✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonnin masu karatu (1)

SakonninkuA yau kuma, cikin yardar Ubangiji, ga mu dauke da wasu daga cikin sakonnin masu karatu, kamar yadda aka saba. Tsawon wannan lokaci da ya…

Sakonninku
A yau kuma, cikin yardar Ubangiji, ga mu dauke da wasu daga cikin sakonnin masu karatu, kamar yadda aka saba. Tsawon wannan lokaci da ya gabata, na samu sakonninku masu dimbin yawa; da wadanda kuka aiko ta hanyar tes, da wadanda kuka aiko ta hanyar Imel, sai wadanda kuke rubuto mini ta shafina da ke Dandalin Facebook (www.facebook.com/babansadik).  Galibin sakonnin da ke bukatar amsar gaggawa, kuma suka dace da yanayin da ba na cikin shagulgula, nakan amsa su nan take ba bata lokaci, musamman wadanda suka kebanci bukatar kasidun baya, da wadanda ake gani a facebook inda nake sakawa lokaci zuwa lokaci, da kuma wadanda ake gani a Mudawwanar Kimiyyar Fasahar sadarwa (http://fasahar-intanet.blogspot.com), duk da cewa na kwana biyu ban zuba kasidun ’yan watannin da suka gabata ba.  
Don haka, sakonnin da ke nan, duk na tes ne.  Ina bayar da hakuri ga wadanda suka so a ce sun samu amsar tambayoyinsu ko bukatar karin bayani kan wani abu da na rubuta, cikin gaggawa, amma hakan bai yiwu ba. Kamar yadda na sha fada, akwai mantuwa, akwai shagala sanadiyyar aiki, sannan kuma wasu lokuta dole ina bukatar aiwatar da bincike ga tambayoyin da ke da sarkakkiya a cikinsu. Yin hakan na da muhimmanci, musamman ganin cewa da yawa cikin masu karanta wannan shafi dalibai ne ’yan uwana a jami’a ko (wasu) makarantun gaba da sakandare.  Akwai bukatar tantancewa kan duk amsar da za a bayar don kauce wa jefa dalibi ko mai tambaya daga neman sani mai inganci zuwa rudani.
Haka kuma, ga wadanda suka saba mu’amala da Dandalin Facebook, akwai shafi na musamman na bude don zuba kasidun da nake rubutawa a nan, da amsa tambayoyin masu karatu, tare da dukkan wasu bayanai da suka shafi harkar sadarwa ta zamani, da shirye-shiryen da nake gabatarwa a Tashar Sunnah Tb a duk ranar Litinin. Ga adireshin shafin kamar haka: www.facebook.com/kimiyyadafasaharsadarwa ko kuma idan ka shiga shafinka, ka gangara kasa inda aka rubuta “Search” sai ka rubuta Dandalin Kimiyya da Fasahar Sadarwa za a kai ka shafin, sai ka matsa “Like.”  Da zarar ka yi haka, to duk sadda aka zuba wasu bayanai a shafin, za ka rika ganinsu kai tsaye.  
A karshe, ina sanar da masu karatu cewa daga wannan mako na canza layin waya, wanda zan rika karbar sakonninku kadai, daga wadda ke sama zuwa wannan layi: 08021225082. Kuma a kiyaye, wannan layi ne na tes zalla, ba a karbar kira daga gare shi. Duk wanda ya bugo ba a dauka ba, kada ya ji haushi. Wancan layin sai a goge shi; musamman ga wadanda suke da shi a wayoyinsu.  Ta sabuwar layin da na bayar a sama ne kadai za a rika turo sakonni. Allah sa mu dace baki daya, amin.

Salaamun alaikum, ina maka fatan alheri da jinjina.  A gaskiya babu abin da za mu ce, sai dai Allah Ya biya ka, domin kasidarka mai taken: “Hanyoyin Inganta Al’umma ta Hanyar Kimiyya da kere-kere” ta taba kowane fanni.  Na dade ban karanta kasidar da ta birge ni ba irin wannan kasida, sannan kuma ta sanya ni kara jajircewa.  Allah saka da alheri.  Daga: Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Gidan Mai mangwaro.
Wa alaikumus salam, ina matukar farin ciki da jin cewa wannan kasida ta kayatar da kai. Allah sa hakan ya zama tafarkin ci gaba a gare ka da al’umma baki daya. Na gode matuka, a ci gaba da karfafa mu, don samun kwarin gwiwa a ko yaushe.

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da kokari.  Da fatan Allah Ya saka maka da mafificin alherinSa, amin.  Shin, a kimiyyance ko akwai wani amfani da rayuwar dan Adam ke samu daga itatuwa?  Daga:  Aliyu Ibrahim Zawiyya, Gusau.
Wa alaikumus salam, Malam Aliyu, idan na fahimce ka, kana son sanin fa’idar da samuwar bishiyoyi ke da ita ne a bangaren lafiya ko in ce a kimiyyance, bayan fa’idar tattalin arziki, da ta tsaro.  Akwai fa’idoji sama da ashirin da masana kimiyya suka tantance da ke samuwa daga bishiyoyin da ke muhallinmu a kullum.  Daga cikinsu akwai tsabtace iskar da muke shaka a kullum, sanadiyyar kamewa da baure kura da suke yi a duk sadda kura ke kadawa.  Akwai samar da iskar shaka, wanda wani bangare cikin abin da ke taimaka wa dan Adam rayuwa a doron wannan kasa.  Malaman kimiyya sun tabbatar da cewa a shekara guda, gungun itatuwa ko bishiyoyi da ke tare a fadin kasa eka guda na iya baiwa mutane 18 iskar shaka su rayu.  Har wa yau, samuwar bishiyoyi a muhallinmu na taimakawa wajen sanyaya yanayi.  Wannan na faruwa ne sanadiyyar inuwa ta musamman da bishiyoyi ke samarwa da ganyayyakinsu.  Bayan haka, samuwar bishiyoyi a muhalli na taimakawa wajen kare kananan yara daga matsanancin sinadarin zafin rana (Ultrabiolet Rays).  A karshe, kariya ne wajen hana zaizayar kasa.  Wadannan kadan ne daga cikin fa’idojin samuwar bishiyoyi a muhalli.

Salaamun alaikum Baban Sadik, ina maka fatan alheri a kodayaushe.  Don Allah ina son gamsasshen bayani a kan wayar salula nau’in BlackBerry Z10.  A baya na yi amfani da nau’in Galady 2 mai dauke da babbar manhajar Android.  Sannan ina son sanin bambancin da ke tsakanin BlackBerry da Samsung Galady 2?  Na gode: Sameer Ibrahim Kano, 08037310464
Wa alaikumus salam, Malam Sameer.  Wayar salula nau’in Blackberry Z10 dai tana dauke ne da sabuwar babbar manhajar Blackberry 10, sabanin sauran da suka gabace ta masu dauke da zubin Blackberry 6 ko Blackberry 7.  Wannan sabuwa kuma babbar manhaja tsarinta ya sha bamban da wadanda suka gabata. A yayin da za ka iya sayen layin mu’amala da Intanet mai bai-daya (wanda ya hade BB Chat da dukkan hanyoyin mu’amala da Intanet da Imel) a tsohuwar babbar manhajar, a wannan dole sai ka sayi layin shiga Intanet nau’i biyu.  Na farko za ka sayi ‘data’ ne, sannan kuma ka biya kudin layi na wata ko mako daya ko biyu, don yin mu’amala da manhajar BB Chat in kana so.  Bayan haka, akwai bambance-bambance a bangaren kananan masarrafar wayar wadanda suka sha bamban da na babbar manhajar baya.
A daya bangaren kuma, bambancin da ke tsakanin Blackberry da Samsung Galady da dukkan nau’ukanta dai shi ne: kamfaninsu dai ba daya ba ne. Blackberry na kamfanin Research in Motion (RIM) ne, a yayin da Samsun Galady kuma na kamfanin Samsung ne.  Babbar manhajar Samsung Galady ita ce Android, a yayin da babbar manhajar Blackberry kuma ita ce Blackberry OS.  Wadannan, a takaice, su ne manya kuma muhimman bambance-bambancen da ke tsakaninsu.  

Salaamun alaikum, muna matukar jin dadin shafinka. Na karanta amsar da ka bayar kan yadda ake adana sakonnin tes ta ma’adanar katin waya (Memory Card), na kuma ji dadin wannan amsa. Amma ta yaya za a iya yin hakan ta amfani da wayar Gionee S20?  Ina kuma barar kasidarka ta musamman da ka rubuta kan bayanin sama da kasa, kamar yadda ya zo a kur’ani. Ga Imel di na: [email protected].
Wa alaikumus salam, na gode da yabawa. Lallai yadda ka ji bayani a baya, babu wani bambanci tsakanin wayoyi kan yadda za ka iya taskance sakonninka na tes zuwa ma’adanar katin waya, wato “Memory Card.”  Dangane da kasidar da ka bukata kuwa, ka duba akwatin Imel dinka, na turo maka. Allah sa mu yi amfani da abin da muke karantawa baki daya, amin.

Assalaamu alaikum, Baban Sadik, ina maka fatan alheri.  Daga masoyinka Sulaiman Yunusa Salai, Gumel, Jigawa.
Wa alaikumus salam, ina matukar murna da kuma godiya da wanna bushara da fatan alheri da ka yi mini. Allah kara dankon kauna tsakaninmu, amin.

Salaamun alaikum, Baban Sadik shin, mene ne “Blogger” kuma yaya ake amfani da shi?  Allah Ya taimake ka, Ya kuma kara maka basira, amin.  Daga: Sabi’u Uba Yola, Adamawa.
Wa alaikumus salam. “Blogger” dai a takaice wata masarrafa ce da ke taimaka wa mutane wajen bude taska ko mudawwana a Intanet.  Ma’ana wani wuri ko shafi naka na musamman, inda za ka rika zuba bayananka don amfanin kanka da sauran masu ziyara.  Wannan masarrafa ta kamfanin Google ce.  Idan kana bukatar bude shafi na kanka ta amfani da wannan masarrafa, dole sai ka bude akwatin Imel na Gmail, sannan ka je shafin da ke: www.blogger.com/start.  Idan ka shiga sai ka shigar da bayanan Imel dinka, za a kai ka inda za ka cika fom don bude shafinka na musamman.  Da fatan ka gamsu.
Za mu ci gaba