✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amodu Shu’aubu yana bin mu bashin albashin watanni biyu – NFF

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta tabbatar da cewa marigayi tsohon kocin kungiyar Super Eagles Amodu Shu’aibu wanda ya rasu a ranar…

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta tabbatar da cewa marigayi tsohon kocin kungiyar Super Eagles Amodu Shu’aibu wanda ya rasu a ranar Asabar da ta gabata yana bin ta albashin watanni biyu ne ba watanni bakwai ba kamar yadda wadansu kafofin watsa labarai ke yayatawa.
Sakatare-Janar na Hukumar NFF Mohammed Sanusi ne ya bayyana haka a ranar Litinin da ta wuce a Abuja, inda ya ce tabbas marigayin yana bin hukumar albashin watanni biyu.  Sai dai Mohammed Sanusi ya ce ba kocin ne kadai yake bin bashin albashin watanni biyu a hukumar ba, daukacin ma’aikatan da ke hukumar ne suke bin bashin albashin na watanni biyu saboda karancin kudi da hukumar ke fuskanta. “Kwanan nan za mu yi kokarin biyan iyalan mamacin basussukan albashin da yake bin mu bashi”, inji Sanusi.
Idan za a tuna, tsohon kocin kungiyar Super Eagles Amodu Shu’aibu dai ya rasu ne a ranar Asabar da ta wuce a Jihar Edo, kuma jim kadan da rasuwarsa ne aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.