✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amina Sani Bello: ‘Na so a ce na zama Lauya kamar mahaifiyata’ (2)

Amina Sani Bello ita ce uwargidan Zababben Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Sani Bello. Kuma ’ya ce ga tsohon Shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar. kwararriyar Likita…

Amina Sani Bello ita ce uwargidan Zababben Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Sani Bello. Kuma ’ya ce ga tsohon Shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar. kwararriyar Likita ce. Amina Sani Bello a cikin murmushi da annashuwa ta tattauna da wakilan Zinariya a kan yadda take hada taura biyu ta hanyar kula da gida da kuma aikin Likitanci sannan da yadda mahaifanta suka tarbiyyantar da ita suka ba ta ilimin da ta kai matsayin da take ciki a yanzu. Wadannan kadan ne daga cikin tambayoyin da aka yi mata. Ga cikakkiyar hirar kamar haka:

Daga Amina Alhassan da Ahmed Garba Mohammed

Asalinta:
An haife ni ne a Benin a shekarar 1973. Na yi kuruciya a bangarori daban-daban na kasar nan saboda yadda aka rika canza wa mahaifina wurin aiki daga lokaci zuwa lokaci. Na yi karatu a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta ’yan mata da ke Bakori Jihar Katsina (Federal Gobernment Girls College, FGGC) inda na samu shaidar karatun sakandare. Daga nan na wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na karantu a bangaren Likita. A asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) na yi aikin sanin makamar aiki (Residency programme). Sannan na yi karatun digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Liberpool da ke Ingila a bangaren kula da lafiyar al’umma (Public Health).
Abubuwan da ba zan manta da su ba tun ina karama:
Abin da ba zan taba mantawa da shi ba tun ina karama shi ne yadda nake ziyartar Minna, Jihar Neja wurin kakannina a duk lokacin da muka yi hutu. Gaskiya kakannina sun taimaka mani wajen tarbiyyantar da ni da kuma nishadantar da ni a lokacin da nake karama, hakan ya sa a duk lokacin da na samu hutu babu inda nake burin zuwa da ya wuce Minna, garin da Kakannina suke. Wannan ne ya sa muka shaku matuka. Don haka ba na mantawa da wannan abu.
Burina a lokacin da nake karama:
Na so ne na yi karatun Lauya don in zama kamar mahaifiyata. Mahaifiyata ta kasance Lauya ce, don haka a lokacin da nake karama na yi hankoron in zama kamar ita, amma sai ta ba ni shawarar in karanta darussan kimiyya da na lissafi, kuma hakan aka yi, yau ga shi na zama kwararriyar likita.
Abubuwan da na koya a wajen iyayena:
Na samu kulawa ta musamman a wajen mahaifiyata da kuma mahaifina. A gaskiya sun dora mu a bisa hanya madaidaiciya kuma ita ce silar samun nasarorin da muka yi a rayuwarmu.
Abin da ya sa muka kafa Cibiyar Tallafawa Ilimi ta Noor Education Foundation:
Ni da kannena da kuma yayye mata ne muka kafa Gidauniyar tallafa wa Ilimi ta Noor Education Foundation. Cibiya ce da ke tallafawa marasa karfi da marayu ta hanyar biya musu kudin karatunsu har su kammala a kowane mataki. Hasalima ni mutum ce mai sha’awar tallafawa yara kanana da kuma daukar kawainiyar kula da lafiyarsu. Ina fata nan gaba zan kafa cibiyar da za ta rika tallafawa kananan yara musamman marasa galihu ta wajen kula da lafiyarsu. Sannan muna kokarin ganin mun bunkasa cibiyoyin da ke kula da lafiya don ganin an samar da ingantaccen yanayin kiwon lafiya a kowane mataki.
Kasancewata a matsayin uwa:
Ina da yara uku, biyu maza, mace daya. Na haifi dana na farko ne tun lokacin ina karatun Likita a jami’a. To ka ga ba karamin kalubale ba ne mace ta hada aikin kula da yaro da kuma yin karatu. Amma dai Alhamdulillah ’yan uwana sun tallafa mini wajen kula da gida a wancan lokaci da hakan ta sa ban samu wata matsala ba. Baya ga haka, ba karamin kalubala ba ne kula da harkokin gida, amma mijina ya taimaka mini wajen kula da gida a wasu lokuta don haka na samu saukin al’amurra a fagen zama matar aure da kuma uwa a bangaren kula da harkokin gida.
Yadda na hadu da mijina:
Na hadu da mijina ne ta hanyar kawayena a Jami’a. Gaskiya a wancan lokacin ba ni da burin yin aure don na mayar da hankalina ne wajen karatun likita. Amma bayan mun hadu sai ya yi kokarin canza mini ra’ayi. Nan da nan na amince da bukatarsa don na fahimci mutum ne kamili wanda ya san yakamata. Kuma mutum ne mai yawan raha inda yake debe min kewa kuma shawarwarinsa sun taimaka mini wajen samun nasara a karatuna.
Abin da na fi so a wajen maigidana:
Mutum ne mai kula da ni yadda yakamata. Mutum ne mai kaifin tunani, mutum ne mai rikon addini kuma mutum ne mai gaskiya. Da wadannan dabi’u da na lissafa, ba na zaton akwai macen da ba za ta so ta mallake shi ba idan ta samu dama.

Wanda na fi sha’awa:
A gaskiya na fi sha’awar mahaifiyata, don ita ce kashin bayan gidan mahaifina. Yadda take kula da mahaifinmu ya yi tasiri a rayuwarmu, don mun koyi darasi masu kyau a rayuwar zaman aure daga wajenta. Don haka a kodayaushe ita nake dubi a matsayin wacce zan yi koyi da ita.
Lokacin da na fi yin farin ciki:
Lokacin da na fi yin farin ciki ko nishadi shi ne lokacin da nake tare da iyalina, watau ’ya’yana da kuma maigidana. Babu abin da ya fi dadi irin yadda mutum zai samu lokacin zama da ’ya’yansa da kuma maigidansa don su fahimci juna.
Abin da na fi kauna:
Na fi kaunar aikina. Gaskiya ina son aikin da nake yi, don haka ba na wasa da shi. Lokacin da na fi samun kwanciyar hankali da natsuwa shi ne lokacin da na karbi haihuwa, kuma a ce macen ta haihu lafiya kuma jaririn ma lafiya. Da zarar hakan ta faru sai na ji ina cikin farin ciki da natsuwa.
Ina son hutawa da iyalina:
Nakan huta tare da iyalina. Wani lokaci mukan ziyarci wuraren shakatawa ko kuma mu zauna a gida mu yi ta kallon tasoshi masu kayartarwa a talabijin.
Irin tufafin da na fi so:
Wadanda ba su da tsada kuma masu suturta al’aura. Da zarar na sanya tufafin da suka lullube ni kamar yadda shari’ar Musulunci ta tsara ba lallai masu tsada ba, zan fita na cigaba da harkokina ba tare da wata matsala ba.
Kyautar da mijina ya yi taba yi min wacce ba zan manta ba:
Ya taba ba ni kyautar zobe a ranar bikin zagayowar ranar haihuwata (birthday). Gaskiya na ji dadi sosai, ba wai zoben ne abin dubawa ba, amma kaunar da ya nuna mini wajen ba ni zoben a ranar, shi ne ba zan taba mantawa da shi ba.
Abin da mijinta ya fi kauna:
Ya fi kaunar a yi ilimi. Abin da ya fi kokawa a kai shi ne yadda harkar karatu ta tabrabare a kasar nan da kuma yadda matasa suke gararamba a kan tituna ba su da aikin yi. Gaskiya wannan abu yana kona masa rai, kuma yana tunanin hanyoyin da zai bi ya ga an mangance wannan al’amari. Yana tunanin bullo da hanyoyin da zai sa matasa su daina zaman kashe wando. Yana tunanin bullo da hanyoyin da zai tallafawa matasa musamman a bangaren aikin gona. Don haka mijina mai tausayin matasa ne kuma yana da hankoron ganin ya tallafa musu don rayuwarsu ta inganta.