Mata da dama na sha’awar ganin fatarsu ta yi sumul-sumul musamman ma a ce babu kuraje.
Wannan ganye na dauke da sinadarai da dama wadanda sukan iya dada tsawon gashin mace da sa fuska sheki da gyaran jiki da sauransu.
- An nada kasurgumin dan bindiga sarautar gargajiya a Zamfara
- Ma’aikacin filin jirgi ya saci jirgin sama
Don haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da za a bi domin amfani da su wajen gyara fata da kuma gashin kai.
Ina so masu karatu su gane cewa, a duk lokacin da na lissafo abubuwan hadin kwalliya guda daya daga cikinsu nake so a yi amfani da shi.
Domin yawan sa wa fuska abubuwa da dama na haifar da fesowar kuraje.
- Kodewar fuska: Yawan aiki ko shiga rana na sa fuska ta yi baki ko launinta ya zama biyu.
A samu ganyen ‘aloe vera’ a matse ruwansa sai a matsa ruwan lemon tsami a kwaba a rika shafawa a fuska don daidaita launin wannan fata.
- Yaushin fata: Wannan ganye na rage tsufa a fuskar mutum. A matse ruwansa a hada da ruwan ‘rose’ a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti goma zuwa goma sha biyar kafin a wanke a kullum.
- Yawan gumi/ maiko: A samu ganyen a dan kankare bayansa, sannan a sa ruwa a tukunya a dora wuta sai ya dahu ya yi laushi, sannan a sauke a zuba zuma bayan ya huce, sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 a kullum kafin a shiga wanka.
- Gautsin fata: A markada dabino da gurji sai a matsa ruwan ganyen ‘aloe vera’ da ruwan lemon tsami, sannan a shafa a fuska da jiki na tsawon minti 30 kafin a wanke.
- Gyaran gashi: A matse ruwan ‘aloe vera’ a hada da man zaitun a kwaba su, su kwabu sosai sannan a rika shafawa a fatar kai da kuma saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai. Yin haka na sa bakin gashi da kuma dada masa tsawo da karfi.