
Ciwon mara ne da fitsarin jini ke damuna. Na sha magunguna wasunsu ma kara mini ciwon suke. Shi ne nake neman shawara
Daga H. Bala
Amsa: Shawara a dauki fitsarin a auna, a kuma yi hoton marar a ga ko mene ne a ciki. Za a iya samun haka a babban asibiti idan an je an daure an ga likita kwararre, kamar a babban asibitin mafitsara, idan kuma ke mace ce a asibitin mata wato gynae.
Sai tambayar Abba Ocal wadda amsar ita ce cewa eh, akwai matsala sai kun samu likita kun je an tattauna batun.