Da Suka Shafi Juna Biyu II
A wane wata ne ake iya gano jinsin jariri a cikin da mai juna biyu ke dauke da shi? Daga wane wata ne ake so a ce kan jariri ya juya ya yi saiti domin haihuwa, a wane wata ne kuma idan bai juya ba akwai matsala?
Amsa: Masana lafiyar mata sun yi amanna daga wata na hudu ne idan aka yi hoto za a iya ganowa ko me mace ke dauke da shi, wato a wannan wata ne za a iya tantance jinsi. Duk wasu hotuna da aka yi kafin wata hudu na kayyade kwanakin watan ne lafiyar cikin baki daya. Ko ya nuna jinsin jariri ma kafin watanni hudu za a iya samun kuskure.
Shi kuma juyawar jariri da saitinsa domin haihuwa ya kamata a ce a daga karshen watan bakwai zuwa na takwas ne jariri ya daidaitu da mahaifa domin shirin fitowa duniya. Zuwa wata na tara idan jariri bai juya ba shi ne ake ganin akwai matsala. Akan samu kwatan jarirai, wato daya bisa hudu ko dai ba su juya yadda ya kamata ba, wato suna kaikaice, ko kuma sun juya a baibai, wato kansu a sama. A irin wadannan idan mace na zuwa awo a lokutan da aka zayyana mata akan iya ganowa da wuri a juyasu. Wasu kuma ba sa juyuwa sai dai a ce wa matar ga irin dabarar da za a yi a ciro jaririn ranar haihuwar. Misali jariri masu kwanciya a kaikaice kai-tsaye tiyatar c/s ce, masu baibai kuma watakila a iya sa karafuna a zarosu.
Yarinya ce ‘yar watanni biyar take kyanda sai na kaita kyamis suka ba ta wasu magunguna har da ruwan gishiri da sukari. Na iya bata tunda ba ta kai wata 6 ba, ba mu ba ta komai sai ta kai
Daga Musa GGC Kano
Amsa: Haba Mallam Musa kada ka ba da Kanawa mana. A ce yarinya na kyanda ka kaita kyamis? Abin da mamaki. kyanda babban ciwo ne a yara da ke bukatar zuwa asibiti. Ai ko muma idan ka ji mun ce a je kyamis abinda za a saya bai wuce panadal da multibite ba.