✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aminiya ta gudanar da kacici-kacici a garin Zuba

A ci gaba da bayyana wa jama’a irin abubuwan da jaridar Aminiya ke dauke da su musamman ga wadanda ba su san jaridar ba. Jaridar…

A ci gaba da bayyana wa jama’a irin abubuwan da jaridar Aminiya ke dauke da su musamman ga wadanda ba su san jaridar ba. Jaridar ta ziyarci garin Zuba da ke yankin Birnin Tarayya Abuja a ranar Juma’ar makon jiya inda ta ba da kyautar kwafin jaridar  dari. Aikin wanda Mataimakin Manajan Kasuwanci da Talla na Jaridar, Malam Abubakar Haruna ya jagoranta tare da rakiyar daya daga cikin wakilanmu na yankin Adamu Umar, ya samu ganawa da shugabanni da kuma daidaikun jama’a da kuma gudanar da gasar kacici-kacici.

A babbar tashar wucin gadi ta garin Zuba, ’yan kasuwa da masu talla da suka halarci gasar, sun samu kyaututtukan kwafin jaridar bayan nasarar amsa tambaya daya game da jaridar, a yayin da wadansu kuma aka mika musu kwafin jaridar a cikin motar da suke shirin yin balaguro. Haka ayarin ya ziyarci daya daga cikin masallatan Juma’a na garin tare da zantawa da shugabannin malamai da ’yan agaji.

Agoran Zuba, Alhaji Muhammad Bello Umar wanda Aminiya ta isa fadarsa a yayin rangadin, ya bayyana gamsuwarsa a kan yadda jaridar ke kawo abubuwa daban-daban wanda ya ce sun shafi dukan harkokin rayuwa, inda ya bukaci su dore a kan haka. Sarkin Fadar Zuba, Alhaji Murtala Muhammad ya gode wa Hukumar Gudanarwa Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trus da Aminya kan zaban garin Zuba da suka yi don gudanar da shirin.