✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi

Matata ce ta haihu sati hudu da suka wuce amma ba mu je allura ba saboda wasu dalilai. To yanzu ina so a kai jaririn,…

Matata ce ta haihu sati hudu da suka wuce amma ba mu je allura ba saboda wasu dalilai. To yanzu ina so a kai jaririn, ya za mu yi?

Daga Musa Isa, Kaduna

 

Amsa: E, kawai tafiya za kai cibiyar allurar riga-kafin ko asibitin da aka haife shi, ko  ma dai wani mafi kusa inda ka san ana alluran riga-kafi, ka musu bayani. Zasu ba jaririn sabon katin alluran riga-kafi a fara masa a wannan lokaci duk a masa wadanda bai karba ba. Za kuma su ba da ranaku ko makonnin komawa don a masa na daidai da watanninsa na yanzu, sai a tambaya domin kada a sake jinkiri a gaba.

Ba kai kadai ba, duk wanda jaririnsa ya tsallake allurar riga-kafi, da an tuna sai a je a yi bayani, domin akwai jadawali na wadanda suka tsallake watannin alluransu, wanda dole sai an musu in dai ba su wuce shekaru biyar ba.

 

Mene ne amfanin naman rago da sa a jikin yara?

Daga Mallam Fasih

 

Amsa: Aaaa, amfani kai! Ai bayan alluran riga-kafi babban muhimmin abu ga lafiyar yara wadanda suka fara tauna abinci shi ne abinci mai gina jiki na protein, wanda nama ko na wace dabba ne shi ne kan gaba. Kai ne ma babba za a iya cewa ka yi kaffa-kaffa da nama ba yara ba tunda watakila kai jikinka ya riga ya ginu. Don haka ya kamata ka karawa yaranka sanwa nama, domin kai kanka za ka ga canji a jikinsu da lafiyarsu.

 

Me ke sa yara tsotsar hannu ne matsala ce ko kuwa? Kuma ana gadonta?

Daga Haruna Muhammad, Katsina

 

Amsa: A’a ba matsala ba ce tsotsar hannu a yara da za a damu da ita, domin ba ciwo ba ne, ba a kuma gado. dabi’a ce kawai ba wani abu ba, misali kamar gyaran murya a manya ai ka ga ba ciwo ba ne dabi’a ce kawai har wasu ma sukan yawan yi fiye da wasu, ko da kuwa ba wani abu a makoshinsu.

Abinda ya sa aka ce ba matsala ba ce shi ne, yawancin yara masu tsotsar hannun za ka ga da sun fara wayo suke dainawa. kalilan ne kadai kan ci gaba har wayonsu.

 

Ko za a mini bayani akan ciwon da ake dauka a bayan gida? Wato toilet infection?

Daga Saliha A.

 

Amsa: Wannan kalma ta toilet infection ba likitanci ba ce, kawai dai kalma ce da ake amfani da ita ake boyewa idan mace ta samu ciwon sanyi. A likitance mu ba mu da wani ciwo toilet infection, don haka kada ki damu da shi. In dai kika shiga bayan gida kika kula da tsabtar tsarki da wanke hannaye ba wani abu da ake tsoron zai biyo baya. A matsayinki na mace ciwon da za ki ji tsoronsa shi ne wanda wani namiji zai iya sa miki, wato ciwon sanyi, domin kusan shi ne zai galabaitar da ke har mace ta kasa haihuwa ma a mafi yawancin lokuta.