Shin ciwon tarin numoniya gadonsa jarirai ke yi ko kuwa? Ta yaya ake gane alamominsa?
Daga Aminu Adamu Malam-madori
Amsa: A’a ciwon numoniya ba gadonsa jarirai ke yi ba, hasali ma ba a ciki suke dauka ba, sai sun zon duniya suke dauka idan suka shaki iska. Akwai dai wani ciwon wahalar numfashi mai kama da numoniya a jarirai wadanda suka sha wahala kafin su fito duniya. Shima ciwon yana kama da numoniya amma ba numoniya bane. A duka matsalolin biyu akwai nmfashi sama-sama, hade da zazzabi, amma ba a cika jin tari ba, ba kamar numoniya ta manyan yara ko manyan mutane ba. Kenan duk wani jariri da aka haifa a gida aka ga irin wadannan alamu tabbas yana bukatar taimakon likitoci cikin gaggawa.
Yaro ne ke yawan fama da mura muka kai shi asibiti aka ce huhunsa ne ya tabu. Shine muke neman shawara
Daga Maman Khalil
Amsa: A’a ai kin san a irin wannan tunda an je asibiti likita ya gani, zai fi kyau likitan ya ba da shawara. A daina tasowa kawai idan akwai tambayoyi da ya kamata a wa likita a zauna a masa, misali mene ne ya tabu a huhun, yana warkewa, me ya kamata mu yi, ko ina za a tura mu. Haka dai tambayoyi har sai ya ba da cikakkiyar amsa wadda za ta samar da mafita.
Ya za a yi wa matar da ba ta son amfani da dabarar tsarin iyali?
Daga Ibrahim Umar, Sokoto
Amsa: A’a ai mun taba fada a nan cewa ba a yi wa mutum dole a bangaren dabarun tsara iyali, ba magani bane na ceton rai da za a ce idan ba a mata ba rai zai halinsa, don haka ba a dole, ba kuma a yi a asirce, domin idan ta gano ta kai kara za a iya bi mata hakkinta. Dabarun tsara iyali kenan miji ba zai wa matarsa dole ba, haka ma ita ma ba za ta yi masa dole ba. Dole sai su duka biyun sun amince ta hanyar fatar baki ko ta takarda.
Akwai wani mai ne da muke shafawa mai suna Cocoa bota shine muke tambaya ko shima yana illa ga jiki, domin mun ga kamar yana sa mu sheki.
Daga Hadin Gwiwar ‘Yammata
Amsa: A’a cocoa bota ba ya cikin jerin irin mayukan da akan yi amfani da su wajen bleaching, sai dai idan jabu ne, domin gangariyarsa babu sinadarai masu kawo matsala. Abin dubawa dai kamar yadda muka sha fada shine a duba sinadarai irinsu mercury, hydrokuinone, clobetasol bethamethasone da lead. Sauran yawanci za a ga sunayensu na karewa da -ol ko -one. Idan akwai ko da daya ne daga cikin wadannan a gujesu, ba a mai ba ma har a sabulan wanka. A yi kwalliya lafiya.