✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfani da ‘ya’yan itace don gyaran fata

Kowace mace ba ta so a ce ta tsufa duk yawan shekarunta kuwa. A kullum tana so a ce tana sake zama yariny. Shin kina…

Kowace mace ba ta so a ce ta tsufa duk yawan shekarunta kuwa. A kullum tana so a ce tana sake zama yariny. Shin kina so ki san sirrin da ke gyara fata a lokaci guda ya boye tsufanta? Ba wani abu ba ne illa yawan amfani da ‘ya’yan itace wajen gyaran fata. Amfani da mayukan kanti na yi wa fata illa. Amma amfani da ‘ya’yan itatuwa na sanya fata santsi da kuma laushi.
·         Ki samu ruwan lemon tsami, sai ki hada shi da sinadarin ‘glycerin’ ko ruwan ‘rose water’, sannan ki shafa a fuska da jiki kafin ki kwanta barci. Yin hakan zai cire miki bakaken kurajen fuska wadanda ke sanya fuska ta yi duhu.
·         Ki markada gurji, sannan ki tsiyaye ruwan, sannan ki hada shi da ruwan lemon tsami. Daga nan ki shafa a fuska. Za ki iya kwantawa da shi, ki wanke washegari. Yin haka na kara hasken fata, ya kuma kara mata lafiya.
·         Ki samu karas sai ki markada shi, sannan ki shafa a jiki da fuska. Bayan awa biyu sai ki wanke. Yin hakan na sanya fata sheki.
·         Ki samu kurkum sai ki hada shi da garin alkama, sannan ki kwaba su da man zaitun, sannan ki shafa a fata.
·         Ki matse ruwan lemon zaki sannan ki shafa a fuska, hakan zai sanya fuskarki ta yi laushi.
·         Ki gauraya madarar saniya da gishiri kadan da kuma ruwan lemon tsami a kwano. Daga nan ki yi amfani da auduga ko tsumma mai tsabta wurin share gumin fuska ko dattin fuska. Hakan zai sanya fuska ta yi haske.