✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aminiya na neman ma’aikata!

Ma'aikatan da za a dauka za su yi aiki ne hedkwatar kamfanin da ke Abuja

Kamfanin Media Trust, mawallafa jaridun Aminiya da Daily Trust da kuma gidan talabijin na Trust TV, na neman wasu ma’aikata domin cike wasu sabbin gurabe a bangaren Aminiya na kamfanin.

Aminiya na da miliyoyin mabiya da masu karatu ta hanyar jaridar da suke wallafawa a kowane mako da kuma wadanda ke bibiyarta ta intanet da shafukanta na sada zumunta.

Kamfanin dai na neman wanda zai shugabanci sashen Aminiya ne da kuma wanda yake da kwarewa wajen dauka da kuma tace bidiyo.

Shugaban Sashen Aminiya

Ga wanda zai jagoranci sashen na Aminiya, ana bukatar ya kasance mai cikakkiyar gogewa da kwarewa a kan fasahohin zamani sannan ya kasance yana da kwarewa a harsunan Hausa da Turanci, don ya jagoranci bangarorinta na jarida (ta takarda) da kuma sashen intanet.

Wanda ya sami wannan aikin zai yi aiki ne a karkashin Mataimakin Daraktan kamfanin mai kula da bangaren labarai da intanet, kuma zai yi aiki ne hedkwatar kamfanin da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya.

Ana bukatar wanda zai yi wannan aikin ya kasance yana da gogewa da kwarewa a aikin jarida da shugabanci, saboda zai yi aiki da tawagar ma’aikata da dama.

Domin neman wannan aikin da kuma samun cikakken bayani a kai, latsa nan.

Mai dauka da tace bidiyo

Shi ma wanda ya sami wannan aikin zai yi aiki ne a hedkwatar kamfanin da ke Abuja, kuma zai yi aiki ne a karkashin Shugaban Sashen Aminiya.

Ana bukatar mai neman wannan gurbin ya kasance yana da kwarewa wajen ba da shawara, dauka, tattarawa da kuma tace bidiyoyin da za a rika amfani da su a shafin intanet da shafukan sada zumunta na Aminiya.

Domin neman wannan gurbin ko karanta cikakken bayani a kai, latsa nan.