✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfanin man zaitun wajen gyaran gashi

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku bayanin yadda za ku…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku bayanin yadda za ku yi amfani da man zaitun wajen gyaran gashi.

Man zaitun na da matukar muhimmanci a jikinmu. Ana amfani da shi a matsayin man kitso.
Da farko a samu man zaitun mai kyau, sai a sanya shi a murhun zamani da ake kira ‘microwabe’ ko a sanya a cikin tukunya, sai a dora shi a murhu, sannan  a bar shi ya yi dumi kamar tsawon minti 10.
• Daga nan a rika amfani da hannu wajen dibar man zaitun din ana shafa wa shi a karkashin gashin kai. Haka za a rika shafawa har sai gashin ya gaurayu da man gaba daya.
• A tabbata gashin a tsefe yake, sai a rufe shi da hular leda kamar na tsawon minti talatin.
• Bayan minti talatin, sai a wanke kan da man ‘shampoo’ da na ‘conditioner’.
Idan aka ci gaba da wanke gashin kai za a samu canji, domin gashin zai zama mai sheki da santsi da laushi da kuma tsayi.