Shin ko ba wa jariri lemo daga sati guda bayan haihuwa yana da illa?
Amsa: Ba daidai ba ne a ba wa jariri dan kasa da watanni biyar ko wane irin lemo, ko da na bawo, ballantana na kwalba, saboda cikinsa bai yi kwarin da zai zuke amfanin ba. Idan ana so yaro ya moru da wani abinci kamar lemon bawo, sai mai shayar da shi ta sha da yawa, ta yadda zai shiga ruwan nono jariri ya sha ya samu amfaninsa. Da fatan za a kiyaye, don kada a zo kuma ayi ta tambaya me ya jawowa jariri zawo, alhali mu mukan jawo mu su ba tare da mun sani ba.
Ni kuma haihuwa na yi watanni biyu baya, nake son hutun haihuwa. Ina so a sa mini irin na hannu. Shin ba shi da matsala?
Daga Maman Sadik.
Amsa: Ai mun sha cewa jiki-jiki ne, ba tabbas cewa ba zai ba ki matsala, domin sai ki ga wata ‘yar uwarki an sa mata ba matsala amma idan aka sa miki ya zama matsala. Shi ya sa mukan ce sai an gwada akan san na kwarai. Amma tunda ba allura bace, ‘implant’ ne, idan ya fara ba da matsala ma za a iya cireshi cikin sauki. A inda za su miki za a miki ‘yan tambayoyi watakila ma da gwaje-gwaje domin a tabbatar ko ya dace da ke.
Ina da yaro ko ana sanyi shi yana yawan zufa. Ko alamar wani ciwo ne haka?
Daga Baban Sadik, Keffi
Amsa: Ba za a sani ba kai tsaye in dai ba kai shi asibiti ka yi aka dubashi ba, watakila ma idan sun ga alamun matsala ce har da aune-aune da gwaje-gwaje za su masa. Domin yawan zufa zai iya zama na lafiya, (musamman idan ba shi da wasu sauran alamun rashin lafiya a tare da shi) zai iya kuma zama na ciwo, don haka sai ka kai shi an duba an tantance.
Ina da mata da take yawan zubar da jini a kullum, sai dai ba da yawa ba. Da na dauketa muka je asibiti shine aka yi aune-aune aka ce tana da juna biyu, suka kuma ce zubar jinin za ta daina. Amma dai har yanzu ba ta daina ba, shine muke neman shawara.
Daga Khalid Ahmed
Amsa: To shawara ita ce ku bude katin awo a wurin ku ce a nan za ta rika awo. Idan kuka yi musu haka duk wasu sauran aune-aune da wata kula da ta dace za su muku, idan ma ba su da shi za su turaku inda ya dace.