✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi

Da Suka Shafi Juna Biyu II   Na samu juna biyu amma a wata na bakwai na samu jijjiga aka mini tiyata aka ciro jaririn…

Da Suka Shafi Juna Biyu II

 

Na samu juna biyu amma a wata na bakwai na samu jijjiga aka mini tiyata aka ciro jaririn ba rai. To idan na samu wani juna biyun zan iya haihuwa da kaina?

Daga Amina M.

Amsa: A’a kada ki kuma sake kuskuren da kika yi a cikin farin mana. Ai da alama ba ki zuwa awo a wancan cikin shi ya sa har ciwon jijjiga ya rinjayeki kika rasa da. Zai wahala mace mai juna biyu mai zuwa awo yadda aka zayyana mata da shan magungunan da aka bata ta samu jijjiga, tunda mu ma’aikatan lafiya mukan yi hasashen matsalar tun da wuri mu tunkareta mu kiyaye aukuwarta idan ana zuwa awo. 

To a yanzu ma idan kika samu wani juna biyu kika koma musu wancan asibitin da aka miki tiyata da wuya su barki ki haihu da kanki, tunda an taba miki tiyata a cikin farko. Don haka kada ma ki fara sawa a ranki za ki haihu da kanki, ko a gida, sai abinda likitocin suka ce miki.

 

Magungunan da akan sha lokacin juna biyu na bitamin da karin jini yaushe ya kamata mace ta fara sha, a yaushe kuma ya kamata ta tsaya?

Daga Maman ‘Yanbiyu

 

Amsa: Wasu mata masu juna biyu da dama sukan fara shan wadannan magunguna bayan sun je asibiti awon farko an basu, su kuma ajiye sha da zarar sun haife. Amma a likitance ba haka ya kamata ba. Kamata ya yi duk mai mace mai niyyar daukar ciki ta fara shan irin wadannan magunguna (idan tana zuwa asibiti kamar wurin likitan iyali, ko ta samu a kyamis) a kalla wata daya kafin batan wata. Ba za ta ajiyesu ba kuma sai an yi yaye, wato sai an daina shayarwa, musamman ma a irinku masu shayar da ‘yan biyu, sai dai idan wani likita ya hango wani abu ya tsayar da su da wuri.

 

Ko yawan wankin ciki ga mace mai bari zai iya jawo matsala ga lafiyarta?

Daga Sani dorayi

 

Amsa: kwarai kuwa, yawan wankin ciki bayan bari zai iya jawo lalacewar mahaifa saboda yawan kartar bangon mahaifar zai iya lalata ta gaba daya ta kasa rike ciki. Sai dai a yanzu maimakon a karce bangon mahaifa an fi yin na sirinji mai zuko duk abinda aka bari bayan an yi barin. Wannan ya dan fi akan na kartar mahaifar

 

Nima matata tana da juna biyu kuma tana yawan yin habo. Ko akwai wata shawara?

Daga B. Tela

 

Amsa: Shawara ita ce ka kaita awo idan har ba ta fara ba, inda za a duba a ga mene ne dalilin habon. Ko ta fara awon ma can din dai za ku koma ku fada musu.