✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfanin man amfuna

Man amfuna yana da matukar mahimmanci a wajen magance cututtuka da kuma gyaran fatar jiki. Shekaru da dama ana amfani da wannan man don haka,…

Man amfuna yana da matukar mahimmanci a wajen magance cututtuka da kuma gyaran fatar jiki. Shekaru da dama ana amfani da wannan man don haka, ba wani sabon abu ba ne. Amfani da wannan man na iya kare mutum daga warin baki da fesowar kurajen fuska. Sinadaren da ke cikin amfuna suna wanke maikon da ke kokarin zama kuraje a fuska.

• Man amfuna yana magance kaikayin jiki ko kuma yawan soshe-soshe a cikin barci. A samu tawul a jika da man amfuna sannan a shafa a jiki domin samun sauki.

• Yana magance warin baki domin ya kunshi sinadaren da suke magance warin baki. A debi rabin cokalin man amfuna sannan a kwaba da ‘baking soda’ sai a mayar da shi man magogi. Ana wanke baki da shi a kullum domin magance warin baki.

• Wannan man na warkar da kaikayin kai ko na jiki. Yana kunshi ne da sinadarin ‘alpha hydrodyl’ wanda yake cire duk abin da ke janyo kaikayi. A shafa man amfuna a tafin hannu sannan dayan tafin hannun kuma a sa shi a ruwa sai a hada hannayen sannan a shafa a fatar kai domin hana amosanin kai fitowa.

• Man amfuna yana magance ciwon farce. Da yake yana da sinadarin yakar wannan kwayar cutar, sai a tsoma yatsan da ake da matsala a cikin man amfuna da zafi,amma sai an daure.

• Za a iya hada wannan man da zuma domin samun kuzari da kuma karfin jiki.