✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da imel (2)

Ban Hakuri… Kamar yadda masu karatu suka gani a makon jiya, na dan dakatar da kasidarmu kan Tekunan duniya saboda wasu dalilai. Zuwa mako na…

Ban Hakuri…

Kamar yadda masu karatu suka gani a makon jiya, na dan dakatar da kasidarmu kan Tekunan duniya saboda wasu dalilai. Zuwa mako na sama in Allah Ya yarda za mu ci gaba. Kafin nan, mu ci gaba da karbar amsoshin tambayoyinmu.

Assalamu alaikum Baban Sadik. Allah Ya saka da alheri dangane da fadakar da mutane da kake yi. Kuma ina rokon a taimaka mini da kasidun da suka hada da “Bamuda Triangle,” da “Alaka Tsakanin kwakwalwa da Zuciya,” da yadda za a yi amfani da harrufan hausa cikin sauki bayan mutum ya samo su, kamar yadda ka yi mana ishara, ta wannan adireshin Imail: [email protected]. Sannan kuma ka ci gaba da hakuri da mutane dangane da ababen da mutane ke yi maka kamar yadda na karanta a “Waiwaye Adon Tafiya” karo na 5. Kuma ina maka fatan alheri. – Adamu Haruna

 Wa alaikumus salam, barka Malam Adamu. Ina godiya matuka da addu’o’inku. Allah saka da alheri, amin. Hakuri kuma duka namu ne. Yadda nake hakuri daku, haka ku ma za ku ci gaba da hakuri dani. Dangane da bukatunka kuma tuni na aika maka su ta adireshin Imel da ka bayar. Sai ka duba. Allah amfanar da mu baki daya, amin. Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, Allah Ya saka da alheri, dangane da karantar da al’umma da kake yi. Allah Ya sa Aljannar Firdausi ce makomarmu gaba daya, amin. Na karanta amsar da ka bayar dangane da harrufan hausa a kwamfuta. Na je wurin da ka yi ishara kuma na gansu har na yi aiki da su. Na gode. Tambaya a nan ita ce: a wani shafi za ka tura cikakken bayani kan yadda za a yi amfani da su cikin sauki, ba sai mutum ya yi ta komawa yana dauko su ba, kamar yadda ka yi alkawari? – Adamu Haruna

Wa alaikumus salam, Malam Adamu har yanzu ban tsara wadannan bayanai na bidiyo ko ba. Yanzu ne nake kan shirya su. Kamar yadda nace, zan yi bidiyo na musamman da zai karantar da yadda ake neman haruffan Hausa masu lankwasa a kwamfuta, da yadda ake amfani da su, sannan in yi wani bidiyo na musamman dake nuna yadda za ka zakulo so, ka lika su da wasu maballan allon rubutunka, wato Keyboard, ta yadda idan ka tashi neman harafin K mai lankwasa, maballi kawai z aka matsa a jikin allon rubutunka don shigar da shi, ba sai ka ta hakilon zuwan bangaren “Insert” da “Symbol” kana ta nemansu ba. Hanya mafi sauki da ake iya aiwatar da hakan kuwa na cikin fasahar “Macros” ne, wato wata dama da kamfanin Microsoft ke baiwa masu mu’amala da manhajojin “Microsoft Office” don kirkirar kananan masarrafan sawwake ayyuka. Idan na gama shirya wadannan laccoci, zan loda su a shafina dake Youtube, da wanda yake Facebook, wato Dandalin Kimiyyar Sadarwa, in Allah Ya so. Zan kuma sanar a shafina na kaina dake Facebook din, don masu sha’awa su je can su duba. Allah sa mu dace baki daya, amin.
 
Assalamu Alaikum. Barka da yamma Malam, da fatan kana lafiya. Na kasance mai sha’awar fannin “Information & Communications Technology,” duk da cewa fannin kiwon lafiya (Health Education) nake karanta a Jami’a. Na karanta kasidarka mai taken “Tsarin Babbar  Manhajar Android (6)” a jaridar Aminiya a makon da ya wuce. Saboda haka ina da bukatar littafin “Learning Android” a matsayina na dan koyo na fari. A ina zan samu littafin? Kuma yana kaiwa nawa? Sannan, tsakanin waya mai dauke da manhajar “Windows Phone” da “Android,” wacce ce za ta fi taimaka min a harkar karatu da bincike, a matsayina na dalibi (kuma mai sha’awar fannin ICT)? A cikin wayoyi masu dauke da manhajar “Android” (Tecno, HTC, Samsung da sauransu) wacce ta fikarko da juriya ta bangaren “Hardware” da “Software?” Na gode. Daga: Hamza Suleiman Anchau

Wa alaikumus salam, barka da warhaka Malam Hamza. Da farko dai, batun littafin da ka bukata mai taken: “Learning Android,” zan iya tura maka ta adireshin Imel dinka idan kana bukata. Ba ni da wanda aka dabba’a, wato “Printed Copy.” Ina mu’amala da wadanda ake iya amfani da su a kwamfuta ne ko wayar salula mai yalwataccen fuska, wato “Soft Copy.” Dukkan littattafan koyon gina manhajar Android da ka ji na ambata a wannan yanayin suke. Amma idan wanda aka dabba’a kake so, ina iya ba ka adireshin gidan yanar da za ka iya zuwa ka saya a turo maka, in kana da katin ATM. Dangane da tambayarka ta biyu kan nau’in wayar da za ta iya taimaka maka wajen karatu da manufofinka kan fannin da kake sha’awa, tsakanin waya mai babbar manhajar Windows Phone da mai dauke da Android, wannan ya danganci halin aljihunka, da kuma ilimin sarrafa da kake da shi. Akwai wayoyi kala-kala, masu mizani daban-daban, masu manhajoji iri. Ya kuma danganci abin da kake son yi da wayar wajen karatun, wannan shi zai ba da damar fahimtar wace irin babbar manhaja ce za ta iya taimaka maka.
Ta bangaren manhajojin waya, babbar manhajar Android ta fi bayar da damar samun manhajoji masu inganci na kyauta. Domin akwai akalla manhajoji sama da miliyan daya a cibiyar Play Store da ke wayoyin Android. A bangaren Windows Phone ma akwai manhajoji na kyauta sosai, amma ba su kai na Android ba. Baya ga haka, ina ganin mallakar kwamfuta ce mafi sauki wajen ba ka wannan dama. Domin wayoyin salula, duk tsada da yawan kayan da suke dauke da su, ba za ka hada su da kwamfuta ba, wajen karatu. In dai bangaren karatu ne, ba wai fannin ilimin sadarwa kadai ba, kowane fanni na ilimi ya shafe shi.
Dangane da wayar da ta fi karko wajen manhaja da gangar-jiki kuma, wannan ya danganci abin da kake bukata. A zamanin baya ne aka san kamfanin Nokia wajen karkon gangar jikin waya da manhaja. Na’ukan wayoyinsu ne za su fadi kasa, su wargaje, amma da zarar ka harhada su ka jona, su mike garau. Amma a halin yanzu galibin wayoyin salula duk tsarin gangar-jikinsu iri daya ne, bambancin ba shi da wani yawa. Haka ma a bangaren ruhi ko manhajar da suke dauke ita, kusan duk iri daya ce; ko dai babbar manhajar Android ce, ko Windows Phone, ko kuma Jaba, wadanda a halin yanzu sun kusa karewa. Don haka, babu lokacin da kamfanonin wayoyin salula suka fi hadewa wuri guda wajen kera wayoyi masu kama ko darajar jiki iri daya, kamar yanzu. Sannan a bangaren gangar jiki za ka samu kusan dukkan wayoyi suna zuwa ne da shafaffen fuska, wato: “Touchscreen.” Duk da cewa kamfanin Apple ya yi fice wajen kera wayoyi masu dauke da kwarangwal na karafuna da roba mai inganci, sai dai ba ya cikin kamfanonin da ka lissafa. A tare da haka ma, wayoyinsa na da dan karen tsada; ba kowa ke iya mallakarsu ba. Da fatan ka gamsu.

Assalamu Alaikum, Mal Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik). Gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri zuwa gareka . Na samu adreshinka ne a shafin da kake amsa tambayoyi na jaridar Aminiya. Ina yi maka fatan Allah ya kara basira. Daga Umar Abubakar, [email protected]

Wa alaikumus salam, barkan ka dai Malam Umar. Ina godiya da addu’a, Allah saka da alheri, Ya kuma amfanar da mu baki daya, amin. Na gode matuka. 

Dubun jinjina gareka Baban Sadik, ina godiya da sakonninka, tare da ba da hakuri na rashin isar da godiyata a lokacin da sakon ya zo. Hakan ya faru ne sabo da matsalar da na samu  na rashin wayar da ke dauke da Imail. Na gode. Na gode. Naka: Abdullahi Azika Jaredi.

Babu komai Malam Abdullahi, takwara na. In dai ka samu sakon babu damuwa. Bukata ta biya. Fatana shi ne ana ci gaba da karatu da bincike. Idan an sani, a sanar da na baya. Duk abin da Allah Ya hore maka na karatu, kada ka boye; ka bayyana. Da haka ake samun kwararru. Dangane da waya kuma ina rokon Allah Ya kawo budi, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka. Da fatan kana lafiya tare da dukkan iyalanka baki daya. Don Allah Baban Sadik idan har ba damuwa ina son ka  kara turo mini sauran kasidar nan na na’urar “Black Bod”. Don a baya ka turo mini na 1 da na 2. To, yanzun ina son ka turo mini sauran. Nagode! Dauda Shuaibu Luti. Daga jihar Bauchi. 08036907090 08056907090.

Wa alaikumus salam, Malam Dauda barka ka dai. Na tura maka sakon tuni. Sai ka duba akwatin Imel dinka. Allah kara budi da fahimta, amin. Na gode.
 
Assalamu alaikum, Malam yaya aiki da yau da kullum? Da fatan komai lafiya. Wato a duk mako ni ma’abucin karanta kayatacciyar jaridar nan taku ce ‘AMINIYA’. Kuma ina jin dadin karanta wannan shafi naka na Kimiyya da kere-kere. To saboda haka ne na rubuto maka wannan sakon tes domin in maka godiya tare da ma’aikatanku baki daya; musamman ta yadda kuke ilimantar da mutane. Da fatan Allah Ya kara kawo ci gaba kuma Ya saka maku da alheri, ameen. Daga Aminu Isyaku, Kofar Sauri ktrs, Katsina State.

Wa alaikumus salam Malam Aminu, muna godiya matuka da sakonnin addu’o’inku. Allah saka muku ku ma da alheri, amin. Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu. Na gode.