✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Aminu Bayero ne kadai Shugaban Majalisar Sarakunan Kano’

An soke batun karba-karba lamarin da masu sharhi ke cewa dama za a rina

A ranar Talata Majalisar Dokokin  Jihar Kano ta yi gyaran fuska ga dokar da ta kirkiri sabbin masarautu a jihar inda ta mayar da Shugabancin Majalisar Sarakunan jihar karkashin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero na dindindin.

Hakan na nufin sauran sarakunan na Gaya, Rano, Bichi da kuma Karaye ba za su sami damar dana kujerar ba sabanin yadda aka tsara a baya cewa shugabancin zai zama karba-karba duk bayan shekara biyu.

To sai dai wasu al’umma a jihar na ganin cewa dama can akwai yiwuwar yin wannan kwaskwarimar bisa zargin cewa da ma gwamnati ta yi ta ne saboda tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, amma yanzu dole ta sa aka sauya tunda gwamnatin ta cimma burinta na tube shi.

A ranar biyar ga watan Disamba, 2020r dai Gwamnan Jihar, Abdullahi Ganduje ya sanya hannu a kan sabuwar dokar da kirkar sabbin masarautu hudu a jihar da kuma mayar da shugabancin majalisarsu na karba-karba.

Amma a ranar Talata Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Abdulazeez Garba Gafasa ya jagoranci amincewa da kudirin sabuwar dokar da ta sauyin yayin zaman majalisar.

A karshen zaman dai, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Kabiru Hassan Dashi ya ce sabuwar dokar ta kawo kashen batun karba-karba a shugabancin majalisar Sarakunan.

A cewarsa, “A cikin sabuwar dokar kuma, majalisa ta kara yawan masu zabar sarki a kowacce masarauta daga hudu zuwa biyar.

“Dalilin yin hakan shi ne muna kokarin kauce wa yanayin da za a samu mutum biyu su zabi mutum daya, ragowar biyun su ma su zabi wani, amma idan mutum biyar ne, ko da biyu sun zabi daya uku suka zabi dayan kun ga an sami maslaha ke nan.

“Sabuwar dokar ta kuma yi tanadin wa’adin kwanaki uku domin zaben sabon sarki”, inji shugaban masu rinjayen.

– ‘Mun san za a rina’ –

To sai dai da yake tsokaci a kan sabuwar dokar, Daraktan kungiyar ta Wayar da Kan Jama’a da Tabbatar da Adalci (CAJA) Kwamaret Kabiru Sa’aidu Dakata, daya daga cikin wadanda suka kalubalanci kirkirar sabbin masarautun tun da farko ya ce lamarin ba zo musu da ba-zata ba.

Ya ce dama can tun an kirkiri sabbin masarautun ne da kuma batun na karba-karbar domin a musguna wa tsohon sarkin.

Dakata ya ce, “Yanzu da aka cire shi daga sarki, dole ne su canza dokar saboda ta dace da bukatarsu.

“Mun san wannan tsari ne da ba zai dore ba saboda shi kansa gwamnan da ya kirkire ta sau uku yana mayar da ita gaban Majalisar domin yi mata kwaskwarima a cikin shekara daya kacal”, inji shi.

– ‘Tarihi ya maimaita kansa’ –

Gwamnatin jihar Kano ta ce an yi gyaran ne da kyakkyawar manufar da ta dace ba don a musgunawa tsohon sarkin ba.

Mai ba gwamnan shawara a kan Harkokin Masarautu, Tijjani Mailafiya Sanka ya ce, “Ai tarihi ne ya maimaita kansa, domin ko a baya lokacin muna hade Kano da Jigawa akwai makamancin wannan tsarin.

“A lokacin marigayi Sarkin Kano Ado Bayero shi ne shugaban Majalisar Sarakunan, yayin da sarakunan Gumel, Hadejia da Kazaure ke zama mambobi.

“Saboda haka babu wani sabon abu. Gwamnati a kodayaushe takan yi abin da take gani ya dace ne ga jama’arta.

“Kuma wannan din ma sai da aka tunutbi dukkan masu ruwa da tsaki da masana tarihin masarautu kafin daukar matakin”, inji Mailafiya.

– Abin da ya rage –

Yanzu dai dokar na jiran amincewar Gwamna ta hanyar sa hannu kafin ta zama cikakkiyar doka.

A ’yan watannin baya dai an yi ta kai ruwa rana tsakanin masu adawa da kirkirar sabbin masarautun da suka kira kansu masu kishin Kano kan abin da suka kira kokarin gwamnan jihar na rusa masarautar mai tarihin sama da shekaru 1,000.