✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da Imel (5)

Kafin kwarewar Turawan Turai ta yi nisa cikin binciken kimiyya, akidarsu dangane da rana ita ce, a tsaye take cak! Duk sauran halittun da ke…

Kafin kwarewar Turawan Turai ta yi nisa cikin binciken kimiyya, akidarsu dangane da rana ita ce, a tsaye take cak! Duk sauran halittun da ke makwabtaka da ita kuma suna jujjuyawa ne a cikin falakinsu, don kewaye ta. Har a karni na biyu haka ake tafiya a Yammacin duniya. Wannan ita ce ka’idar da ake kira: “Heliocentric Theory of Planetory Motion.” A cikin shekarar 1512 ne wani malamin kimiyya mai suna Nicholas Copernicus ya samar da wannan ka’ida ta ilimi mai suna Heliocentric Theory of Planetory Motion, wanda ke nuna cewa dukkan sauran halittun da ke sararin samaniyar duniya baki daya suna jujjuyawa ne a cikin falakinsu da ke gewaye da rana. Amma ita rana a tsaye take cak, ba ta motsawa. Haka ma binciken da Yohannus Keppler ya tabbatar, cikin shekarar 1609. Sakamakon wadannan bincike ne ya fara wayar wa Turawa da kai, suka dada samun fahimta kan yadda manyan halittun da ke sararin samaniya ke juyawa, suka kuma ba su damar fahimtar “juyin-wainar” da dare da yini ke yi a cikin falakinsu. 

Na tabbata idan ba yanzu ba, da dama cikinmu (wadanda suka yi sakandare shekarun baya), an karantar da mu wannan ka’ida ta ilmin kimiyya da ke nuna cewa “dukkan sauran halittun da ke sararin samaniya na kewaye da rana ne, a halin zagayen da suke yi.” Amma a yanzu kam, malaman kimiyyar sararin samaniya, wato Astronomers, sun warware waccan ka’ida ta Nicholas da Keppler, inda suka tabbatar da cewa lallai rana ma na jujjuyawa a nata falakin, ba a tsaye cak take ba guri guda.
Wata Mahangar
Idan muka koma Alkur’ani mai girma cikin Suratul Ambiya’, za mu samu tabbaci da ke nuna cewa da rana da wata, duk kowanne daga cikinsu na da nashi falaki (ko hanya, ko magudana) da yake bi, da yanayin gudu ko saurinsa. Ga abin da Allah ya ce:
“Kuma Shi ne wanda Ya halitta dare da rana (yini), da rana da wata, dukkansu a cikin wani sarari suke iyo.” (Ambiya’:33)
Wannan ke nuna cewa lallai akwai falaki ko tafarki da kowannensu ke bi a halin iyonsa. An ambaci dare da yini a nan don nasaba da ke tsakaninsu da rana da kuma wata. Har wa yau, tsarin tafiya ko juyawa da suke yi a cikin wannan falaki nasu ya sha bamban. Kowanne da irin saurin da ya kamace shi yake tafiya. Dangane da haka Allah Ya sake cewa:
“Rana ba ya kamata a gareta, ta riski wata. Kuma dare ba ya kamata a gareshi ya zama mai tsere wa yini. Kuma dukkansu a cikin sarari (falaki) guda suke iyo.” (Yasin:40)
Kalmar “iyo” ko “sulmuya” da Allah ya yi amfani da ita (wato “Yasbahoon”) zai sa wani ya yi tunanin ko akwai ruwa ne a sararin samaniya da har rana da wata suke yin iyon a cikinsa. A a, ba haka lamarin yake ba. Kalma ce mai fadin sha’ani, ya kuma danganci yadda aka yi amfani da ita a jimla. Idan aka yi amfani da ita kan mutum a cikin ruwa, yana nufin yana iyo ke nan. Idan a kasa yake, ana nufin yana tafiya ke nan. Haka rana da wata, su ma tafiya suke yi, a cikin muhallinsu a sararin samaniya. Sai dai kowanne daga cikinsu da tafarkinsa daban. Kuma malaman kimiyyar sararin samaniya a yanzu sun tabbatar da cewa rana kan gama kewayenta ne – daga tashar farawa zuwa tashar tukewa (ko “adis”, a turance) – cikin kwanaki 25, a kowane wata. Ke nan, cikin kwanaki 25 take yin kewaye daya. Shi kuma wata yana kewaye wannan duniya tamu ne cikin kwanaki ashirin da tara da rabin kwana (29½). Dangane da haka Allah ya ce:
“Kuma da wata, mun kaddara masa manziloli, har ya koma kamar tsumagiyar murlin dabino, wadda ta tsufa.” (Yasin:39)
Wadannan “manziloli” da Allah ya fada, su ne masaukai da yake sauka a cikinsu a kullum, har ya gama zagayensa cikin wadancan kwanaki da suka gabata. Wannan ke nuna mana cewa dukkan halittun da Allah ya dora a sararin samaniya suna juyawa ko motsawa ne. Amma a tare da haka, ba ka samun wata hatsaniya ko hargitsi cikin lamarin baki daya. Mene ne dalili?
Iko da kudurar Ubangiji
Dalili na farko dai za mu same shi ne cikin iko da kudura da iya kyautata halitta da Allah ya siffatu da su. Babu wanda zai iya samar da ababen halittu irin wadannan sannan ya samar da natsuwa da kimtsi cikin gudanuwarsu, tsawon zamani, ba tare da samun matsala ba, sai Allah. Don haka, ko da ba mu samu wani dalili na zahiri ba dangane da abin da ke sa a kasa samun hargitsi a wannan duniya bayan juyawa da zagaye da take yi a duk yini da shekara ba, wannan kadai ya isa dalili, ga kowane dan Adam mai lafiyayyen hankali.
Tsarin Janyo Nauyi kasa (Force of Grabity)
Da suka gudanar da bincike na kwakwaf, Malaman ilimin Sararin Samaniya sun tabbatar da cewa babban dalilin da ya sa ba a samun hargitsi bayan samuwar abin da a a zahiri zai iya sa a samu hargitsi da rugujewar al’amura a wannan duniya tamu, shi ne samuwar wata ka’ida da tsari da Allah ya kimtsa a duniyar. Wannan tsari kuwa shi suke kira: “The Force of Grabity.” Tsari ne da ke janyo dukkan wani abin da ke sama, zuwa kasa, iya gwargwadon nauyinsa. Suka ce wannan tsari ne ke like mu da kasa, ta hana mu yawo cikin sararin duniyar, kamar yadda auduga ko fallen takarda ko ganyayyakin itatuwa suke yi idan iska ta kada; mai karfi ko mai rauni. Amma a wasu duniyoyin babu wannan ka’ida. A tare da samuwar wannan ka’ida, akwai wasu alamomi da za su nuna mana, idan mun natsu mun yi kallo mai cike da basira, cewa duniyar na juyawa. Wasu alamu ne wadannan?
Alamar farko suka ce ita ce hargitsin ruwan teku da ke samuwa lokaci-lokaci. Sai alama ta biyu, wato iska mai karfi da ake samu a sararin wannan duniyar tamu. Wadannan alamomi, in ji Malaman ilimin Sararin Samaniya, dalilai ne guda biyu da ke nuna mana cewa lallai wannan duniya tamu tana juyawa a duk sa’a guda. Domin asalin samuwarsu na daga karfin juyawar duniyarmu ne, sadda take zagayenta a falaki.
Da fatan ka gamsu.