✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfanin dabino ga mai azumi

Amma masu ciwon suga ba a so su ci sama da kwaya 3 a rana, saboda lafiyarsu.

Binciken masana a duniya ya nuna cewa dabino yana da nau’in sinadaran abinci daban-daban masu amfani ga jikin ɗan’adam.
Dabinon da a yanzu ya yi tashin gwauron zabo a wasu sassan Najeriya dalilin hauhawar farashin kayayyaki da kuma zuwan watan azumi, na daga cikin muhimman abincin da Musulmi a duniya ke buda-baki da shi.

Farfesa Bappa Adamu, Ƙwararren Likita ne kuma malami a sashen cututtukan da suka shafi ciki da cutar ƙoda a Jami’ar Bisha ta Saudiyya, ya ce dabino yana bai wa mai azumi kuzari nan take bayan shan ruwa, ba tare da ya ƙara yawan sukari da yawa a cikin jini ba.

Sai dai kuma a tattaunawarsa da TRT, Likitan ya gargadi masu larurar ciwon suga da su taƙaita cin sama da guda uku a rana.

“Dabino na dauke da nau’in abinci iri-iri da ke amfani ga jiki. Misali, yana bai wa mai azumi kuzari nan take bayan an sha ruwa ba tare da kara yawan sinadrin sukari da yawa a jini ba.

“Amma masu ciwon suga ba a so su ci sama da kwaya 3 a rana, saboda lafiyarsu.” in ji shi