✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonninku ta tes da Imel (3)

A wannan mako na amsa ragowar sakonnin masu karatu ne da suka turo ta tes da Imel.  Idan ba a manta ba, makonni biyu da…

A wannan mako na amsa ragowar sakonnin masu karatu ne da suka turo ta tes da Imel.  Idan ba a manta ba, makonni biyu da suka gabata na tsakuro wasu daga cikin sakonnin, wadanda suka bayyana a karkashin kasidun makonnin. Allah sa mu dace baki daya, amin.

Salaamun Alaikum, gaskiya na yaba da kokarinka.  Kuma don Allah ka yi mini bayanin yadda zan samu haruffan Hausa masu lankwasa a kwamfutata.  Allah saka da alheri, amin.  –  Muhammad Sani Garba.
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Muhammad Sani.  Bayani kan haka ya gabata a kasida ta musamman mai take: “Akwai Haruffan Hausa Masu Lankwasa a Cikin Kwamfutocin Zamani.”  Amma ga alama ba ka ci karo da wannan kasida ba.  Bayan kai, akwai da yawa daga cikin masu karatu da suka sha mini wannan tambaya a wurare da dama da muka hadu da su.  Wannan ya sa nace zan samar da lacca ta musamman ta bidiyo mai dauke da dukkan hanyoyin, wanda zan dora a Intanet ga duk masu bukata, in Allah Ya yarda.  Ga dai bayanin nan a takaice.
Idan kana da masarrafar taskance bayanai mai suna: “Microsoft Word 2007,” ko “2010,” ko “2013,” (duk tsarin iri daya ne) ka bude, sai ka je bangaren “Insert” da ke sama, hagu maso dama, ka matsa.  Da zarar bangaren ya budo, sai ka je can kuryar dama a karshe, za ka ga sashen “Symbols”, mai dauke da abubuwa biyu; “Ekuations” da “Symbols”.  Ka matsa na karshen, wato “Symbols” ke nan.  Da zarar ka matsa wani dan karamin shafi zai budo, mai dauke da wasu haruffa ko alamomi, wadanda a baya ka taba amfani da su, a can kasansu kuma za ka ga: “More Symbols”, sai ka matsa.  Shafi babba zai budo, mai dauke da dukkan haruffan da kwamfutarka ke dauke da su baki daya.  Wannan cibiya ce ta musamman, wacce ke dauke da haruffa da kuma alamomin rubutu, da isharorin da kwamfutarka ke iya fahimtarsu da bayyana su a duk sadda aka shigar mata da bayanai masu dauke da su ko irinsu.
Idan wannan babban shafi ya budo mai dauke da wadannan haruffa, za ka ga bangarori guda biyu ne a sama.  bangaren farko shi ne: “Symbol”, wanda ke bude ke nan.  bangare na biyu kuma shi ne: “Special Characters,” wato alamomi da isharori na musamman da kwamfutar ke dauke da su.  A bangaren farko, wanda shi ne inda damuwarmu take, ka duba can kasa, za ka ga: “Character Code,” wato isharorin da kowane harafi ke wakilta ke nan.  Wannan mahalli shi ne hanya mafi sauki ta samun haruffan Hausa masu lankwasa, idan ka san lambobin da ke ishara ga kowane harafi ke nan.  Amma idan ba ka san lambobin ba, sai ka rika bin haruffan da ke shafin daya-bayan-daya, don nemo harafin da ya dace da abin da kake nema.
Amma don sawwakewa, na ciro maka dukkan lambobin da ke wakiltar dukkan haruffan Hausa masu lankwasa. Don haka, ka zarce wajen “Character Code” kai tsaye, sai ka shigar da 0257 a inda lambobin nan suke, sai ka matsa “Enter” a jikin allon rubutunka, nan take za a kawo maka karamin harafin da mai lankwasa, cikin shudin launi.  Sai ka matsa “Insert” da ke can kasan shafin, za ka gan shi a shafin masarrafar “Microsoft Word” dinka da ke bude.  Sai ka sake shigar da 0253 don samun karamin harafin b mai lankwasa, ka shigar da 0199 don samun karamin harafin k mai lankwasa.  Wadannan kananan haruffa masu lankwasa ke nan.  
Idan kana bukatar manyan haruffa masu lankwasa kuma, sai ka shigar da 018A don samun babban harafin D mai lankwasa, ka shigar da 0198 don samun babban harafin K mai lankwasa, sannan ka shigar da 0181 don samun babban harafin B mai lankwasa.  Wadannan su ne haruffan Hausa masu lankwasa gaba daya, kuma duk suna cikin babban manhajar “Windows,” tun daga “Windows bista” har zuwa “Windows 8.”  Dukkansu suna rukunin “Latin Unicode Character” ne.  
Ga hoton dukkan wuraren da kake bukatar shiga nan cikin sauki; hoton farko daga dama, bangaren “Insert” ne, na biye da shi kuma na bangaren “Symbol” ne, na kasa daga hagu na bangaren haruffan da ka yi amfani da su ne a baya (idan ka lura za ka ga haruffan Hausa masu lankwasa, haka ya faru ne saboda ban jima da yin amfani da su ba), a bangaren karshe kuma za ka ga babbar cibiyar haruffa, inda a nan ne za ka zabi dukkan haruffa ta hanyar bincike daya-bayan-daya, ko ta hanyar shigar da lambobin da ke ishara gare su, kamar yadda muka yi.
A karshe, kana iya cewa ai hanyoyin suna da yawa kuma ga nisa, idan doguwar kasida nake rubutawa yaya zan yi?  Na dinga kai-komo ke nan wajen shigar da kowane harafi idan na zo kansa?  Amsar ita ce eh, amma kuma akwai hanya mafi sauki da za ka iya amfani da ita wajen “koya” wa kwamfutarka fahimtar kowane harafi a yayin da ka matsa wasu maballai da ke jikin allon shigar da bayananka, wato “Keyboard.”  Dabarar da ke sawwake haka ita ake kira “Macros,” kuma hakan na cikin bayanan da zan yi cikin bidiyon da zan fitar ba da jimawa ba, in Allah Ya so.  Domin abu ne da ke bukatar a karantar da shi a aikace, kana gani.  Amma ta hanyar rubutu kadai ba zai gamsar ba.  Da fatan za ka yi hakuri da abin da ya samu.  
Salaamun alaikum, Baban Sadik Allah saka maka da alheri.  A gaskiya muna karuwa sosai da shafinka.  Bayan haka, wacce matsala ce take hana sako isa inda aka tura?  Daga wayar salular ce, ko daga wajen wanda aka tura masa ne?  Na gode.  –  Muhammad Sharada, Kano.
Wa alaikumus salam Malam Muhammad, da fatan kana lafiya kai ma.  Dalilan da ke hana sakon tes isa ga inda aka aika shi suna da yawa.  Na farko, ko dai babu kudi ne isasshe a wayar, sakon ba zai je ba.  Domin kamfanin waya na cajin kudin aikinsa ne da zarar ka baiwa wayar umarni wajen aika rubutaccen sako ko kira.  Idan akwai kudi isassu a wayar, watakila babu yanayi mai kyau ne, wato “Mobile Network” ke nan.  Don haka, kana iya nemo yanayi ta hanyar tsare-tsaren wayar, wato “Settings” ko ka kashe wayar ka sake kunna ta, za ta nemo da kanta.  
Dalili na uku, in har akwai yanayin sadarwa mai inganci, amma sakon ya ki zuwa, ta yiwu wajen latse-latsenka ko wani, ka goge lambar cibiyar sadarwar sakonnin tes, wato: “Message Center Number” ke nan.  Idan lamba guda ta goge daga cikin lambobin da ke wannan cibiya ta karba da aika sakonnin tes, ko cikin kuskure ka kara wata lamba, to, babu yadda za a yi sako ya tafi. Wayar za ta rasa dalili, don haka sai ta daburce, ta ajiye maka sakonka a bakin kofa, wato “Outbod.”  Idan kana son gane haka, ka je “Settings” ka zarce “Messages”, sai ka je “Options”, za ka ga “Message Settings,” daga nan sai ka shiga.  A nan ne za ka ci karo da “Message Center” ka shiga.  Ya danganci nau’in wayarka da nau’in babbar manhajar wayar.  Idan ka shiga “Message Center”, idan wayar mai SIM biyu ce, za ka ga dukkan kamfanonin wayar (MTN da Etisalat, misali), sai ka matsa wadda ka tura sakon daga gare ta.  Idan MTN ce, za ka ga lambobi kamar haka: +234803000000.  Idan Etisalat ce, za ka ga: +2348090001518.  Idan Airtel ce, za ka ga: +2348020000009.  Idan kuma Glo ce, za ka ga: +2348050001501.  Wadannan su ne lambobin cibiyoyin aika sakonni na kamfanonin wayoyin da sunayensu ke biye da su.  Sai ka kirga ka gani, duk wanda bai yi daidai ba, sai ka gyara.  Da zarar ka gyara, kana aikawa nan take sakon zai tafi, in Allah Ya so.  Da fatan ka gamsu.

Za mu cigaba, insha Allah