Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta sanar da nada gogaggen dan jarida, Isa Sanusi, a matsayin Babban Daraktanta a Najeriya.
A wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani, ya fitar ranar Alhamis, ta ce zai jagoranci fadada ayyukan bincike, yakin neman zabe, da shawarwari na kungiyar a Najeriya.
- Kotu ta dakatar da Gwamnan Kano daga rusa gine-ginen jikin badala
- Za a kashe wa sababbin ’yan majalisa biliyan 70 a matsayin kudaden ‘maraba’
Kazalika, sanarwar ta ce sabon Daraktan zai mayar da hankali kan rikice-rikice, ilimin hakkin dan Adam, inganta rayuwar mata, sauyin yanayi da shigar da matasa wajen inganta kare hakkin dan Adam.
Kafin sabon nadin nasa, Isa Sanusi ya kasance manajan yada labarai da sadarwa na kungiyar ta Amnesty a Najeriya, mukamin da yake rike da shi tun a shekarar 2016.
Kafin nan kuma, ya yi jarida a Sashen Hausa na BBC na tsawon shekaru 10 kuma ya kasance Mataimakin Edita a jaridar Daily Trust.
Sabon Daraktan na Amnesty ya kuma jagoranci ayyukan kare hakkin dan Adam daban-daban da horar da masu kare hakkin dan Adam a fadin Najeriya wanda.
Ya yi digirinsa na farko a fannin Turanci a Jami’ar Bayero da ke Kano da kuma digiri na biyu a fannin aikin jarida daga Kwalejin Birkbeck ta Jami’ar Landan.
“Isa Sanusi yana cikin tawagar Amnesty a Najeriya tsawon shekaru kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da manyan ayyukan kare hakkin dan Adam da aka samu nasara a kansu.
“Don haka a yanzu, Amnesty International Najeriya za ta shiga wani sabon mataki na ci gaba wanda zai hada da tallafawa da yin aiki tare da kungiyoyin farar hula, masu kare hakkin dan Adam, da masu fafutuka don ciyar da fafutukar kare hakkin dan Adam gaba, tabbatar da cewa masu cin zarafi da kuma wadanda aka zalunta su ji dadin samun damar yin amfani da su cikin adalci,” in ji Rafsanjani.