✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Amfani da man bilicin na iya haifar da ciwon koda’

Gidauniyar dai ta kuduri aniyar tallafa wa masu fama da cutar

An bayyana amfani da man bilicin wajen canza launin fata da kuma shaye-shaye da cewa suna cikin manyan abubuwan da za su iya haifar da kamuwa da ciwon koda.

Shugaban gidauniyar yaki da ciwon koda ta Kidney Care and Transplant Trust, Akitek Ibrahim Haruna Abdullahi ne ya bayyana haka lokacin da suka ziyarci mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa ranar Alhamis.

Ya ce sun kai ziyarar ce domin yi wa Sarkin bayani kan shirye-shiryen da gidauniyar ke kokarin yi na kaddamar da wani asusun da zai tallafa wa masu fama da cutar da wanki da kuma dashen kodar.

Ya ce yanzu bincike ya nuna yawan masu kamuwa da cutar a Najeriya da ma duniya baki daya na dada karuwa.

“Wasu daga cikin cututtukan da suka fi haifar da wannan cuta ta koda sun hada da hawan jini da ciwon suga da ciwon mafitsara ga maza da shaye-shaye da kuma yawan amfani da magunguna ba tare da umarnin likita ba ko magungunan gargajiya da kuma amfani da man bilicin don canza launin fata.

“Saboda haka Mai Martaba, wannan gidauniyar ta kuduri aniyar ganin ta tallafa wa masu karamin karfi wajen wankin koda ko kuma dashenta, saboda yana da matukar tsada,” inji shi.

Dag nan sai Shugaban gidauniyar ya ce za su tuntubi ragowar masu hannu da shuni a ciki da wajen Jihar ta Kano don ganin hakar su ya cim ma ruwa.

Da yake nasa jawabin, Sarkin na Kano ya yi alkawarin cewa masarautar za ta ba gidauniyar duk irin gudunmawar da take bukata wajen ganin yunkurin ya samu nasara.

Sarkin, wanda Madakin Kano, Yusuf Nabahani ya wakilta, ya kuma koka kan yadda ya ce cutar na ci gaba da yaduwa tare da kama manya da yara, inda ya ri kira ga jama’a da su ci gaba da bin shawarwarin likitoci don kare kansu.