✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amma dai za a takura wa Allah!

Wani Bafulatani ne ya sayar da shanunsa sai wani malamin tsibbu ya ji labari, ya sa aka yi sallama da shi. Bayan sun gaisa sai…

Wani Bafulatani ne ya sayar da shanunsa sai wani malamin tsibbu ya ji labari, ya sa aka yi sallama da shi. Bayan sun gaisa sai malamin ya ce masa: “Da ma wani abin alheri ne na zo maka da shi.” Bafulatani ya ce: “Wane irin abin alheri ne?” Sai ya ce: “Ka kawo dukkan kudin da kake da su, zan yi maka addu’a, ka zama Sarkin Kano!” Sai Bafulatani ya ce: “Kai ba zai yiwu ba.” Sai malamin ya ce: “Allah fa za a roka!” Sai Bafulatani ya ce: “Kai, amma dai za a takura wa Allah!”
Daga Farfesa A. A. Garba Bata, 07062767748