Kankana tana daya daga cikin ’ya’yan tsirrai da suke dauke da sinadaran gyaran jiki da magance gautsin fata da rage tsufa.
Tana dauke da sinadaran da suke wanke maikon da yake taruwa a magudanar gumi wanda yawansa yake haifar da fesowar kuraje da dama.
- ’Yan bindigar da suka sace masu ibada 66 a Kaduna sun kashe 2 daga cikinsu
- Dakin otal na karkashin ruwa da ake biyan sama da N22m a dare daya
Don haka, amfani da kankana a jiki yana da matukar muhimmanci ga rayuwarmu ta yau da kullum.
A yau na kawo muku hanyoyi da dama da za a bi domin yin amfani da kankana, don samun fata mai laushi da sheki a kodayaushe!
Kodewar fuska
A markada kankana da gurji a rika shafawa kamar sau biyu a rana, hakan na matukar magance wannan matsala.
Sannan za a iya markada kankanan zalla, sai a dauko auduga ana tsomawa ana shafawa a fuska, sai a bari ta bushe na tsawon minti 15.
Za a iya markada kankana da ganyen na’ana’a sai a rika shafawa a wajen da fatar ta kode. Amma abu daya ake so a yi amfani da shi a cikin ababen da aka lissafo.
Domin yankwanewar fata
A markada kankana a zuba mata zuma kadan, sai a rika shafawa a inda fatar take yankwanewa sau biyu a rana.
A samu kankana da ruwan lemun tsami da sukari a hada su wuri daya.
Kafin sukarin ya narke sai a rika dirzawa a inda fatar ta yankwane domin mikar da fatar.
Rage shekaru
A samu kankana da man zaitun da kindirmo da kwaiduwar kwai, sannan a kwaba a rika shafawa a fata a kullum domin samun sakamako mai kyau.
Za a iya markada kankana a samu ayaba a kwaba a hada su wuri daya, sai a rika shafawa a fata.
A samu markadaddiyar kankana da madara da fiya a kwaba a rika shafawa a fata domin samun sakamako mai kyau.
Kurajen fuska
A samu kwallon kankana a busar a rana, a daka ya yi laushi sai a tafasa ruwa a zuba a tace sannan a rika wanke fuskar da shi sosai.
Gautsin fata
A markada kankana, a zuba mata man ridi da na kwakwa a shafa a fata na tsawon minti 20 sannan a wanke.