✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonninku ta tes da Imel (4)

Assalaamu alaikum Baban Sadik, don Allah ina son ka turo mini da kasidar “Tsibirin Bamuda” ta wannan adireshin:  [email protected].  Allah taimakeka, na gode.  Wa alaikumus…

Assalaamu alaikum Baban Sadik, don Allah ina son ka turo mini da kasidar “Tsibirin Bamuda” ta wannan adireshin:  [email protected].  Allah taimakeka, na gode.  
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nafi’u, ka duba jakar Imel dinka, na aika maka kasidar tuni. Allah amfanar da mu baki daya, amin.
Assalaamu alaikum, Allah Ya taimaki Baban Sadik.  Don Allah ina son sanin ko ka wallafa littafi kan “Tsarin Mu’amala da Kwamfuta” (Computer Operations) da harshen Hausa?  In kuma ka wallafa, to a ina zan samu littafin? – Aminu Ringim. Wa alaikumus salam, barka ka dai.  A gaskiya kam ban rubuta wani littafi na musamman kan koyon mu’amala da kwamfuta ba.  Na dai rubuta kan tsarin mu’amala da fasahar Intanet, kuma shi ma ba a buga ba.  Akwai yunkurin buga kasidun da suka bayyana a wannan shafi, wanda shi ne abin da nake aiki a kai a halin yanzu.  Sannan akwai kokari wajen samar da kasida guda daya ta musamman, mai bayani kan abin da kake tambaya a kai, dalla-dalla, don fahimtar Malam Bahaushe, wanda bai taba sanin mece ce kwamfuta ba.  Wadannan su ne abubuwan da na sa a gaba, ban kuma sa lokaci ba, saboda yanayin aikina.  Sai dai a ci gaba da bibiya ta lokaci zuwa lokaci. Allah sa mu dace baki daya, amin.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka.  Ina so ne ka mini tsokaci kadan kan Nokia samfurin Lumia, wato Windows Phone.  Ka huta lafiya.  – Aminu Muhammad
Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Bayanai kan wannan nau’in waya ya sha maimaituwa a wannan shafi. Ka yi hakuri, idan kana da kudura wajen iya mu’amala da fasahar Intanet, kana iya zuwa shafinmu da ke Dandalin Facebook, wato “Dandalin Kimiyya da Fasahar Sadarwa” da ke wannan adireshi: http://www.facebook.com/kimiyyadafasaharsadarwa, don samun kasidu da amsoshin da na bayar kan wannan tambaya ko nau’in wayar salula.  Allah sa mu dace baki daya, amin.
Salam Baban Sadik, don Allah ina so a yi mini karin bayani; ina da waya nau’in Tecno, amma a duk sadda na nemi shiga Intanet sai a ce mini: “Unsupported scripts in content.”  Daga baya kuma sai a ce mini: “Memory full.”  Don Allah ka yi mini karin bayani ta waya ta, domin a kauye nake, ba na samun jaridar Aminiya a inda nake.  –  Babangida Kurma, ’Yandaka, Ruma.
Wa alaikumus salam Malam Babangida, da fatan an wuni lafiya. Na fahimci sakonka, sai dai za ka min uzuri, domin bayan cire sakonka daga waya ta, sai na mance ban adana lambarka ba, shi ya sa na buga a jarida. Fatana shi ne Allah sa wani na kusa da kai ya gani don nusar da kai, ko kuma a dace ka ci karo da shafin.
Wannan sako da wayarka ke ba ka a duk sadda ka yi kokarin shiga Intanet, ishara ce da ke nuna ko dai babu cikakkar ma’adana a wayarka (ma’ana, ma’adanar wayarka ta cike), ko kuma nau’in bayanan da kake son saukar wa wayar, bai dace da nau’in babbar manhajar da ke wayarka ba.  Wannan shi ake kira “Incompatibility,” kuma hanya mafi sauki da za ka bi wajen ganin warware wannan matsala ita ce: ko dai ka share bayanan da ba ka bukata, wadanda suka yi babakere a ma’adanr.  In har matsalar rashin isasshen ma’adana ne, hakan zai warware matsalar nan take.  Amma idan ka yi haka kuma ba a samu natija ba, to, sai dai ka yi “Resetting” wayar, kuma dukkan bayananka za su goge, domin wayar za ta koma yadda aka kero ta asali ne.  In kana son yin hakan abu ne mai sauki; ka je “Settings”, ka gangara “Security” sai ka shiga.  A can karshe za ka ga “Restore to Factory Settings” ko wani abu makamancin haka, ya danganci kamfanin da ya kera wayar ko nau’in babbar manhajar.  Kana matsa “Restore to Factory Settings,” nan take za ta aiwatar.  Za ta kashe kanta, bayan ta gama kintsawa, sannan ta sake kunna kanta.  Sai ka saurara mata.
Muddin matsalar ba ta warware ba bayan bin wadannan hanyoyi, to a nan kam sai dai a hakura; domin alama ce d ake nuna cewa dabi’ar wayar ko babbar manhajar wayar ba ta dace bane da nau’in bayanan da kake son saukarwa ko shigar wa wayar.  Allah sa a dace, amin.
Assalamu alaikum, ranka ya dade.  Abubuwan alherin da kake yi muna godiya ga Allah Ya kara tsare ka, ya kuma daukaka ka.  Wassalam. Daga mai goyon bayanka, dan’azumi Gimba, kankara. Ka huta lafiya.
Wa alaikumus salam, godiya nake matuka kan wannan tallafi na addu’a da karin kwarin gwiwa.  Allah saka maka da alheri kaima, Ya kuma karbi ayyukanmu kyawawa, amin.  Na gode!
Salaamun alaikum Baban Sadik, barka da warhaka, da fatan ka wuni lafiya.  Allah Ya saka da alheri, amin.  A gaskiya ina matukar karuwa da kasidun da kake rubutawa a jaridar Aminiya.  Allah Ya saka maka da alherinsa, Ya kara maka basira, amin.  – Salahuddeen Auwalu Rijiyar Lemu, Kano.
Wa alaikumus salam, ina godiya matuka Malam Salahuddeen, Allah Ya saka maka da alheri kaima, Ya kuma inganta mu baki daya, amin.
Assalamu alaikum, da fatan kana cikin koshin lafiya, Allah sa haka, amin.  Don Allah Baban Sadik ina son a yi mini bayanin yadda zan yi amfani da makalutun sadarwa na Intanet, wato Internet Modem. – Usman Adamu Gumel, Jigawa.
Wa alaikumus salam, barka Malam Usman.  Da farko dai, idan ka siyo Makalutun Sadarwar (Modem), sai ka jona wa kwamfutarka.  Idan ta hange shi, za ta sanar da kai cewa, sai ka je “Computer” ko “My Computer,” za ka ga alamar ma’adanar filash da ke dauke da mkkalutun sadarwar, sai ka matsa.  Nan take kwamfutarka za ta loda shi a kanta kai tsaye, wato “Install” kenan.  Idan ta gama, za ka ga alamar masarrafar a kan shafin kwamfutarka.  Duk sadda ka tashi amfani da makalutun sadarwar, sai ka shigar wa kwamfutarka shi, da zarar ta hango, za ta budo maka shafi.  Sai ka matsa inda aka rubuta: “Connect”, ka ci gaba da yawo a duniyar giza-gizai.  
Idan kudin kati ya kare, za a sanar da kai.  Domin akwai katin SIM  a cikin makalutun da aka ba ka sadda ka je saya.  Kana iya cire katin, ka sa wayarka sannan ka loda kudi, ka sayi “Data”, wato damar da za a ba ka wajen yawo a Intanet ke nan.  Idan kuma za ka saba mu’amala da manhajar kwamfuta, a jikin shafin makalutun Intanet din ma kana iya loda kati, ka sayi “Data” abun ba wuya, wai cire wando ta ka!  Allah sa a dace, amin.