Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya ce amfani da na’ura mai kwakwalwa yayin zabe ne kadai hanyar magance kalubalen zabe a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne jim kadan da kada kuri’arsa a zaben Kananan Hukumomin Jihar Kaduna da yake gudana ranar Asabar.
- An kashe Babban Injiniyan ‘Federal Poly Bauchi’ a gidansa
- Yadda zaben kananan hukumomin Kaduna ke gudana
Sarkin ta ce, “Ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa yayin zabe, za a magance matsalar tafka magudi, saboda kana kada kuri’a za ta tafi wajen tattara sakamako.”
Sarkin na Zazzau ya kuma ce tsarin zaben zai magance matsalar satar akwati.
Alhaji Ahmed Bamalli ya kuma kira ga al’umma da su ba da goyon baya ga duk wanda Allah ya ba nasara dan samun dauwamammen zaman lafiya da ci gaban kasa.
Zaben Kanana Hukumomin a wasu sassa na Jihar Kaduna dai ya fuskanci matsalar isuwar kayan aiki a makare da kuma karancin masu zabe.
Bugu da kari, wakilimu ya lura cewa dokar hana zirga-zirga ba ta yi tsauri ba a yankin Zariya, a inda harkokin sufuri ke gudana a tashoshin mota da ke yankin kwangila.
Haka kuma, a wasu mazabun a Kananan Hukumomin Zariya da Sabon Gari ba a fara zaben a cikin lokaci ba.
Da wakilin mu ya nemi jin ta bakin Babban Jami’in Zabe na Karamar Hukumar Sabon Gari, Malam Iliya Musa ya shaida mana cewar sun raba kayan zabe tun misalin karfe 8:00 na safe.
Zaben dai na gudana lami lafiya sai yan kananan matsalolin naurar zabe da shima ake warwarewa.